Dokokin Aikin Stablecoin na Paxful

Ranar farawa: Maris 4, 2021

DAURE KA KARANTA WANNAN YARJEJENIYA CIKIN NATSUWA. Idan ka yi amfani da tsarin Stablecoin ɗin Paxful, ka nuna cewa ka aminta da waɗannan ƙarin "Dokokin Aikin Stablecoin ɗin Paxful" sannan ka aminta da cewa ka karanta cikin natsuwa kuma daki-daki, ka fahimta, sannan ka yarda da dukkannin dokoki da ƙa'idojin da suke ƙunshe a nan, waɗanda suka kasance ƙari a kan Dokokin Aikin Paxful ("Yarjejeniyar"). Duk wasu dokoki da aka jaddada waɗanda aka yi amfani da su amma ba a zayyano su a ƙasa ba suna da ma'anonin da aka ba su a cikin Jarjejeniyar. Idan aka samu wani cin karo tsakanin Yarjejeniyar da Dokokin Aikin Stablecoin ɗin Paxful a yayin harƙallarka da ta shafi tsarin Stablecoin ɗin Paxful, to na Dokokin Aikin Stablecoin ɗin Paxful za a bi.

Game da Stablecoin ɗin Paxful

Tsarin Stablecoin na Paxful ya kasance tsarin gabatar da mutane a wanda ke ba ka dama, a matsayinka da mai amfani da Paxful, ka shiga cikin harƙalla irin ta mutum-zuwa-mutum tare da wani kamfani na daban ("Kamfanin Haɗin Guiwar Stablecoin"), wanda Paxful ya zaɓa, domin sauya Bitcoin naka zuwa USD kwatankwacin darajar stablecoins, wanda Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin za su riƙe domin ci gabanka. Ta wannan hanyar, Stablecoin na Paxful na ba ka damar sauya matsayin Bitcoin naka zuwa stablecoin da aka zaɓa.

Tsarin Gayyata

Tsarin Stablecoin na Paxful ya kasance taƙaitaccen tsarin gabatar da mutane wanda ke kan kafar Paxful. Yayin da ka nuna ra'ayinka cewa kana son gudanar da harƙallar Stablecoin na Paxful, Paxful zai gabatar da kai zuwa ga Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin domin gudanar da harƙallar. Daga nan dole ne ka bi matakan tura dokokin tayinka zuwa Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin ɗin. Idan Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin ya karɓi dokokin tayinka, za a gudanar da harƙallar tsakanin kai da Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin ɗin. Tamkar yadda sauran harƙalloli ke gudana a kasuwanninta, Paxful ba za ta shiga shiga ba, ko juya akala, ko samun iko, ko yanke hukunci ba a game da harƙallolin Stablecoin na Paxful wanda ka shiga ciki ko ka yi yunƙurin shiga tsakaninka da Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin. Paxful ba za ta ajiye stablecoins ba sannan ba za ta ba da umarni ga kowane mai amfani da Paxful ba domin ya mallaki waɗannan stablecoins.

Tana iya kasancewa Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin na da nasu dokoki da ƙa'idoji da suka shafi harƙallar Stablecoin na Paxful, sannan harkar Stablecoin na Paxful na iya bambanta ta fuskokin da suka shafi farashin musanye, saurin musanye, da sauran dokoki da ƙa'idoji da Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin ya gindaya ("Dokokin Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin"). Idan ka shiga cikin harƙalla da Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin, hakan na nuna cewa ka aminta da Dokokin Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin ɗin. Dokokin Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin za su kasance masu aiki a kowane lokaci har sai ko idan sun ci kare da Yarjejeniyar, ko waɗannan Dokoki da Ƙa'idojin Stablecoin na Paxful, ko sun saɓa doka, ko ba su kama hankali ba, ko kuma idan sun kasance suna da wahalar a bi su (kamar yadda Paxful ta nuna a wurin bayanin mallakar 'yanci), ko idan kai da Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin kun aminta kan cewa za ku kauce wa Dokokin Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin ɗin. HAƘƘINKA NE KA KARANTA DOKOKIN KAMFANIN HAƊIN GUIWA NA STABLECOIN ƊIN SANNAN KA BI DOKOKIN YADDA SUKE. IDAN BA KA BI DOKOKIN KAMFANIN HAƊIN GUIWA NA STABLECOIN ƊIN BA, ZA A IYA HANA KA HARƘALLARKA. KADA KA TAƁA SHIGA CIKIN HARƘALLAR STABLECOIN NA PAXFUL HAR SAI KA BIBIYI DUKKANIN DOKOKI DA ƘA'IDOJIN DA AKA LISAFA. IDAN BA KA BI WAƊANNAN DOKOKI DA ƘA'IDOJI BA, WATA KILA PAXFUL BA ZA TA IYA TAIMAKONKA BA A MATAKIN JAYAYYA DOMIN DAWO DA KUƊAƊENKA.

