Shiga cikin tawagar Paxful

A Paxful, muna ƙoƙarin samar da sauyi mai amfani ga rayuwar mutane ta yau da kullum. Mun yi imani cewa, samun damar gudanar da hada-hadar kuɗi na ɗaya daga cikin 'yancin ɗan adam sannan muna bakin ƙoƙarinmu wajen jadda hakan. Shiga cikin tafiyarmu domin samun sauyi!

Kana son sanin me Paxful ta ƙunsa? Kalli wannan ƙayataccen bidiyo domin samun masaniya!

Shiga cikin tawagar Paxful

Yaya aiki a Paxful yake?

Aiki a Paxful ba wani abu na daban ba ne. Ma'aikatanmu suna rarrabe a tsakanin ofisoshi huɗu da ke wurare daban-daban a duniya, suna aiki kan alƙibla guda. Muna aiki sosai, mu huta sosai, sannan mu yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa mun cimma manufofinmu. Sau da dama za ka ga ma'aikacin Paxful a wurin waƙa, wurin motsa jiki, wurin cin abinci, ko wurin shan hantsi. Wata ƙila ya kasance wani iri, amma haka yake cewa muna kiran junanmu a matsayin iyali saboda muna ƙaunar juna sannan muna ƙaunar abin da muke yi.

Manufarmu

Manufarmu ita ce samar da 'yanci kan tattalin arziki ta hanyar harƙallar kuɗi ta mutum-zuwa-mutum. Ta hanyar kafa mai tsaro da sauƙin amfani wadda ta tattara kwastomomi da aka tantance, muna son zamowa kan gaba a duniyar harƙallar kuɗi sannan masu taimakawa wajen sauya kuɗi na duniya. Ta hanyar ba wa ilimi muhimmanci, tawagarmu na ƙoƙarin taimaka wa mutane da ke faɗin duniya wajen haɗuwa da juna da gina mu'amala, wanda hakan ke ba su damar samun ilimi tare da bunƙasa al'amuransu. Daga ƙarshe, za a samu sauyi mai amfani ga rayuwar mutane a ko'ina. Sauyi ne na haƙiƙa wanda mutane na haƙiƙa suka samar.

Kana ƙarƙashin kulawarmu

Mun damu da lafiyarka

Muna ba da abincin rana da na dare a kowace rana. Muna ba da katin zama mamba na nau'in motsa jiki iri-iri da kake da ra'ayi, da zuwa wurin tausa, da sauran al'amuran kiwon lafiya da ake aiwatarwa a ƙungiyance. Sannan akwai damar ganin manyan likitoci ta kan intanet.

Mun mayar da hankali sosai game da ci gabanka

Ta hanyar kai ziyara jami'o'i daban-daban a duniya da kuma karɓar laccoci da horaswa daga masana, mun yi imani cewa hanyar ci gaba kawai ita ce ta ƙara neman sani da ƙwazo.

Taɓa kiɗi taɓa karatu

Kawo sauyi a duniya ba abu ne mai sauƙi ba. Saboda haka, kuma domin samun hutu daga aiki tuƙuru da muke yi, muna gudanar da shirye-shirye, tarurruka, har ma da yawon shaƙatawa wanda kamfani ke biya domin a samu nishaɗi, da samun ƙarin ilimi da kuma samun damar haɗuwa da abokan aiki da ke sauran ɓangarori na duniya.

slider-image1
slider-image2
slider-image3
slider-image4
slider-image5

Sassa

Fasahar Gini kan Intanet

Zuciyar Paxful. Tawagar gudanarwa da lura da al'amura na aiki tuƙuru kuma ba ƙaƙƙautawa wajen samar da sababbin abubuwa da inganta waɗanda suke wanzuwa tare da hasashen abubuwan da za su fi dacewa a nan gaba na abin da ya shafi harkar kuɗi ta mutum-zuwa-mutum.

Kaya

Tawagar da ke da alhakin kula da kayayyaki suna aiki tuƙuru. A koyaushe suna tunanin sababbin hanyoyin da za su inganta ayyukanmu. Masu Zane, Manajojin Kaya, da Masu Nazari duk suna ƙoƙarin ganin cewa zuzzurfan tunanin da nazarce-nazarce da suke sun koma abubuwan zahiri waɗanda al'umma za su amfana da su.

Bin Doka da Damfara da kuma Walwalar Kwastoma

An rarraba babban sashen Paxful a nahiyoyi da daban-daban domin tabbatar da ba da taimako da warware jayayya a kowane lokaci kuma a kowace rana 24/7. Wannan tawaga na aiki domin ba da tsaro a kafarmu da kuma masu asusu, ta hanyar tabbatar da cewa ana bin ƙa'idojin da suka kamata sannan suna gudanar da nazari dangane da blockchain.

Talla

Waɗannan su ne mutanen da ke yaɗa aƙidar harƙallar kuɗi ta mutum-zuwa-mutum a duniya. Ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na gargajiya da na zamani, suna da burin kai wa ga al'ummar duniya ta hanyar ilimantarwa, ƙunshiya, gina al'umma.

Kuɗi

Waɗannan sassa sun kasance madugun tafiya gare mu. Suna tabbatar da cewa bayananmu sun kasance ingantattu sannan dukkannin harƙallolinmu ba su saɓa wa shari'a ba.

Hada-Hadar Mutane

Mutanen da ke tabbatar da cewa al'amuran Paxful sun kasance masu daɗin sha'ani. Su ke kula da dukkannin ƙoƙarin mutanenmu, sannan su ke gudanar da dukkannin al'amura da suka shafi ci gaban ma'aikata, tare da dura da ayyukan ofisoshi da ayyuka daban-daban da suka shafi gudanarwa da al'amuran masana'antar.

Ta yadda za ka shiga cikin tawagar Paxful

Fahimtar yanayi da tura takardar neman aiki

Ka zama kana shirye da a kira ka

Jarabawar neman aiki ta farko

Ta yaya ka yi nasara game da jarabawar neman aikinka?

  • Karanta bayanai game da #AnGinaDaBitcoin da kuma manufarmu na samar da adalcin hada-hadar kuɗi ta hanayr Bitcoin.
  • Duba kafafen sada zumuntarmu. Idan ba ka san mene ne Bitcoin ba, ka yi bincike domin samun bayanai game da tasirinsa a kimiyance da kuma tasirinsa ga tattalin arziki
  • Duba kafafen sada zumuntarmu domin ganin yadda tsari da salonmu yake
  • Faɗa mana sama da abin da yake cikin takardar bayanin kanka! Mene ne ya sa ka zama na daban?