DOKOKIN AIKIN Paxful Inc.

WANNAN YARJEJENIYA NA ƘUNSHE DA BAYANAI MASU MATUƘAR MUHIMMANCI DANGANE DA 'YANCINKA DA NAU'IN DA SUKA RATAYA A KANKA, DA KUMA YANAYE-YANAYE, IYAKOKI DA KEƁANCEWA DA KA IYA SHAFAR KA. DAURE KA KARANTA A NITSE.

Waɗannan Dokokin Aiki da duk waɗansu gyare-gyare da ƙarin bayanai da za a iya yi musu a nan (“Yarjejeniyar”) ya kasance yarjejeniya bisa doka wadda ta shafi ayyukan da Paxful ke maka, wanda ya haɗa da samar maka da muhallin kasuwanci domin ba da dama ga masu saye da masu sayar da "Dukiyoyin Kan Intanet" (a fahimci waɗannan dokoki a matsayin gama-gari da ke ƙunsar kuɗaɗen intanet irin su Bitcoin, Tether, da sauransu, waɗanda lalitar Paxful ke hulɗayya da su) su gudanar da harƙalloli tsakanin junansu (“Muhallin kasuwancin”), gudanar da ayyukan da suka shafi samarwa da adana lalitar kan intanet, adanawa da tura Dukiyoyin Kan Intanet yayin da aka buƙaci a yi hakan bayan kammala sayen Dukiyoyin Kan Intanet da dukkannin sauran nau'ukan ayyuka da aka yi bayani a cikin wannan Yarjejeniya (a kammale “Ayyukan” sannan a keɓance, “Aiki”) wanda Paxful, Inc. ke samarwa da dukkannin sauran abokan haɗin guiwarta, ciki har da, amma bai taƙaita ba ga Paxful USA, Inc.(a jimlace, “Paxful” ko “mu” ko “mu” ko “kamfanin”) zuwa gare ka a matsayin mutum guda (wanda kumadu aka sani da “mai asusu” ko “kai”). Paxful.com da dukkannin ayyukanta sun kasance mallaki kuma suna gudana ƙrƙashin Paxful. Ƙa'idojin Sirrantawa, Ƙa'idojin Kuki, da Izinin Sa Hannun Kan Intanet.

WAƊANNAN DOKOKI SUNA BUƘATAR AMFANI DA TSARIN YANKE HUKUNCI DOMIN SASANTA JAYAYYA KOMA BAYAN ZUWA KOTU KO ƊAUKAR MATAKI A ƘUNGIYANCE.

Idan ka yi rajista domin amfani da asusu a paxful.com, ko wata kafar intanet da ke da alaƙa da ita, APIs, ko manhajojin waya, ko duk wasu URLs da Paxful ke gudanarwa (a jimlace “Kafar Paxful” ko “Kafar”), to ka aminta da cewa ka karanta cikin tsanaki, ka fahimta, sannan ka yarda da dukkannin dokoki da ƙa'idojin da ke cikin wannan Yarjejeniya ciki har da Ƙa'idojin Sirrantawa, Ƙa'idojin Kuki, da Izinin Sa Hannun Kan Intanet.

DARAJAR DUKIYOYIN KAN INTANET NA IYA HAWA KO FAƊUWA SANNAN ZA KA IYA HASARAR KUƊI YAYEN SAYE, SAYAR DA, ADANA, KO SANYA HANNUN JARI A HARKAR DUKIYOYIN KAN INTANET. KA YI ZAƁI CIKIN NATSUWA GAME DA IRIN KASUWANCI KO ADANA DUKIYOYIN KAN INTANET YA DACE DA KAI TA LA'AKARI DA YANAYIN TATTALIN ARZIKINKA.

Game da Paxful da Ayyukanta

Paxful ya kasance kasuwar mutum-zuwa-mutum da ke kan gaba wajen ba da damar saye da sayar da Kadarorin Intanet a inda masu sayarwa ke karɓar kuɗi ta hanyoyin biyan kuɗi sama da 300 a matsayin biya ga Kadarorin Intanet nasu. Ana tattauna hanyoyin biyan kuɗi a matakin mutum-zuwa-mutum a tsakanin masu saye a Kasuwa (“Masu saye”) da masu sayarwa a Kasuwa (“Masu sayarwa”). Masu amfani da kafarmu su ke aminta da hanyoyin biyan kuɗin da za a yi amfani da su wajen kammala harƙalla sannan duk wani haƙƙin amfani da waɗannan hanyoyin biyan kuɗi ya rataya a kansu bisa tsarin doka.

Sannan Paxful na gudanar da ayyukan da suka shafi samar da lalitar kan intanet ta hanyar kamfanin da ke jagorancin harkar samar da lalitocin kan intanet a duniya. Tsarin amfani da kafarmu na game-duniya na ba da damar ɗora tayi na saye ko sayar da Dukiyoyin Kan Intanet cikin hanyoyi da dama masu aminci. Haƙƙi ne a wuyan mai ƙirƙiran tayi na ya jero dokokin harƙallar, ciki har da hanyoyin biyan kudin da za a iya biyan Mai Sayarwar ta amfani da su. Da zarar wani mai asusu a Paxful ya zabi tayin, za a kulle Dukiyar Kan Intanet ɗin Mai Sayarwar a matsayin wani mataki na gudanar da harƙalla (wanda muke kira da "Tsarin Adana na Paxful") har sai an kammala dukkannin abubuwan da suka dace a yi domin kammalar kasuwancin. Idan aka kammala kasuwanci, za a buɗe Dukiyoyin Kan Intanet sannan Mai Sayarwa ya tura su zuwa ga Mai Saye bayan Mai Saye ya bi dukkannin ƙa'idojin kasuwancin sannan an tabbatar da cewa ya tura kuɗi sannan sun kai zuwa ga Mai Sayarwa. PAXFUL BA TA TSAYAWA A MATSAYIN MAI GUDANAR DA BIYAN KUƊI. DUKKANNIN ABUBUWAN DA SUKA SHAFI ƊAUKAR ALHAKIN TURAWA DA KARƁAR KUDI DA TANTANCE INGANCIN HARƘALLAR SUN RATAYA NE A KAN MAI SAYE DA MAI SAYARWA. Za mu mayar wa Mai Sayarwa Dukiyar Kan Intanet ɗin da ke kulle idan Mai Saye ya zabi da ya soke harƙallar. Mai sayarwa ba zai iya soke harƙallar ba a kowace gaɓa. Zaɓin da Mai Sayarwa ke da shi kawai shi ne na buɗe Dukiyar Kan Intanet ɗin da tura ta zuwa ga Mai Saye. An yi haka ne domin ba wa Mai Saye kariya. Idan Mai Sayarwa na buƙatar ka soke kasuwanci kasancewar Mai Saye ba ya bin ɗokokin harƙallar, to dole ne ya buɗe jayayya sannan ya bayyana dalilinsa na son soke harƙallar kamar yadda aka yi ƙarin bayani a Sashe na 8 na wannan Yarjejeniya. Harƙalloli a kan Kafarmu na gudana ne tsakanin Masu Saye da Masu Sayarwa. Kamar haka kuma, Paxful ba ta da hannu cikin kowace harƙalla.

Lalitar kan intanet da Paxful ke samarwa ya kasance cikin tsari mai tsaro na ajiyewa, turawa, da karɓar kuɗin intanet. Paxful ba ta ajiyewa ko tsare kowane nau'in Ɗukiyar Intanet. Ana ajiye Dukiyoyin Intanet ne a kan kafafensu ko a tsarin blockchains. Dukkannin harƙallolin kuɗin intanet na gudana ne a cikin fasahar kuɗin intanet amma ba a kan Paxful ba. Babu garantin cewa harƙallar za ta gudana a kan fasahar kuɗin intanet. Paxful na da damar dakatar da gudanuwar wata harƙalla idan doka ta buƙaci hakan ko idan muka ɗauka cewa harƙallar ta ci karo da dokoki da ƙa'idojinmu da ke cikin wannan Yarjejeniya. Ka aminta cewa ka ɗauki alhakin dukkannin harƙallolin da za su gudana a ƙarƙashin lalitarka sannan ka karɓi dukkannin kasadar da ta shafi samun damar kaiwa ga lalitarka ko da izini ne ko ba da izini ba, iya ƙololuwar yadda doka ta ba da dama.

  1. GABA ƊAYA

    1. Muna da damar gyarawa, sabuntawa, sauyawa, ko bitar wannan Yarjejeniya a kowane lokaci, yayin da muka ga dama sannan ba tare da mun ba da sanarwar cewa za mu yi hakan ba. Duk wasu sauye-sauye da suka shafi ta'ammulinka da Ayyukan za su fara amfani ne bayan an ɗora sauye-sauyen a Kafar Paxful amma ba za su shafi abubuwan da suka gabata ba. Idan ka ba mu adireshin imel, zamu iya sanar da kai ta imel cewa an yi bitar Yarjejeniyar. Idan ba ka yarda da dokokin Yarjejeniyar da aka yi bita ba, mafitar da kake da ita wadda ta kasance guda ɗaya ita ce ka katse hulɗayyarka da Ayyukan sannan ka kulle asusunka.
    2. Haƙƙi ne a kanka da ka karanta Yarjejeniyar a nitse sannan ka riƙa bibiyar Yarjejeniyar lokaci zuwa lokaci kamar yadda aka ɗora a kan Kafar Paxful. Idan ka ci gaba da amfani da Ayyukanmu, hakan na nuna cewa ka aminta da Yarjejeniyar da ke ci a wannan lokaci.
    3. Idan Paxful ba ta yi ba, ko ta yi jinkirin zartarwa ko ta zartar da wani ɓangare na abin da Yarjejeniyar ta ƙunsa, kada a ɗauki hakan a matsayin dama ko janye wani daga cikin 'yancin da muke da shi ko mataki da za mu iya ɗauka.
  2. ASUSU DA RAJISTA