Kuɗaɗe

A koyaushe Paxful za ta riƙa bayyana bayanan da suka shafi kuɗi domin yin ƙeƙe-da-ƙeƙe game da duk wani caji da za a maka sakamakon amfaninka da kafar Paxful. Domin neman ƙarin bayani dangane da kuɗin musanye, to ka tuntuɓi Sashen Taimakonmu.

Asusun da Suka Tantance da Kuma Iyakantattun Muhallan Shari'a

Tsarin Stablecoin na Paxful ba kowa ne zai iya amfani da shi ba, sai masu amfani da kafar waɗanda suka cancanta. Idan kana so ka samu cancantar amfani da tsarin Stablecoin na Paxful, to dole ne ka tantance akawun ɗinka sannan ka mallaki a ƙalla Bitcoin da ya kai darajar Dalar Amurka $1.00 a cikin lalitarka ta Paxful, tare kuma da ƙarin adadin Bitcoin da ake buƙata wanda zai isa ya biya dukkannin kuɗaɗe da ya kamata a biya. Paxful na da damar hanawa ko sauya salon harƙallar Stablecoin na Paxful ga kowanne mai amfani da kafar, sannan Kamfanin Haɗin Guiwa na Stablecoin na iya ƙin yin harƙalla da kowane mai amfani da Paxful. Ƙari kan Taƙaitawar Muhallin Doka wanda aka gabatar a Sashe na 2.7 na Dokokin Aikinmu shi ne, mutanen da suke Jahar Texas ba za su iya harƙallar Stablecoin ɗin Paxful ba.

BABU GARANTI, TAƘAITAWAR ƊAUKAR NAUYI DA KARƁAR KASADA

TSARIN STABLECOIN ƊIN PAXFUL ANA KAWO SU NE "KAMAR A CIKIN" SANNAN "KAMAR YADDA SUKE" BA TARE DA WANI GARANTI, KO WAKILCI BA, KO DA WANDA AKA BAYYANA NE KO WANDA AKA SANYA KO WANDA AKA BA DA DAMA. PAXFUL TA NISANTA KANTA DA DAGA BA DA KOWANNE IRIN NAU'IN GARANTI, KO TALLA, KO SHAWARA GAME DA WANI DALILI, IYA MIZANIN ƘOLOLUWAR ABIN DA DOKA TA TANADAR. PAXFUL BA TA BA DA WANI GARANTI NA CEWA ZA A CI GABA DA IYA HULƊA DA KAFAR INTNAET ƊIN, KOWANNE NAU'I NA HARƘALLOLI, KO KUMA KOWANNE ABUN DA KE CIKIN KAFAR BA TARE DA KATSEWA KO MATSALA BA. PAXFUL BA ZA TA ƊAUKI ALHAKIN DUK WATA MATSALA DA TA AUKU SAKAMAKON NA'URAR WASU MUTANE NA DABAN BA KO FASAHARSU, KO KUMA KOWANE NAU'IN KATSEWA KO HASARA DA MAI ASUSU ZAI YI. KA YARDA KUMA KA AMINCI DA CEWA BA KA SAKANKANCE KAN WATA MAGANA BA KO WATA FAHIMTA, WACCE TAKE RUBUCE KO WACCE TAKE CIKIN SAUTIN MAGANA, DA KE DA DANGANTAKA DA AMFANINKA DA WANNAN KAFA. BA TARE DA TAƘAITAWA BA, KA YARDA KUMA KA AMINCE DA HAƊARURRUKAN DA KE TATTARE DA AMFANI DA KUƊAƊEN INTANET WAƊANDA SUKA HAƊA DA (AMMA BA SU TAƘAITA GA WAƊANNAN BA), MATSALAR NA'URA WANDA AKE KALLO, MATSALAR NA'URA WANDA BA A KALLO, MATSALAR INTNAET, MATSALAR SOFWAYA, KATSALANDAN NA WANI DABAN WANDA KA IYA HAIFAR DA HASARA KO RASHIND AMAR KAIWA GA ASUSUNKA KO LALITARKA KO SAURAN BAYANAN MAI ASUSU, MATSALAR UWAR GARKE KO ƁACEWAR BAYANAI. KA YARDA KUMA KA AMINCE CEWA PAXFUL BA ZA TA ƊAUKI ALHAKIN KOWANE NAU'IN GAZAWA TA ƁANGAREN AIKA SAƘO BA, KO MATSALOLIN DA SUKA SHAFI KATSEWA, KO SAURAN MATSALOLI, KO JINKIRI YAYIN AMFANI DA KAFAR, KO DA KUWA MENE NE YA YADDASA SU.