    1. Domin samun damar yin amfani da wannan Tsari, akwai buƙatar ka ƙirƙiri asusu a kan Kafar Intanet tamu. Yayin gudanar da rajistar za mu tambaye ka game da wasu bayanai waɗanda suka haɗa da sunanka, adireshinka da wasu keɓantattun bayanai domin tantance shaidarka. Za mu iya yanke shawarar ƙin buɗe maka asusu idan muka ga dama. Ka yarda kuma ka aminta da cewa ka kasance: (a) wanda ya kai shekarun da doka ta ba shi damar amincewa da wannan Yarjejeniya; sannan (b) ba a dakatar da kai ko a kore ka daga amfani da Tsarinmu ba a baya.
    2. Yayin da ka ci gaba da amfani da asusunka, hakan na nuna ka aminta da cewa za ka yi amfani da Ayyukan da muke gudanarwa ne kawai domin karan kanka sannan ba za ka yi amfani da asusunka a matsayin ɗan-tsakiya ba ko zagin kowane mutum na daban ko rukunin mutane ba. Sai ko idan a bayyane Paxful ta ba ka dama, asusu guda kawai aka ba ka damar mallaka. Sannan ba a ba ka damar sayarwa, ba da aro, amfani tare da wani ko bayyana asusunka ko bayanan da za a iya amfani da su wajen shiga asusunka ga wani mutum da ba kai ba.Kai tsaye haƙƙini a kanka da ka tabbatar da ingantaccen tsaro a kan dukkannin da kuma kowanne daga cikin sunayenka na mai asusu, adiresoshin imel, kalmomin sirri, lambobin matakin tsaro na biyu ko kowaɗanne lambobi ko bayanai na daban da kake amfani da su wajen kai wa ga Ayyukan. Dole ne asusunka ya kasance bai ƙunshi bayanan yaudara ko na damfara ba. Ƙirƙirar bayanan ƙarya na asusunka, yin ƙarya game da ƙasarka ko gabatar da fayilolin shaida na damfara, duk abubuwa ne da aka hana kai tsaye.
    3. Yayin ƙirƙirar asusunka, ka aminta da ka turo mana bayanan da muka buƙata domin tantance shaida da kuma binciken almundahana na kuɗi, zamba, ko wani nau'in laifi da ya shafi kuɗi sannan ka ba mu damar adana waɗannan bayanai. Akwai buƙatar ka kammala wasu matakan tantancewa kafin a ba ka damar amfani da Tsarin, wanda ya shafi matakan da za su iya sauyawa sakamakon bayanai da ake karɓa waɗanda suka shafe ka a-kai-a-kai. Bayanan da muƙe buƙata za su iya haɗawa da keɓantattun bayanai kamar sunanka, adireshi, lambar waya, adireshin imel, kwanan watan haihuwa, lambar social security, lambar haraji, da katin shaida na gwamnati. Yayi gabatar mana da wannan ko kuma wani bayani na daban da za mu iya buƙata, ka tabbatar da cewa dukkannin bayanan na gaskiya ne, daidai suke, sannan babu yaudara a ciki. Ka yarda da cewa za ka sanar da mu cikin gaggawa yayin da wani daga cikin bayanan ya samu sauyi. KA BA MU DAMAR MU YI BINCIKE, KO DAI KAI TSAYE KO KUMA TA HANYAR WASU MUTANE NA DABAN, GAME DA ABUBUWAN DA MUKA GA SUN ZAMA DOLO MU TANTANCE GAME DA SHAIDARKA KO MU KARE KA TARE DA KARE KANMU DAGA FAƊAWA TARKON YAUDARA KO WASU LAIFUKA DA SUKA SHAFI KUƊI, SANNAN MU YAKE HUKUNCIN DA MUKE GANIN YA DACE TA LA'AKARI DA SAKAMAKON WAƊANNAN BINCIKE. YAYIN GUDANAR DA WAƊANNAN BINCIKE, KA AMINTA DA DACEWA ZA A IYA BAYYANA BAYANANKA DOMIN BA DA MISALI DA KUMA KARE FAƊAWA TARKON DAMFARA KO A HUKUMOMIN HANA LAIFUKAN DA SUKA SHAFI KUƊI SANNAN WAƊANNAN HUKUMOMI NA IYA BA DA CIKAKKIYAR AMSA GA TAMBAYOYINMU.
    4. Idan kana amfani da Ayyukanmu a madadin tawagar da doka ta aminta da ita kamar kamfanin haɗin guiwa, to kana wakilta kuma ka aminta da cewa: (i) kamfanin yana kan tsari yadda ya kamata sannan yana wanzuwa ƙarƙashin dokokin wurin da yake; sannan (ii) kana da cikakken izini daga kamfanin domin ka wakilce shi. Asusun haɗin guiwa da aka tantance ya kasance mallaki na kamfanin kawai sannan mutumin da ya yi masa rajista ne kaɗai zai iya amfani da shi. Ba a yarda wasu mutane na daban ko kamfanoni su yi amfani da asusun haɗin guiwar ba. Asusun haɗin guiwa da aka tantance, an ba su waɗannan keɓantattun damarmaki:

      • Asusun haɗin guiwa da aka aminta da shi na iya ƙunsar asusai daban-daban da ake amfani da su a kowane lokaci, idan dai dukkanninsu kamfanin ya tantance su sannan masu gudanar da su sun kasance ma'aikatan kamfanin wanda Paxful ta riga ta aminta da shi a bisa radin kanta;
      • Asusun haɗin guiwa zai iya ƙunsar tayi guda ɗaya ne kawai a lokaci guda. Ba a ba da damar samun tayi daban-daban daga sauran asusai na haɗin guiwar ba waɗanda suka shafi harƙalla guda.
    5. Haƙƙi ne da ke kanka ka ƙirƙiri kalmar sirri mai ƙarfi sannan ka tabbatar da zaro mai inganci tare da gudanar da dukkannin IDs, kalmomin sirri, ba da haske, keɓantattun lambobin ganewa (PINs), mabuɗan API ko duk wata lamba ta daban da kake amfani da ita wajen kaiwa ga Ayyukanmu. Yayin da aka samu ɓacewa ko wani ya kai ga samun waɗannan bayanai da/ko kuma keɓantattun bayanai, to hakan na kai ga ka rasa samun damar kai wa ga asusunka sannan yana iya kai ga a maka satar wata Dukiyar Intanet da/ko kuma kuɗaɗe da ke da dangantaka da asusunka, wadanda suka haɗa da hanyoyin biyan kuɗin da ka haɗa da asusun. Haƙƙi ne da ke kanka ka tabbatar adireshin imel, lambar waya, da sauran bayanan tuntuɓa sun kasance waɗanda suke aiki a kan furofayil ɗin asusunka domin samun damar duk waɗansu sanarwa da za mu tura maka su riƙa kaiwa gare ka. Kada ka taɓa ba wa wani damar kaiwa ga kwamfutarka ko ka bayyana fuskar kwamfutarka ga wani mutum na daban yayin da kake cikin asusunka. Babu alhakin da zai hau kanmu ya yin da aka samu wata hasara sakamakon bayanan shiga asusunka ya kai ga hannun wani wanda kuma ba laifin Paxful ba ne sannan/ko kuma ya faru ne sakamakon ba ka bi ba ko ba ka yi amfani da wani daga cikin sanarwar da muke tura maka ba.
    6. Kafin samun damar amfani da Ayyukanmu, akwai buƙatar ka cika wasu ƙa'idoji na doka na ƙsarka da/ko kuma jahar da kake zaune. Idan ka aminta da waɗannan dokoki a cikin wannan Yarjejeniya, to ka tammbatar da cewa ka bibiyi dokoki da ƙa'idojin wurin da kake sannan kana sane da su, kuma ka cika dukkannin waɗannan abubuwan da ake buƙata. Sakamakon abubuwan da aka hana ƙarƙashin doka ko tsarin gudanarwa, ba ma gudanar da harƙallolinmu a wasu wurare. Idan ka aminta da dokokin da ke cikin wannan Yarjejeniya, to hakan na nuna ka tabbatar da cewa kai ba mazaune ba ne na ire-iren waɗannan wurare da ba ma gudanar da harƙallolinmu a wurin sannan dokokin wuraren ba sa aiki a kanka.
    7. Ba dole ne mu samar da waɗannan Harƙalloli ba ga dukkannin kasuwanni da muhallan shari'a sannan ba dole ne mi sanya iyakoki ko mu hana amfani da ɗaukacin ko wani ɓangare na Ayyukan da muke samarwa ba a wasu muhallan shari'a (“Iyakantattun Muhallan Shari'a”). A wannan lokaci, Iyakantattun Muhallan Shari'a sun haɗa da waɗanda aka bayyana a kan “Jerin Ƙasashen da Aka Haramta wa Harƙalla”, da Jahohin Washington da New York. Bugu da ƙari, mazauna Jahar Texas ba su da damar gudanar da Harƙallolin kuɗin intanet, Tether (USDT). Kada ka yi yunƙurin shiga Harƙallolinmu idan kana zaune a ɗaya daga cikin waɗannan Iyakantattun Muhallan Shari'a. Kada ka yi ƙoƙarin kauce wa duk wani iyakancewa da aka samar game da Harƙallolin, kamar ta hanyar sauya adireshinka na IP ko bayar da bayanin da ba na gaskiya ba game da wurin zamanka.
  3. MUHALLIN DOKA, YANKE HUKUNCI DA GUDANUWAR DOKA

    1. Wannan yarjejeniya da kuma amfaninka da Kafar da Ayyukanta za su kasance ƙarƙashin dokoki da ƙa'idojin Jahar Delaware, ba tare da wani keɓancewa ba sakamakon ƙa'idojin saɓanin dokoki.
    2. Yanke hukunci. Kai da Paxful kun aminta da cewa duk wani saɓani da ya taso daga ko wanda ke da dangantaka da wannan Yarjejeniya ko Ayyukan, to za a sasanta shi ne ƙarƙashin matakan yanke hukunci, a matakin mutane masu zaman kansu, daidai da yadda dokokin yanke hukunci na Ƙungiyar Yanke Hukunci ta Amurka suka samar wanda ke da dangantaka da jayayyar da suka shafi mai amfana da haja (wanda za a iya samu a https://www.adr.org/rules). Ta la'akari da abubuwan da muhallin doka ke buƙata, ko mai amfana da hajoji da ke da ƙorafi (ɗaiɗaikun mutanen da harƙallolinsu sun shafi abubuwan da za su yi amfani da su a karan kansu, iyali, ko gidan da suke) na iya zaɓar su kai ƙorafinsu zuwa ƙananan kotuna saɓanin muhallin doka idan dai matsalar ta shafi 'yar ƙaramar tuhuma sannan ta shafi mutum guda ne kawai (wanda ba ya cikin wata tawaga kuma ba wakilci yake yi ba).

      JANYE DAMAR AIKI CIKIN RUKUNI: IYA ƘUREWAR YADDA DOKA TA BA DA DAMA, ZA A GABATAR DA DUKKANNIN TUHUMA NE KAWAI A MATAKIN ƊAIƊAIKUN MUTANE, AMMA BA A MATSAYIN RUKUNI BA KO MAMBA NA WANI RUKUNI KO TAWAGA DA KE ƊAUKAR MATAKI A TARE, KO A MATSAYIN WAKILI (WANDA A KAMMALE AKE KIRA DA "AIKIN RUKUNI"). MAI YANKE HUKUNCI BA ZAI ƊAUKE ƘORAFIN SAMA DA MUTUM GUDA BA KUMA BA ZAI YANKE HUKUNCI A KAN WANI ABU DA YA SHAFI RUKUNIN JAMA'A BA. KA AMINTA DA CEWA, IDAN KA YARDA DA WAƊANNAN DOKOKI, KAI DA PAXFUL KUNA KAWAR DA DUK WATA DAMA NA FUSKANTAR SHARI'A A ƘUNGIYANCE SANNAN KANA JANYE DUK WATA DAMA KO 'YANCIN FUSKANTAR PAXFUL A MATSAYIN RUKUNI KO TAWAGA.

      Dokar Yanke Hukunci ta Ƙasa, 9 U.S.C. §§ 1-16, tana cikakken aiki a kan yanke hukuncin. Mai yanke hukunci zai kasance mutum guda, wanda yake tsaka-tsakiya (ba tare da bin ra'ayin ɓangare guda ba), sannan dole ne wannan ya faru a Jahar Delaware, ko wani wurin da aka yi yarjejeniyar a haɗu, sannan cikin harshen Ingilishi. Mai yanke hukuncin da iya yanke duk wani hukunci da kotu ko doka za ta iya yankewa, wannan ya haɗa da kuɗin mai shari'a idan doka ta ba da damar hakan, sannan hukuncin da aka yanken na iya amfani a kotu inda kotu za ta tabbatar da an bi shi. Za a iya zaman sauraren hukuncin gaba-da-gaba ko ta kan waya, wanda ya danganta da buƙatarka sannan mai yanke hukuncin na iya amfani da bayanan da aka samar kawai wajen yanke hukunci ba tare da ya saurari ɓangarorin biyu baki-da-baki ba. Ɓangaren da ke jagaba a kowane zama na tabbatar da wannan Yarjejeniya na ɗauke da haƙƙin ba da farashin kuɗin mai shari'a.

      Idan mai yanke hukunci(masu yanke hukunci) ko jami'i mai yanke hukunci zai sanya cajin kuɗi a kanka, to za mu biya ka, yayin da ka buƙaci hakan, idan dai waɗannan kuɗaɗe ko caji da aka yi ba za su haura wadanda za a kashe ba da a ce kotu aka je. Sannan za mu biya ƙarin kuɗaɗe idan dokokin jami'i mai yanke hukuncin sun nuna haka ko dokar da ke ci a wurin ta nuna haka. Saɓanin waɗannan, kowane ɓangare shi zai ɗauki nauyin duk wasu kuɗade, kamar kuɗin lauya wanda ɓangaren za su iya buƙata.

    3. Idan wani mai yanke hukunci ko wata kotun Amurka ta bayyana wani ɓangare na daga wannan a matsayin marar inganci ko wanda ba za a iya sanyawa a kan mutane ba a ɗungurungum ɗinsa ko wani ɓangarensa, to wannan ba zai shafi inganci da tasirin sauran ɓangarorin dokoki da ƙa'idojin ba. Duk waɗansu kanu-kanu da ke cikin wannan Yarjejeniya suna nan ne kawai a bisa dalailai na ƙarin bayani amma ba su kasance an samar da su domin ɗora wata doka daga cikin wannan Yarjejeniya ba.
  4. BAYANIN SIRRI DA TSARO

    1. Muna matuƙar ƙoƙari wajen ɗaukar ƙwararan matakai na kare keɓantattun bayananka. Duk da haka, ba za mu iya ba da garanti na tsaron duk wani bayani ba da ka sanya a kan intanet. Ka aminta da duk wani haɗari da ke ƙunshe cikin samar da bayani da gudanar da harƙalloli a kan intanet sannan ba za ka tuhume mu ba yayin da aka samu matsala a ɓangaren tsaro sai dai idan hakan yan faru ne sakamakon sakacinmu.
    2. Daure ka duba bayanan sirrantawarmu: https://paxful.com/privacy.
  5. BABU GARANTI, TAƘAITAWAR ƊAUKAR NAUYI DA KARƁAR KASADA

    1. ANA SAMAR DA WAƊANNAN AYYUKA NE A BISA "KAMAR YADDA YAKE" "SANNAN KAMAR YADDA AKAWAI SHI A" YANAYIN DA BA MU BA DA WANI GARANTI BA KO WANE IRI NE, KO DA WANDA MUKA BAYYANA NE KO WANDA YAKE KASANCEWA A SAKAMAKON WANI YANAYI.. PAXFUL TA NISANTA KANTA DA DAGA BA DA KOWANNE IRIN NAU'IN GARANTI, KO TALLA, KO SHAWARA GAME DA WANI DALILI, IYA MIZANIN ƘOLOLUWAR ABIN DA DOKA TA TANADAR. PAXFUL BA TA BA DA WANI GARANTI NA CEWA ZA A CI GABA DA IYA HULƊA DA KAFAR INTNAET ƊIN, KOWANNE NAU'I NA HARƘALLOLI, KO KUMA KOWANNE ABUN DA KE CIKIN KAFAR BA TARE DA KATSEWA KO MATSALA BA. PAXFUL BA ZA TA ƊAUKI ALHAKIN KOWANE NAU'IN KATSEWA KO HASARA DA MAI ASUSU ZAI YI BA. KA YARDA KUMA KA AMINCI DA CEWA BA KA SAKANKANCE KAN WATA MAGANA BA KO WATA FAHIMTA, WACCE TAKE RUBUCE KO WACCE TAKE CIKIN SAUTIN MAGANA, DA KE DA DANGANTAKA DA AMFANINKA DA WANNAN KAFA. BA TARE DA TAƘAITAWA BA, KA YARDA KUMA KA AMINCE DA HAƊARURRUKAN DA KE TATTARE DA AMFANI DA KUƊAƊEN INTANET WAƊANDA SUKA HAƊA DA (AMMA BA SU TAƘAITA GA WAƊANNAN BA), MATSALAR NA'URA WANDA AKE KALLO, MATSALAR NA'URA WANDA BA A KALLO, MATSALAR INTNAET, MATSALAR SOFWAYA, KATSALANDAN NA WANI DABAN WANDA KA IYA HAIFAR DA HASARA KO RASHIN DAMAR KAIWA GA ASUSUNKA KO LALITARKA KO SAURAN BAYANAN MAI ASUSU, MATSALAR UWAR GARKE KO ƁACEWAR BAYANAI. KA YARDA KUMA KA AMINCE CEWA PAXFUL BA ZA TA ƊAUKI ALHAKIN KOWANE NAU'IN GAZAWA TA ƁANGAREN AIKA SAƘO BA, KO MATSALOLIN DA SUKA SHAFI KATSEWA, KO SAURAN MATSALOLI, KO JINKIRI YAYIN AMFANI DA KAFAR, KO DA KUWA MENE NE YA HADDASA SU.
    2. BABU WANI ABIN DA ZAI SA PAXFUL, ABOKAN HAƊIN GUIWARTA DA SAURAN MASU GUDANAR DA AL'AMURA, KO WANI DAGA CIKIN MA'AIKATANSU, DARACTOCI, WAKILAI, MA'AIKATA, MASHAWARTA, MA'AIKATAN TUNTUƁA KO WAKILAI, SU ƊAUKI ALHAKIN (A) KOWANE ADADIN KUƊI DA YA HAURA JIMILLAR DARAJAR KUƊIN GUDANARWA DA KA BIYA NA WANI AIKIN DA SHI NE SANADIYYAR JAWO BUƘATAR ƊAUKAR MATAKI A CIKIN WATANNI SHA BIYU (12) KAFIN A SAMU HASARAR KO (B) KOWANE NAU'IN HASARAR RIBA, FAƊUWAR DARAJA KO KASUWANCI, KOWANE IRIN NAU'IN HASARA, DAMEJI, ƁACI KO GURƁATAR BAYANAI KO KOWANE NAU'IN KAYA DA BA A GANI KO AKA SAMU BAƁIN ABU TA HANYA TA MUSAMMAN, TSAUTSAYI, A KAIKAICE, KO HANYAR DA BA A GANI, KO SAKAMAKON FARUWAR WANI ABU, KO DA HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON KWANTIRAGI, SAƁA ƘA'IDA, RASHIN LURA, ALHAKIN AIKATAWA KAI TSAYE, KO WANI ABU NA DABAN, WANDA YA FARU GAME DA KO YAYIN HULƊAYYA AMINTACCIYA KO WACCE BA AMINTACCIYA BA DA KAFAR KO AYYUKAN, KO WANNAN YARJEJENIYA, KO DA AN TUNTUƁI AMINTACCEN WAKILIN PAXFUL KO YA SAN DA AL'AMARIN KO KUMA YA SAN DA WANNAN MATSALA NA IYA AUKUWA, SANNAN DA GAZAWAR DUK WATA HANYAR SAMAR DA MAFITA KO WANI ƁANGARE MAI AMFANI DAGA GARE TA DA ZAI TAIMAKA WA WANNAN AL'AMARI, SAI DAI IDAN DOKA TA GANO CEWA WANNAN HASARA TA SAMU NE SAKAMAKON BAYYANANN SAKACIN PAXFUL, DAMFARA, AIKATA BA DAIDAI BA BISA NIYYA KO KARYA DOKA DAGA CIKIN GIDA. WASU DOKOKI BA SU BA DA DAMAR WAREWA KO TAƘAITA NAU'UKAN HASARA DA SUKA AUKU BISA TSAUTSAYI KO SAKAMAKON WANI AIKI BA, A BISA HAKA, TAƘAITAWAR DA KE NAN SAMA BA DOLE NE TA YI AMFANI A KANKA BA.
    3. Ba mu mallaka ba kuma ba mu ke sarrafa akala ba ta matakan softwaya da ke gudanar da harkar Dukiyoyin Kan Intanet. A gaba ɗaya, matakan sun kasance buɗaɗɗu wadanda kowa zai iya amfani da su, kwafa, gyarawa, ko ya tura su. Muna nesanta kanmu daga ɗaukar alhakin duk waɗannan matakai sannan ba za mu iya ba da garanti game da aiki ko gudanuwar abin da ya shafi tsaro a kan intanet ba. Kai tsaye, matakan na iya fuskantar sauye-sauye na bagatatan ga dokokin gudanar da su (waɗanda suka haɗa da “forks”). Kowanne daga cikin sauye-sauyen nan na iya shafar samu, daraja, amfani, da/ko kuma sunan wannan kuɗin intanet. Paxful ba ita ke sarrafa akalar waɗannan sauye-sauye ba game da lokacin faruwarsu da yanayin faruwarsu. Haƙƙi ne a kanka da ka nemi masaniya a kan waɗannan sauye-sauye da ka iya tasowa sannan dole ne ka riƙa bibiyar bayanan da al'umma ke samarwa da bayanan da wataƙila Paxful za ta samar, kafin ka yanke hukuncin ci gaba da wadannan Harƙalloli. Idan aka samu wani ɗaga cikin waɗannan nau'ukan sauye-sauye, Paxful na da damar ɗaukar matakan da wataƙila suka kasance tilas domin ba da kariya ga kafarta, wanda hakan ya haɗa da dakatar da hada-hadar wannan nau'in kuɗin(kuɗaɗen) intanet, da sauran matakai da suka kasance dole. Paxful za ta bi hanyoyin da suka dace domin sanar da kai game da matakan da ta ɗauka game da duk wasu sauye-sauye da aka samu; sai dai kuma, waɗannan sauye-sauye ba a hannunmu suke ba, sanan za su iya faruwa ba tare da Paxful ta sani ba. Matakin da za mu ɗauka game da kowane sauyi da ya faru, abu ne da ya kasance muna da damar gudanar da shi yadda muka so, wanda kuma ya haɗa da idan muka ga dama mu yanke hukuncin cewa ba za mu ci gaba da bin sabon tsarin ba ko kuma mu ɗauki wasu matakai na daban. Ka aminta da ɗaukar kasadar duk wadansu sauye-sauye da za su iya faruwa a Dukiyoyin Kan Intanet sannan ka aminta cea Paxful ba ta da wannu cikin wadannan sauye-sauye sannan alhakin duk wata hasara na faɗuwar darajar kuɗin intanet ba zai ɗoru a kanta ba. Ka aminta da cewa Paxful na da damar yanke hukuncin da ta ga dama game da yadda za ta ɓullo wa duk wasu sauye-sauye da suka faru a kan kuɗaɗen intanet sannan haƙƙi bai rataya a wuyanmu ba na taimaka maka game da nau'ukan kuɗin da ba a amfani da su a kan kafar.
    4. Yayin amfani da Hajojinmu, za ka iya kallon ƙunshiya ko ka yi amfani da wata Hajar da wasu mutane na daban suka samar waɗanda suka haɗa da liƙau da zai kai ka zuwa kafar intanet ɗinsu da kuma hajojin waɗannan mutane (“3ƙunshiyarhajar wasu mutane na daban”). Ba ma ba da tabbaci, runguma ko gudanar da al'amuran ƙunshiyar wasu3na daban sannan babu wani alhaki na waɗannan hajoji na mutane3na daban da zai hau kanmu ta kowace irin siga. Bugu da ƙari, duk waɗansu harƙalloli da za ka gudanar da waɗannan mutane za su kasance ne tsakaninka da su. Ba za mu ɗauki alhakin duk wata hasara ko matsala da ta auku ba kowace iri ce sakamakon harƙallarku, sannan ka fahimci cewa amfaninka da hajojin waɗansu mutan 3na daban, da kuma hulɗarka da waɗannan mutane, abu ne da dukkannin haƙƙinsa ya rataya a wuyanka.
    5. Domin gusar da kokonto, Paxful ba ta gudanar da abin da ya shafi sanya hannun jari, haraji, ko shawara kan shari'a. Paxful ba ta yi rajista da Hukumar Tsaro da Musanye na Amurka ba sannan ba ta gudanar da ayyukand a suka shafi tsaro ko shawara kan sanya hannun jari. Dukkannin harƙalloli a Kasuwarmu na gudana ne bisa tsarin mutum-zuwa-mutum tsakanin Mai Sayarwa da Mai Saye sannan kai ke da hakkin tantancewa idan sanya hannun jari, ko hanyar sanya hannun jari ko wata harƙalla mai kama da wannan ta dace da kai wanda hakan ya shafi keɓantattun manufar kasuwancinka, da yanayin kuɗinka da kuma yadda kake ɗaukar kasada. Daga lokaci zuwa lokaci, za mu iya samar da bayanai masu ilmantarwa game da kafarmu da kayayyakinmu domin mu taimaka wa masu amfani da kafar wajen ƙara sani game da Ayyukanmu. Daga cikin nau'ukan bayanan za a iya samun rubuce-rubuce a kan kafa, muƙalu, liƙau zuwa bayanai a wurin wani mutum na daban, labarai, koyarwa, da bidiyoyi. Bayanan da za a bayar a kan Kafar Intanet ɗin ko kafofin wasu mutane daban ba su shafi shawarwarin sanya hannun jari, ko shawarwari kan kuɗi, ko shawarwari kan kasuwanci, ko kowane irin nau'in shawarwari ba. Sannn kada ka yi wannan fahimta ga kowanne daga cikin ƙunshiyar Kafar Intanet ɗin. Kafin yanke hukuncin saye, sayarwa ko riƙe kowane irin nau'in Kadarorin Intanet, to ka gudanar da bincike na karan kanka sannan ka tuntuɓi masu ba ka shawara kan harkokin kuɗi kafin yanke shawarar sanya kowanne hannun jari. Ba za a tuhumi Paxful ba game da shawarar da ka yanke na saye, sayarwa, ko mallakar Kadarorin Intanet sakamakon bayananan da Paxful ta samar.
    6. Ka aminta da cewa ba za mu ɗauki alhakin duk wani sauyi a farashin Dukiyoyin Kan Intanet ba. Yayin da aka samu wata tangarɗa ko wata Jarabta (kamar yadda aka yi bayani a Sashe na 17), za mu iya aiwatar da ɗaya ko sama da haka na daga cikin waɗannan abubuwa da ke tafe: (a) dakatar da gudanar da Ayyukan; ko (b) hana ka kammala wasu harƙalloli ta yanayr Ayyukan. Ba za mu ɗauki alhakin kowane nau'in hasara ba da ka fuskanta wanda ta samo asali daga matakan da muka ɗauka. Bayan faruwar haka, idan komai ya dawo yadda yake, ka aminta da cewa farashin kasuwa na iya sauyawa sosai da na farashin da ya kasance kafin faruwar al'amarin.
    7. Ba mu ba da garantin cewa Kafar, ko uwar garken da kafar ke kanta sun kasance tseratattu daga baros ko matsaloli ba, ko kuma ƙunshiyarta ya kasance daidai, ko ba za ta taɓa samun katsewa ba, ko kuma cewa za a gyara kowane nau'in koma baya ba. Ba za mu ɗauki alhakin duk wata hasara da ta same ka ba, dangane da abin da ka aiwatar sakamakon dogaro da ɗaya daga cikin bayanan da ke ƙunshe cikin Kafar.
  6. ZARE PAXFUL DA RASHIN TUHUMA