BABU WANI ABIN DA ZAI SA PAXFUL, ABOKAN HAƊIN GUIWARTA DA SAURAN MASU GUDANAR DA AL'AMURA, KO WANI DAGA CIKIN MA'AIKATANSU, DARACTOCI, WAKILAI, MA'AIKATA, MASHAWARTA, MA'AIKATAN TUNTUƁA KO WAKILAI, SU ƊAUKI ALHAKIN (A) KOWANE ADADIN KUƊI DA YA HAURA JIMILLAR DARAJAR KUƊIN GUDANARWA DA KA BIYA NA WANI AIKIN DA SHI NE SADIYYAR JAWO BUƘATAR ƊAUKAR MATAKI A CIKIN WATANNI SHA BIYU (12) KAFIN A SAMU HASARAR KO (B) KOWANE NAU'IN HASARAR RIBA, FAƊUWAR DARAJA KO KASUWANCI, KOWANE IRIN NAU'IN HASARA, DAMEJI, ƁACI KO GURƁATAR BAYANAI KO KOWANE NAU'IN KAYA DA BA A GANI KO AKA SAMU BAƁIN ABU TA HANYA TA MUSAMMAN, TSAUTSATSI, A KAIKAICE, KO HANYAR DA BA A GANI, KO SAKAMAKON FARUWAR WANI ABU, KO DA HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON KWANTIRAGI, SAƁA ƘA'IDA, RASHIN LURA, ALHAKIN AIKATAWA KAI TSAYE, KO WANI ABU NA DABAN, WAND AYA FARU GAME DA KO YAYIN HULƊAYYA AMINTACCIYA KO WACCE BA AMINTACCIYA BA DA KAFAR KO AYYUKAN, KO WANNAN YARJEJENIYA, KO DA AN TUNTUƁI AMINTACCEN WAKILIN PAXFUL KO YA SAN DA AL'AMARIN KO KUMA YA SAN DA WANNAN MATSALA NA IYA AUKUWA, SANNAN DA GAZAWAR DUK WATA HANYAR SAMAR DA MAFITA KO WANI ƁANGARE MAI AMFANI DAGA GARE TA DA ZAI TAIMAKA WA WANNAN AL'AMARI, SAI DAI IDAN DOKA TA GANO CEWA WANNAN HASARA TA SAMU NE SAKAMAKON BAYYANANN SAKACIN PAXFUL, DAMFARA, AIKATA BA DAIDAI BA BISA NIYYA KO KARYA DOKA DAGA CIKIN GIDA. WASU DOKOKI BA SU BA DA DAMAR WAREWA KO TAƘAITA NAU'UKAN HASARA DA SUKA AUKU BISA TSAUTSAYI KO SAKAMAKON WANI AIKI BA, SABODA HAKA, TAƘAITAWAR DA KE NAN SAMA BA DOLE NE YA YI AMFANI A KANKA BA.