    1. Idan akwai jayayya tsakaninka da mai asusu guda ɗaya ko sama da haka game da Ayyukanmu, to ka zare Paxful, abokan haɗin guiwarta da masu gudanar da ayyuka, da kuma dukkannin jami'ai, daraktoci, ma'aikata, wakilai ɗinta ko ɗinsu, daga kowane nau'i da dukkannin tuhuma, buƙata ko diyya (na kai tsaye da waɗanda suka faru sakamakon waɗansu dalilai) wanda ya kasance kowane iri ne wanda ya faru a bisa kowane irin dalili ne da ke da alaƙa da wannan jayayya. Ka aminta da cewa ba za ka tuhumi Paxful ba, abokan haɗin guiwarta ko kowanne daga cikin jami'ansu, daraktocinsu, ma'aikatansu, da wakilansu ba, game da kowanne tuhuma ko neman diyya (ciki har da kuɗin shari'a da kowane caji, ko tara da aka wata hukumar gudanarwa ta ɗora maka) wanda ya faru sakamakon ka saɓa wannan Yarjejeniya ko ka karya wata doka, ko ƙa'ida, ko 'yancin wani mutum na daban.
  7. HARƘALLOLI A MUHALLIN KASUWANCIN PAXFUL

    Kafar na ba wa masu asusu damar neman tayi domin saye ko sayar da Dukiyoyin Kan Intanet.

    Yayin da mai asusu ya buɗe harƙallar saye ko sayar da Dukiyoyin Kan Intanet, to za a gudanar da harƙallar ne ta bin Yarjejeniyar nan da ƙarin dokoki, idan akwai, wanda mai asusu ya zayyana ko abokin harƙallar mai asusun. Za a iya samun bayanai game da matakan saye da sayar da Dukiyoyin Kan Intanet a kan Paxful a nan https://support.paxful.com/support/solutions/150000191612.

    Waɗannan dokoki gama-gari sun hau kan kowace harƙalla da aka yi bayani a ƙasa:

    1. Sayen Dukiyoyin Kan Intanet ta hanayar nema da tayi.

      Yayin sayen Dukiyoyin Kan Intanet a Muhallin Kasuwancin Paxful:

      1. Ba a karɓar wasu kuɗaɗen caji na Tsarin Adana na Paxful a matsayin wani ɓangare na harƙalla wadda Masu Saye za su biya a Muhallin Kasuwancinmu.
      2. Tayi daga mutane a kan Paxful na ɗauke da dokoki da ƙa'idojinsu sannan kowane tayi na iya bambanta ta fannin farashin canji, saurin canji, da sauran dokoki da ƙa'idojin da Mai Sayarwa ya gindaya. Yayin da ka karɓi tayin Mai Sayarwa, to hakan na nuna ka aminta da dokoki da ƙa'idojin tayin. Dokoki da ƙa'idojin da Mai Sayarwa ya zayyana suna aiki a dukkannin yanayi har sai idan sun ci karo da ko sun saɓa wa wannan Yarjejeniya, ko idan sun saɓa wa doka, ko ba su kama hankali ba ko suna da wuyar bi (wanda wannan Paxful ce ke da damar yanke hukuncin yadda ta so), ko idan dukkannin ɓangarorin biyu sun yarda da su saɓa dokoki da ƙa'idojin tayin. HAƘƘI NE A KANKA DA KA KARANTA DOKOKI DA ƘA'IDOJIN TAYIN DA MAI SAYARWA YA GABATAR CIKIN NITSUWA SANNAN KA BI SU YADDA SUKE. IDAN BA KA BI DOKOKI DA ƘA'IDOJIN TAYIN BA, BA ZA A KARƁI KUƊIN DA KA BIYA BA. KADA KA TAƁA TURA KUƊI HAR SAI IDAN KA BI DUKKANNIN DOKOKI DA ƘA'IDOJIN DA AKA ZAYYANA A CIKIN TAYIN. IDAN KA TURA KUƊI BA TARE DA BIN DOKOKI DA ƘA'IDOJIN BA, PAXFUL BA ZA TA IYA TAIMAKON KA BA YAYIN JAYAYYA DOMIN DAWO DA KUƊINKA.
      3. Haƙƙin tantance biyan kuɗi tare da ba da umarnin Buɗe Ɗukiyoyin Kan Intanet daga Ɓangaren Adana na Paxful sun rataya ne a kan Mai Sayarwa ba Paxful ba. Idan Mai Sayarwa bai turo maka Dukiyoyin Kan Intanet ba bayan ka kammala cika dokoki da ƙa'idojinsa, kai tsaye ka ba da rahoton matsalar ta hanyar madannin jayayya da ke cikin ɓangaren tattaunawar kasuwanci. Sashen taimako na Paxful zai duba tare da sasanta jayayyar. Wannan mataki na sasanta jayayya an yi bayaninsa a ƙasa cikin "Sashe na 8 - Jayayya a Kan Harƙalla ta Hanyar Matakin Sasanta Jayayya na Paxful." Idan ba ka bi wannan matakin sasanta jayayya ba, Paxful ba za ta iya taimakon ka a kan al'amarin ba.
    2. Sayar da Dukiyoyin Kan Intanet

      Yayin sayar da Dukiyoyin Kan Intanet a Muhallin Kasuwancin Paxful:

      1. Dole ne masu sayarwa su tantance tare da yin abin da ya kamata bayan an tura musu kudi cikin lokaci, sannan ya kasance cikin ƙayyadadden lokacin da aka bayyana a dokokin tayi. Da zarar Mai Saye ya turo maka kuɗi kamar yadda dokokin tayi suka tanadar, hakki ne a kanka da ka tantance biyan kuɗin cikin gaggawa sannan ka buɗe Kadarorin Kan Intanet daga wurin Adana na Paxful sannan ka tura wa Mai Saye. Idan ba ka bi dokokin da ke kan tayin ba, ba za ka samu damar kaiwa ga Kadarorinka da aka Kulle ba.
      2. A matsayinka na Mai Sayarwa, ka aminta da dukkannin kasada da hasara da zai iya aukuwa sakamakon karya wannan Yarjejeniya yayin sayar da Dukiyoyin Kan Intanet. Haƙƙin biyan duk wani haraji ya rataya a wuyanka. Paxful na cajar kuɗi daga gare ka a matsayinka na Mai Sayar da Dukiyoyin Kan Intanet, wanda kuɗin ya shafi ladar kulle Dukiyoyin Kan Intanet a Ɓangaren Adana na Paxful har lokacin da za a sayar. Sai dai idan Paxful ta ga dama bisa raɗin kanta, ba za ta biya kowane hasara da Mai Sayarwa ya samu ba wanda ya faru sakamakon ko dai karya Yarjejeniyar nan, damfara ko koma bayan haka, sannan ba za mu maido da kuɗin da muka caja ba.
      3. Duk wani kuɗi da aka turo maka, to ka tabbatar da sun iso gare ka tukunna kafin ka buɗe Dukiyoyin Kan intanet daga Ɓangaren Adana na Paxful. Paxful ba za ta ɗauki alhakin hasarar da ka yi ba idan ka buɗe Dukiyoyin Kan intanet kafin ka tantance cewa kuɗi sun shigo gare ka. Dole ne ka kasance mai saurare da ba da amsa ga Mai Saye daga wurinka. Ka cire duk wasu tayi da ba sa aiki.
      4. Ba a yarda ka tallata kafar intanet ɗinka ba a kowanne ɓangare na Muhallin Kasuwancin Paxful (kamar su taƙaitaccen tarihinka, ko ɓangaren tattaunawar kasuanci) wanda zai kai ga saye ko sayar da Dukiyoyin Kan Kintanet a wajen Paxful. A wasu ƙayyadaddun lokuta, ana yarjewa da ka ɗora kafar intanet ɗinka wanda an ƙirƙire ta ne kawai domin Mai Sayarwa ya karɓi kuɗi ta ciki domin kammaluwar harƙallar (misali, amintaccen gudanar da biyan kuɗi na katin debit/credit) a cikin ƙa'idojin harƙallar; idan har an bayyana amfani da waɗannan kafafen intanet a cikin dokokin tayin sannan idan waɗannan kafafen intanet ba su ƙunshi waɗansu tallace-tallace ba ko kuma bayanan tuntuɓarka.
    3. Bin Doka

      1. Paxful da Ayyukanta ba su da haɗi ko alaƙa da, kuma ba sa ƙarƙashin sa hannu ko ɗaukar nauyin wani mutum na daban, wannan ya haɗa da amma bai taƙaita ba ga duk wani mai amfani da katin kuɗi. Alamar kasuwanci, nau'in kamfani da sauran abubuwan da za su sa a gane wani duk sun kasance mallaki na mamallakansu. Paxful da Ayyukanta ba sa ƙarƙashin sa hannu, ɗaukar nauyi, haɗin kai, ko haɗin guiwa ta kowace fuska da waɗannan mamallaka.
      2. Paxful ba ta da lasisin dillancin katin kuɗi sannan ba amintacciyar dilar katin kuɗi ba ne na kowane kamfanin da ke samar da katunan kuɗi. Duk wani katin kuɗi da ka karɓar ta hanyar Muhallin Kasuwancin Paxful to yana da alaƙa da dokoki da ƙa'idojin ɗan kasuwar da ke da mallakin wannan katin kuɗi wanda shi ne (“Mai bayarwa”). Paxful ba za ta ɗauki alhaki ba na duk wani rashin cika ko inganci na Mai Bayarwa(Masu Bayarwa), ko wani cajin kuɗi, ranar daina aiki, hukunci ko dokoki da ƙa'idojin da ke da alaƙa da katin kuɗin Mai Bayarwa wanda aka karɓa ta hanyar Muhallin Kasuwancin Paxful. Idan ka karɓi katin kuɗi daga wurin mai asusu, ya nuna ka aminta da cewa ka karanta dokoki da ƙa'idojin katin kuɗin, sannan ka nuna wa Paxful cewa ka cancanci ka yi amfani da wadannan katunan kuɗi ƙarƙashin dokoki da ƙa'idojin Mai Ba da katin kuɗin, ko ƙarƙashin dokar da ta shafi al'amarin.
      3. AN HANA SAYAR DA KATUNAN DA AKA RIGA AKA SAYAR KO AKA YI AMFANI DA SU A KAN KAFARMU DA MUHALLIN KASUWANCINMU. DOLE NE KA KASANCE MAMALLKIN KATIN KUƊIN SANNAN YAYIN DA PAXFUL TA BUƘTA, KA AMINTA CEWA ZA KA GABATAR MATA DA INGANTACCIYAR SHAIDAR DA KE NUNA KAI NE MAMALLAKIN KATIN KUƊIN (KAMAR RASIDI). PAXFUL BA TA TABBATARWA, WAKILTA KO BA DA GARANTIN CEWA KOWANE HANYAR BIYAN KUƊI DA KE KAN KAFAR YA BA DA DAMAR GUDANAR DA HARƘALLOLI TA PAXFUL, KO KUMA CEWA DUK WATA HANYAR BIYAN KUƊI DA KE KAN KAFARMU NA AIKI LAFIYA ƘALAU A KAN AKFAR. KADA KA YI AMFANI DA HANYAR BIYAN KUƊIN A KAN PAXFUL IDAN MAMALLAKIN HANYAR BIYAN KUƊIN BAI BA DA DAMAR YIN HAKAN BA
      4. HAƘƘI NE A KANKA DA KA BI DUK WASU DOKOKI DA ƘA'IDOJI NA MUHALLIN DOKA(DOKOKI) INDA HARƘALLARKA KE GUDANA.
      5. Dole ne a gudanar da dukkannin harƙalloli a cikin Paxful. An hana gudanar da harƙalloli a wajen Paxful ko yin musanyen bayanan tuntuɓa.
    4. Iyakokin Taransifa. Za mu iya, yayin da muka ga dama, sanya iyakokin takunkumi game da adadi, nau'i ko yanayin gudanar da duk wata harƙallar taransifa, kamar iyaka ga jimillar adadin Dukiyoyin Kan Kintanet da za a iya ɗorawa domin sayarwa.
    5. Babu Garanti. Paxful ba ta ba da garanti ba na cewa za ka iya sayar da Dukiyoyin Kan Kintanet a kan Muhallin Kasuwarta. Kasancewar yanzu ana saye da sayar da Dukiyoyin Kan intanet a Muhallin Kasuwancin Paxful bai zama garanti ba na cewar nan gaba ma za ka iya saye da sayar da Dukiyoyin Kan Kintanet a Muhallin Kasuwancin.
    6. Dangantaka. Babu wani abu daga cikin wannan Yarjejeniya da aka samar da nufin ƙulla wani kasuwancin haɗin guiwa, hukuma, zama abokin shawara ko amintacce, kai da Paxful kun kasance ne kowa na cin gashin kansa.
    7. Daidaiton Bayanai. Kana wakilta sannan ka ba da garantin cewa dukkannin bayanai da ka samar zuwa ga Ayyukan sun kasance daidai sannan kammalallu. Ka aminta cewa Paxful ba za ta ɗauki alhakin duk wata matsala ko ƙetarewa wanda za ka gudanar ba dangane da kowace harƙalla da ka gudanar ƙarƙashin Ayyukan, misali, kamar idan ka rubuta adireshin Lalita ba daidai ba ko idan ka gabatar da bayanan da ba daidai ba. Muna ba ka shawarar ka riƙa duba bayanan harƙallarka cikin natsuwa kafin kammala su yayin gudanar da Ayyukan.
    8. Babu Sokewa ko Gyarawa; Harƙallolin Lalita. Da zarar an tura bayanan harƙalla zuwa ga tsarin kuɗin intanet ta hanyar Ayyukan da muke samarwa, Paxful ba za ta iya taimaka maka ba wajen soke harƙallar ko gyarawa. Paxful ba ta da hannu cikin gudanar da kowane nau'in kudin intanet sannan ba ta da damar sokewa ko gyara kowane nau'in harƙalla. Paxful ba ta ajiyewa ko gade kowane nau'in Dukiyoyin Kan Intanet. Koyaushe Dukiyoyin Kan Intanet suna kasancewa ne a muhallin fasahar da ke tallafe da su ko kuma blockchains. Dukkannin harƙallolin kuɗin intanet suna faruwa ne a cikin farfariyar fasahar kuɗin intanet ɗin, ba a kan Paxful ba. Babu garantin cewa harƙallar zai gudana lafiya ƙalau a farfajiyar fasahar kuɗin intanet ɗin. Paxful tana da damar ƙin gudanar da kowace harƙalla idan doka ta buƙaci hakan ko idan muka ga harƙallar ta saɓa wa dokoki da ƙa'idojinmu da ke cikin wannan Yarjejeniya. Ka aminta cewa za ka ɗauki dukkan alhakin harƙallolin da za su auku a ƙarƙashin Lalitarka sannan ka karɓi dukkannin kasada da ta shafi kaiwa ga Lalitarka ga wanda aka ba wa izini ko wanda ba a ba shi ba, iya ƙololuwar yadda doka ta ba da dama.
    9. Haraji. Haƙƙi ne a kanka ka gano, idan akwai, duk waɗansu haraji da suka dace a biya game da harƙallolin da kake ƙoƙarin gudanarwa a kan Kafar, sannan haƙƙi ne a kanka da ka ba da rahoto tare da biyan haraji yadda yake zuwa ga hukumar haraji da ta dace. Ka aminta cewa ba haƙƙi ba ne da ke kan Paxful da ta gano idan akwai buƙatar biyan haraji ga harƙallolin kuɗin intanet da za ka gudanar sannan ba haƙƙi ne a kanta ba da ta karɓa, ba da rahoto, riƙewa ko gudanar da harƙoƙin haraji da suka shafi duk wata harƙallar kuɗin intanet.
    10. Ƙimar Mai Asusu. Idan ka gudanar da Harƙalla, mukan ba da dama ga masu asusu da su rubuta tsokaci game da hulɗayyarka da su. Sannan mukan ba da dama ga masu asusu da su rubuta rahoto idan sun tabbatar cewa ka karya wannan Yarjejeniya ta kowace hanya. Waɗannan rahotanni abubuwa ne na sirri, amma za mu iya yin amfani da su a muhallin jayayya kamar yadda aka bayyana a Sashe na 8.
    11. Tarihin Harƙalla. Za ka iya kallon tarihin harƙallarka ta cikin Asusunka. Ka aminta cewa idan Na'urarmu ta kasa samar da wannan tarihin harƙalla, to hakan ba zai shafa ba ko ba zai sa dokokin harƙallar su daina aiki ba.
    12. Paxful Pay. Paxful ta ba da dama ga waɗansu 'yan kasuwa domin su riƙa karɓar Paxful a matsayin hanyar biyan kuɗi domin biyan kuɗaɗen kaya da na ayyuka a kan intnaet (“Yardaddun 'Yan Kasuwa”). Za ka iya biyan Yardajjen Ɗan Kasuwa ta hanyar zaɓar zabin "Paxful Pay" domin biyan kuɗi. Paxful Pay zai kai ka zuwa Muhallin Kasuwancinmu domin kaiwa ga Dukiyoyin Kan Intanet da kake da su a cikin asusunka ko a haɗa ka da Mai Sayarwa. Idan ka sayi Dukiyoyin Kan Intanet a wurin Mai Sayarwa domin kammala harƙallai, to za a yi amfani da dokokin da ke ƙarƙashin Sashe na 7.1 na wannan Yarjejeniya.
    13. Hajojin Ɗan Kasuwa. Paxful ba ta da alhakin duk wasu hajoji ko ayyuka da za ka biya kuɗinsu domin saya daga Yardajjen Ɗan Kasuwa ta amfani da asusunka ko tsarin Paxful Pay. Idan akwai wata jayayya tsakaninka da Yardajjen Ɗan Kasuwa, to ku shawo kan matsalar jayayyar kai tsaye a tsakaninku.
    14. Maidowa, Dawo da Kuɗaɗe. Idan ka biya kuɗin haja ko wani aiki daga wani mutum ta amfani da Asusunka, to zance ya ƙare. Ba ma gudanar da harƙar maidowa ko dawo da kuɗaɗe. Yardajjen Ɗan Kasuwa na iya dawo maka da kuɗi, ba ka katin sito ko katin kuɗi idan ya ga dama wanda wannan zai auku ne bisa tanadin dokokin Ɗan Kasuwar.
    15. Paxful na cazar kuɗaɗen Ayyuka. Za a nuna maka kuɗin da za a caja kafin ka yi amfani da duk wani abin da ke buƙatar a biya masa kuɗi. Duba “Kuɗaɗen Paxful” domin samun ƙarin bayani. Kuɗaɗen da muke caja na iya sauyawa sannan Paxful na da damar sauya farashinta da kuɗaɗen da take caja a kowane lokaci.
  8. JAYAYYA GAME DA HARƘALLOLI TA BIN MATAKAN SASANTA JAYAYYA NA PAXFUL

    1. Jayayya a Kan Harƙalla. A wasu lokuta, hanya mafi sauƙi ta sasamta jayayya ita ce Mai Saye da Mai Sayarwa su tattauna, su yi aiki tare domin gano matsalar da ta auku, sannan su kai matsaya a kanta. Idan Mai Saye da Mai Sayarwa suka kasa samun matsaya, to tawagar taimako ta Paxful (“Sashen Taimako na Paxful”) na iya taimakawa. Ɗaya daga cikin ɓangarorin biyu na iya buɗe matakan sasanta jayayyar (“harƙallar da aka yi jayayya a kai” ko “jayayya”) game da wata harƙalla. Za a iya buɗe jayayya ne kawai ga harƙallolin da Mai Saye ya yi maki a matsayin "an biya." Idan harƙalla ba ta kasance Mai Saye ya yi makin dinka a matsayin "an biya" ba, Mai Saye bai soke ta ba, ba ta soke kanta ba sakamakon ƙarewar lokacin da aka ware domin gudanar da ita, ko an riga da an buɗe jayayya a kanta sannan an sasanta jayayyar, ko idan Mai Sayarwa ya riga da ya tura Dukiyoyin Kan Intanet ɗin zuwa ga Mai Saye, to ba za a iya buɗe jayayya kan irin wannan harƙalla ba, kuma ba za a iya soke abin da aka riga aka yi ba ko a sauya ba.
    2. matakan sasanta jayayya. A ƙasa an jero matakan da Sashen Taimako na Paxful ke ɗauka domin warware jayayya.

      1. Farawa

        Za ka iya buɗe jayayya ta hanyar shiga cikin Asusunka na Paxful, ka buɗe harƙallar da kake son buɗe jayayya a kanta sannan ka dannan madannin "jayayya." Madannin "jayayya" zai kasance yadda za a iya dannan shi ne kawai idan an riga Mai Saye ya riga da ya yi makin ɗin harƙallar a matsayin "an biya." Da zarar ka buɗe jayayya, sai ka zabi nau'in jayayyar daga cikin zaɓuɓɓukan da ke nan sannan ka yi bayanin dalilin da ya haddasa jayayyar.

        Zaɓuɓɓukan da ke da akwai domin bayyana nau'in jayayyarka idan kai Mai Sayarwa ne sun kasance kamar haka:

        • Mai Riƙe Kuɗi (misali, Mai Saye da ba ya ba da amsa) - May Saye ya yi makin ɗin harƙllar a matsayin "an biya" amma ba ya ba da amsa kuma ba ya kan intanet.
        • Matsalar biyan kuɗi - Mai Saye yana kan intanet kuma ya yi yunƙurin biya, amma akwai matsaloli game da biyan kuɗin.
        • Wani daban - buɗaɗɗen zaɓi da zai ba ka damar yin bayanin dadilin da ya haifar da jayayya. Mai Saye yana da damar duba bayananka.

        Zaɓuɓɓukan da ke da akwai domin bayyana nau'in jayayyarka idan kai Mai Saye ne sun kasance kamar haka:

        • Dillalin da ba ya ba da amsa - ka biya kuɗi, amma Mai Sayarwa ba ya ba da amsa kuma ba ya kan intanet.
        • Matsalar biyan kuɗi - ka tura kuɗi, amma Mai Sayarwa yana iƙirarin cewa akwai matsala dangane da biyan kuɗin sannan ya ƙi ya tura Ɗukiyoyin Kan Intanet ɗin.
        • Wani daban - buɗaɗɗen zaɓi da zai ba ka damar yin bayanin dailin da ya haifar da jayayya. Mai Sayarwa yana da damar duba bayananka.
      2. Sanarwa

        Da zarar an tura jayayya, Sashen Taimako na Paxful za su tura sanarwa ga abokin harƙallar ta imel ɗinsa da kuma ta hanyar tura saƙo ta cikin tsarin tattaunawar kasuwanci inda Mai Saye da Mai Sayarwar suna ciki a Muhallin Kasuwancin domin sanar da mutumin cewa an buɗe jayayya. Idan an buɗe jayayyar ne game da ɗaya daga cikin harƙallolinka, Sashen Taimako na Paxful za su sanar da kai wanne ne daga cikin harƙallolin ake jayayya a kansa sannan a bisa wane dalili ake wannan jayayya.

      3. Amsa

        Ka duba jayayyar sannan ka tura bayani game da abin da ya faru zuwa ga Sashen Taimako na Paxful. Ka haɗa da duk waɗansu shaidu da za su taimaka wajen tabbatar da bayananka, waɗanda suka haɗa da shaidar biyan kuɗi, shaidar mallaka ko shaidar cewa ka karɓa ko ba ka karɓi kuɗin da aka turo ba.

      4. Bitar Paxful

        Sashen Taimako na Paxful za su yi bincike game da harƙallolin da aka buɗe jayayya a kansu sannan za a yanke hukunci ta la'akari da shaidu da aka bayar daga ɓangarorin biyu. Sashen Taimako na Paxful na sasanta jayayya ta hanyar la'akari da abubuwa da dama kamar yadda aka yi bayani a ƙasa a Sashe na 8.

    3. Duba Jayayya. Yayin duba jayayya, Sashen Taimako na Paxful na iya ba ka ƙa'idojin da ake buƙatar ka bi. Ƙa'idojin da za a ba ka za su iya buƙatar da ka kawo ƙarin shaidu, kamar ƙarin shaida domin tantancewa, shaidar biyan kuɗi, wani nau'in shaida cikin hoto, odiyo, ko bidiyo, ko duk wani nau'in shaida da Paxful ta ga ya dace, sannan za a iya buƙatar ka kawo wannan shaida cikin wani ƙayyadadden lokaci. Idan ka karya waɗannan ƙa'idoji, hakan na iya kaiwa da abokin jayayyarka ya yi nasara kan al'amarin. Sashen Taimako na Paxful za su ba da sanarwar hukuncin da suka yanke ta cikin tsarin tattaunawar harƙalla a Muhallin Kasuwancin cikin kwanaki 30 daga ranar da aka fara jayayya, amma a bisa wasu yanaye-yanaye na musamman, al'amarin na iya ɗaukar tsawon lokacin da ya fi haka.
    4. Rashin ba da Amsa. Idan ka fara gudanar da harƙalla, abu ne mai muhimmanci ka kasance kana ba da amsa da wuri sannan kana kan intanet tun daga lokacin da aka fara gudanar da harƙallar har lokacin da za a kammala shi, soke shi, ko samar da maslaha ga shi. Wannan na nufin dole ne ka ba da amsa game da abubuwan da Sashen Taimako na Paxful za su buƙata dangane da harƙallar da aka buɗe jayayya a kanta cikin adadin lokacin da Sashen Taimako na Paxful ta zayyana, wanda idan ba haka ba za a iya yanke hukuncin cewa ba ka ba da amsa sannan a ba wa abokin jayayyarka nasara ga wannan jayayya.
    5. Janye Kuɗi. Mutum na iya fuskantar wasu ƙarin ƙalubale ko da kuwa Paxful ta ba shi nasara kan jayayyar da ake yi, wanda wannan ya danganta da nau'in hanyar biyan kuɗin da aka yi amfani da shi. Matakan sasanta jayayya da aka zayyana a cikin Yarjejeniyar bai shafi duk wani sakamako ba da Mai Saye ko Mai Sayarwa za su samu wanda ke da alaƙa da hanyar biyan kuɗin da aka yi amfani da ita yayin gudanar da harƙalla. Ba haƙƙi ne a kan Paxful ba da ta kula da al'amarin janye kuɗi sannan ba za ta ɗauki alhakin kuɗaɗen da aka dawo da su ba, ko aka janye, ko kuma buɗe jayayya ta hanyar da aka samar bisa hanyar biyan kuɗin da aka yi amfani da shi yayin gudanar harƙallar, ko da kuwa bayan an rufe jayayya ne.
    6. Sasanta Jayayya. Yawanci Sashen Taimako na Paxful kan kawo ƙarshen jayayya game da harƙalla ta hanyar tura Dukiyoyin Kan Intanet zuwa ga Mai Saye ko Mai Sayarwa na harƙallar da ake jayayya a kanta da zarar an kai ƙarshen matakan sasanta jayayyar.

      A ƙasa an kawo zaɓaɓɓun misalai da za su iya ba ka haske game da yadda Paxful za ta iya sasanta jayayya. Wannan ba yana nufin iya hanyoyin ba ke nan. Hanyar da za a bi domin sasanta jayayya ya danganta da yanayin jayayyar da nau'ukan shaidu da masu asusun suka gabatar.

      Sashen Taimako na Paxful za ta ba wa Mai Saye nasarar jayayya idan a ƙalla ya cimma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu zuwa:

      • Mai Saye ya biya kuɗi ta hanyar bin ƙa'idojin da Mai Sayarwa ya gindaya a tayin harƙallar sannan Mai Sayen ya gabatar da wadataccen shaidar da ke nuna cewa ya biya kuɗin ne ta hanyar bin waɗannan ƙa'idoji. Saɓa wa wannan Yarjejeniya ne idan Mai Sayarwa ya ƙi kammala harƙallar da zarar Mai Saye ya bi dukkannin dokoki da ƙa'idojin Mai Sayarwa kamar yadda Mai Sayen ya karɓi tayin sannan ya biya kuɗin harƙallar.
      • Mai Sayarwa ya daina ba da amsa sannan bai ba da amsar da ake buƙata ba a cikin wa'adin lokacin da Sashen Taimako na Paxful suka buƙaci ya yi hakan.
      • An tura kuɗin ne zuwa ga wani daban ba wanda ake gudanar da harƙallar da shi ba ko kuma an tura kuɗin ne ga wani asusun da ba a yi rajistar sa da sunan Mai Sayarwa ba.

      Sashen Taimako na Paxful za ta ba wa Mai Sayarwa nasarar jayayya idan ya cimma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu zuwa:

      • Mai Sayarwa bai biya kuɗi ba, bai biya kuɗi a kammale ba ko bai biya kuɗi ta hanyar bin ƙa'idojin da Mai Sayarwa ya gindaya ba a tayin wannan harƙalla.
      • Mai gudanar da biyan kuɗi ko kamfanin hanyar biyan kuɗin ya riƙe, dakatar, ko tsayar da kuɗin da Mai Saye ya turo. Wanna ya haɗa da lokutan da Mai Saye ya fuskanci zare kuɗi ko yake da jayayya tsakaninsa da bankinsa ko kamfanin da ya ba shi katin biyan kuɗi.
      • Mai Saye ya daina ba da amsa sannan bai ba da amsar da ake buƙata ba a cikin wa'adin lokacin da Sashen Taimako na Paxful suka buƙaci ya yi hakan.
      • An tura kuɗin ne daga wani daban ba wanda ake gudanar da harƙallar da shi ba ko kuma an tura kuɗin ne daga wani asusun da ba a yi rajistar sa da sunan Mai Saye ba.

      Idan Mai Saye ko Mai Sayarwa da ke jayayya a kan harƙalla ya gabatar da bayanai na damfara ko fayiloli na damfara ko ya yi iƙirari na ƙarya ko ya yi amfani da hanyoyin yaudara, cikin gaggawa za a kai ƙarshen jayayya ta hanyar ba shi rashin gaskiya sannan nan take za a iya dakatarwa ko rufe asusun mutumin wanda wannan ya danganta da hukuncin da Sashen Taimako na Paxful suka ga ya fi dacewa.

      A wasu lokutan da ta kasance babu ɗaya daga cikin ɓanarorin da ya cika ƙa'idojin da ake buƙata, ko kuma idan an samu yanayin da ba zai yiwu a iya gane wanda ya cika matakan da za su sa ya yi nasarar jayayyar ba, to Paxful na iya yanke hukuncin raba Dukiyoyin Kan Intanet ɗin tsakanin Mai Saye da Mai Sayarwar daida-wa-daidai ko kuma na wani ya fi na wani.

    7. Ɗaukaka Ƙara. Idan ka ga cewa Paxful ta yanke hukunci saɓanin yadda abin yake a cikin wannan Yarjejeniya, to kana da damar tura buƙatar ɗaukaka ƙara. Domin ɗaukaka ƙara, akwai buƙatar ka sanar da mu nan take a rubuce ta hanyar tuntuɓar sashen taimakon kwastomomi na Paxful cikin ƙasa da kwanaki 10 bayan samun sanarwar hukuncin Sashen Taimako na Paxful, sannan ka gabatar mana da wadatattun bayanai da hujjoji da ke tabbatar da iƙirarinka. Ɗaukaka ƙarar akwai buƙatar ta ƙunshi bayanai na dalilan da suka sa ka ce hukuncin da Paxful ta yanke bai yi daidai ba ta la'akari da dokokin wannan Yarejeniya sannan ka gabatar da hujjar da ke nuna cewa hukuncin ba daidai ba ne.

      Yana da kyau ka tuna cewa ko da lokacin da ake gudanar da jayayya ko kuma duk wani lokaci da kake amfani da Ayyukan da muke samarwa, wajibi ne ka yi amfani da kalaman da suka dace sannan ka girmama sauran masu asusu da kuma Sashen Taimako na Paxful. Ka duba, "Sashe na 13 - Abubuwan da Aka Hana Amfani da su".

    8. Kammaluwa. Ka aminta da cewa hukuncin Paxful game da jayayya ya kasance kammalalle, na ƙarshe sannan wanda zai yi aiki a kanka kamar yadda aka yi bayani a cikin wannan Yarjejeniya. Paxful ba za ta ɗauki alhakin komai ba daga abin da ya safi Mai Saye ko Mai Sayarwa dangane da hukunce-hukuncen da take yankewa.
  9. CAJIN KUƊAƊEN AMFANI DA AYYUKAN DA PAXFUL KE GABATARWA

    1. Ƙirƙirar Lalita abu ne da ake yi kyauta. Paxful na cazar kuɗaɗen Ayyuka. Za a nuna maka kuɗin da za a caja kafin ka yi amfani da duk wani abin da ke buƙatar a biya masa kuɗi. Duba “Kuɗaɗen Paxful” domin samun ƙarin bayani. Kuɗaɗen da muke caja na iya sauyawa sannan Paxful na da damar sauya farashinta da kuɗaɗen da take caja a kowane lokaci.
  10. BABU 'YANCIN SOKE KUƊAƊEN AYYUKA KO NA MASU HAƘAR KUƊAƊEN INTANET

    1. Idan ka yi amfani da wata Haja wanda ake cajar kuɗi, ko ka ƙirƙiri harƙalla wanda ta ƙunshi biyan kuɗin masu haƙa ta hanyar Kafar, to ba za a dawo maka da kuɗi ba da zarar ka tabbatar da gudanar da harƙallar.
  11. TSAYAWAR AYYKAN DA MUKE GUDANARWA

    1. Za mu iya gyarawa, ko dakatar da kowane ɓangare na Ayyukan da muke gudanarwa na wucin gadi ko na dindindin a lokacin da muka ga dama ba tare da buƙatar mu biya wata diyya ba, sannan ko da mun ba da sanarwar yin hakan kafin mu yi ko ba mu bayar ba.
  12. DAKATARWA KO KULLE AYYUKA DA ASUSU; TAKUNKUMI GA LALITARKA

    1. Za mu iya (wanda muna da cikakkiyar damar yin hakan a loakcin da muka so ko da mun ba da sanarwa kafin aiwatarwa ko ba mu bayar ba): (a) dakatar da, sanya takunkumi, ko katse damar da kake da ita na kaiwa ga Ayyukan da muke gudanarwa (ciki har da sanya takunkumi ga Lalitarka), da/ko kuma (b) rufewa ko soke asusunka idan: (i) dokar da abin ya shafa ta buƙaci hakan, ko dokar buƙatar aiwatar da wani abu, ko dokar kotu, ko dokar gwamnatic mai ci; (ii) idan muka tarar da ka ko wataƙila za ka saɓa wannan Yarjejeniya; (iii) asusun yana fuskantar jiran yanke hukunci na shari'a, bincike, ko zama na gwamnati da/ko kuma idan muka yi hasashen wani haɗarin da ta shafi rashin bin doka wanda ya shafi harƙallolin asusunka; (iv) abokan haɗin guiwarmu na gudanar da ayyuka ba za su iya ci gaba da jiɓintar al'amarin asusunka ba; (v) ka aiwatar da wani abu da muka kalla a matsayin zagaye ko ƙin bin matakan da muka samar ko (vi) idan muka yi tunanin yin hakan ya zama dole domin kare kanmu, masu asusu a kafarmu, ciki har da kai, ko kare ma'aikatanmu daga wani haɗari ko hasara. Idan muka yi amfani da 'yancin da muke da shi na taƙaitawa ko hana ka samun damar kaiwa ga Ayykan da muke gudanarwa, to ba za mu ɗauki alhakin duk wani sakamako da ya biyu bayan hana ka kaiwa ga Ayyukan da muke gudanarwa ya haifar ba, wanda ya haɗa da duk wani jinkiri, lalacewa ko rashin jin daɗi da za ka fuskanta a sakamakon haka.
    2. Idan muka dakatar ko muka rufe asusunka, ko muka dakatar da damar da kake da ita na kaiwa ga Ayyukan da muke gudanarwa bisa wani dalili, ko muka taƙaita damar da kake da ita na amfani da Lalitarka, za mu yi ƙoƙarin sanar da kai game da abin da muka yi sai ko idan dokar kotu ko wasu matakan shari'a sun hana mu tura maka wannan sanarwa. KA AMINTA DA CEWA HUKUNCIN DA ZA MU YANKE NA AIWATAR DA WAƊANSU ABUBUWA, CIKI HAR DA TAƘAITA DAMAR KAIWA GA, DAKATARWA, KO RUFE ASUSUNKA KO LALITARKA, NA IYA KASANCEWA SAKAMAKON DALILAI NA SIRRI DA SUKA SHAFI KARE KAI DAGA HAƊURRA DA KUMA MATAKAN TSARO. KA YARDA DA CEWA BAI ZAMA DOLE BA GA PAXFUL DA TA BAYYANA CIKAKKEN BAYANIN MATAKAN KARE KAI DA SAMAR DA TSARONTA ZUWA GARE KA. Idan ya kasance mun dakatar da asusunka ko damar kaiwa ga lalitarka, za mu janye wannan dakatarwa cikin lokaci idan dalilin dakatarwar ya kai, saidai bai zama tilas ba gare mu da mu sanar da kai game da yaushe (idan ma akwai lokacin) ne za a janye dakatarwar.
    3. Idan kana da Dukiyoyin Kan Intanet a cikin Lalitarka ta Paxful sannan aka daɗe ba a gudanar da harƙalla da asusunka ba har na tsawon lokacin da doka ta zayyana, to za mu iya ba da rahoton sauran Dukiyoyin Kan Intanet da ke cikin asusunka a matsayin kayayyakin da babu mai su daidai yadda dokokin kayayyakin da aka fita batunsu suka tanadar. Idan haka ta auku, za mu yi bakin ƙoƙarinmu wajen sanar da kai a rubuce. Idan ba ka ba da amsa ba ga wannan sanarwa cikin kwanakin aiki bakwai (7) bayan samun sanarwar, ko kuma idan duka ta buƙata, za mu iya ba da waɗannan Dukiyoyin Kan Intanet ga muhallin doka da ta dace a matsayin kayayyakin da babu mai su. Muna da damar cire kuɗin ajiya ko wasu kuɗaɗen da suka shafin caji na gudanarwa daga cikin waɗannan Dukiyoyin Kan Intanet kamar yadda dokar da abin ya shafa ta tanadar.
    4. We reserve the right to reverse internally received Digital Assets to your Paxful Wallet back to the originating account if the owner of the originating account successfully demonstrates that the Digital Assets were transferred to your Paxful Wallet in error, and if there has been no activity in your account for a period of 24 months. If this occurs, we will use reasonable efforts to provide written notice to you. If you fail to respond to any such notice within 14 days, we may be required to reverse Digital Assets to the owner of the originating account.
  13. HARAMTA AMFANI

    1. Yayin kaiwa ga ko amfani da Ayyukan da muke samarwa, to ka aminta da cewa za ka yi ta'ammuli da su kamar yadda yake a zayyane cikin dokoki da ƙa'idojin wannan Yarjejeniya (ciki har da Ƙa'idojin Sirrantawa) sannan ba za ka aikata duk wani aikin da ba ya kan ƙa'ida ba, sannan da cewa dukkannin haƙƙoƙin abin da kake aikatawa sun rataya a wuyanka yayin ta'ammuli da Ayyukan da muke samarwa. Ba tare da taƙaita abubuwan da aka bayyana a sama ba, ka aminta da cewa ba za ka:
      1. yi ta'ammuli da Ayyukan da muke samarwa ba ta kowace fuska da za ta iya samar da katsa landan ga, rushe, yin tasiri marar kyau ga sauran masu asusu ko hana so morar Ayyukanmu yadda ya kamata, ko abin da zai lalata, hana gudanuwar, ko haifar da matsala ga aiwatuwar Ayyukanmu ta kowane fanni ko yanayi;
      2. gudanar da duk wata harka da za ta iya saɓa, taimakawa wajen saɓa, duk wata doka, matsaya, tsari, ko ƙa'idar shirye-shiryen da suka shafi ƙasashen da muke gudanar da harƙallolinmu a cikinsu, ko wanda zai ƙunshi kowane nau'in aiki marar kyau; bugawa, rabawa, ko yaɗa duk wani nau'in bayani da ya saɓa wa doka.
      3. katsalanda ga damar da wani mai asusu yake da shi na hulɗayya da Ayyukan da muke samarwa; ƙasƙantarwa, ɓatanci, ƙwace, tursasawa, tsarewa, barazana ko kuma tauye 'yancin shari'a (waɗanda suka haɗa da, amma ba su taƙaita ba ga, 'yancin sirrantawa, da na hulɗa da na mallakar abubuwa) na waɗansu masu asusu; janyowa, barazana, ƙarfafawa, ko ba da ƙarfin guiwa game da gaba, bambancin launin fata, ko tashin hankali ga wasu, cira ko ɗaukar bayanan waɗansu masu asusu daga Kafarmu.
      4. gudanar da waɗansu ayyuka da za su kai ga ƙasƙantarwa ko samar da cutuwa ga Paxful ko masu amfani da kafarmu; ko samar da duk wani bayani na ƙarya, wanda bai daidai ba, na yaudara, ko na ha'inci zuwa ga Paxful ko wani mai asusu wanda kuma ya shafi Ayyukan da muke samarwa ko kamar yadda aka samar ko aka buƙata a cikin wannan Yarjejeniya;
      5. sanyo duk wani nau'in baros cikin Ayyukanmu, Trojan, worms, logic bombs, ko waɗansu nau'ukan abubuwa masu illatarwa; amfani da saƙago, spider, crawler, scraper ko waɗansu fasahohi masu sarrafa kansu da za a yi amfani da su domin kaiwa ga Ayyukan da muke gudanarwa waɗanda kuma ba mu ne muka samar da su ba, ko a ɗauki bayanai; ƙoƙarin zagaye ko kauce wa duk wasu matakan tacewa da muke amfani da su, ko ƙoƙarin kaiwa ga duk wani nau'in aiki ko ɓangaren Ayyukan da muke gudanarwa waɗanda ba a ba da izinin kaiwa gare su ba; ko sanya talla a kowane wuri a Muhallin Kasuwancin Paxful wanda zai kai ga saye da sayar da Dukiyoyin Kan Intanet a wajen Paxful;
      6. gudanar da duk wata harka da ta shafi amfani da wasu abubuwa da suka saɓa ko karya haƙƙin mallaka, alamar kasuwanci, 'yancin hulɗayya kko sirrintaka ko duk wani 'yancin da ya shafi mallakar kaya a ƙarƙashin doka, ko waɗansu abubuwa da ke da lasisi ba tare da samun izini daga masu su ba; amfani da wani mallaki na Paxful; suna, ko tamari, ciki har da amfani da tambarin kasuwanci ko na ayyukan Paxful, ba tare da samun rubutaccen izini daga gare mu ba ko cikin yanayin da zai iya cutar da Paxful ko hajar Paxful; kowane aiki da ya shafi sa hannun ƙarya ko haɗin guiwar ƙarya da Paxful; ko gina duk wata manhaja da ke iya hulɗa da Ayyukan da muke samarwa ba tare da samun rubutaccen izininmu ba; ko
      7. ƙarfafa wa wani guiwa ko sa shi ya aikata wani abu daga cikin abubuwan da aka hana a ƙarƙashin wannan Sashe na 13.
  14. HAƘƘOƘIN MALLAKAR FASAHA

    1. Mun ba ka lasisi taƙaitacce, marar keɓancewa, kuma wanda ba a iya taransifa ga wani, wanda kuma dole ya yi daidai da dokoki da ƙa'idojin wannan Yarjejeniya, domin ka samu damar kaiwa ga sannan ka yi amfani da Ayyukan da muke gudanarwa, Kafar, da ƙunshiya da ke da dangantaka da wannan, sauran abubuwa, bayanai (a jimlace, "Ƙunshiya") domin dalilan da Paxful ta aminta da su wanda ke iya sauyawa lokaci zuwa lokaci. An haramta duk wani nau'in amfani da Kafar ko Ƙunshiyar sannan duk waɗansu haƙƙoƙi, suna, da abin da ya shafi Ayyukan da muke gudanarwa, Kafar, da Ƙunshiyar sun kasance mallakin Paxful kaɗai. Ka aminta cewa ba za ka kwafa ba, ko aika, raba, sayar, ba da lasisi, juya fasaha, gyara, buga, ko sa hannu ga taransifa ko sayar da, ko ƙirƙirar ayyuka da aka ciro daga, ko bibiyar Ƙunsiyar ta ko wace fuska, a jimlace ko wani ɓangare nata ba tare da samun rubutaccen izinin Paxful ba. Ba za ka iya kwafa, kwaikwaya ko amfani da kowanne daga cikin shaidar kasuwancin Paxful, shaidar rajista, tambari ko wani daga cikin fasahohin da ta mallaka ba tare da rubutaccen izini daga Paxful ba.
    2. Duk da cewa muna da burin samar da bayanai da suka kasance ingantattu kuma cikin lokaci a kan Kafar Intanet ta Paxful, ba dole ne Kafarmu ta Intanet (wanda ya haɗa da Ƙunshiya, amma bai taƙaita ga nan ba) ya kasance daidai, cikakke, ko ba wanda ya tsufa ba a koyaushe, sannan zai iya ƙunsar matsaloli na na'ura ko na kura-kuren rubutu. A ƙoƙarinmu na samar muku bayanai da suka kasance cikakku kuma ingantattu, za a iya sauyawa ko sabunta bayanai daka lokaci zuwa lokaci ba tare da sanarwa ba wanda wannan ya haɗa da bayanai dangane da dokoki, kayayyaki da Ayyuka. Saboda haka, ka tantance kowane bayani kafin yin amfani da shi, sannan duk hukuncin da ka yanke dangane da bayanan da ke kan Kafar Intanet ta Paxful ya kasance ra'ayinka ne sannan babu alhaki da zai ɗoru a kanmu dangane da wannan shawara da ka yanke. Bayai dawasu mutane suka samar a sun kasance ne kawai saboda dalilai na samar da bayanai sannan Paxful ba ta ba da tabbacin kasancewarsu ingantattu. Liƙau da ke yi wa mutum jagora zuwa wasu shafuka na wasu mutane daban (waɗanda suka haɗa da kafafen intanet) za a iya cin karo da su amma ba mu ne ke sarrafa akalarsu ba. Ka yarda da cewa ba mu da alhaki game da duk wani abin da ya safi bayani, ƙunshiya, ko Ayyuka da ke cikin kowanne abin da wasu mutane na daban suka samar ko a kan kowaɗanne kayayyaki ko liƙu da ke kan Kafar Intanet ta Paxful.
  15. TSOKACI DA TURO BAYANAN MAI ASUSU

    1. A koyaushe Paxful na ƙoƙarin ƙara inganta Ayyukan da take gudanarwa da kuma Kafar. Idan kana da wani tunani ko wata shawara game da ingantawa ko ƙari a kan Ayyukan da Paxful ke gudanarwa ko game da Kafar, Paxful za ta so da ji su; sai dai kuma, dukkannin abubuwan da aka turo dole su bi dokoki da ƙa'idojin wannan Yarjejeniya.
    2. Babu wani abin da zai sa bayyana duk wani tunani ko tsokaci, ko duk wani bayani mai kama da wannan da aka turo wa Paxful ko wani daga cikin ressanta, asalin kamfanin ko kamfanonin da ke da haɗin guiwa da shi, ko wani daga cikin jami'anta, darakotoci, manajoji, wakilai, da waɗanda aka sanya ayyuka (kowanne a mazaunin "Sashen Paxful" sannan a jimlace "Sassan Paxful") ya kasance ƙarƙashin duk wani nau'in tilasci na sirrantawa, buƙata ko biyan diyya.
    3. Idan ka tura wata shawara ko tsokaci ko wani bayani mai kama da wannan wanda ya shafi haƙƙoƙin mallakar fasaha ("Aikin") na Paxful ko wani daga cikin Sashen Paxful, to ka ba wa Paxful, dangane da Aikin da aka turo, damar amfani da ƙunshiyar ba tare da iyakancewa ba, kuma na har abada, sannan ba tare da an biya kuɗi ko an samu lasisi ba domin yin amfani da ƙunshiyar ko tsokacin bisa kowane dalili ne. Bugu da ƙari, ka janye duk wani 'yanci da kake da shi a kan Aikin iya ƙololuwar abin da dokar Amurka ta ba da dama, sannan ka ba da garanti ga wannan Sashe na Paxful cewa Aikin mallakinka ne, sannan babu wani mutum na daban da yake da wani 'yanci a kan Aikin sannan dukkannin Sassan Paxful za su iya amfani da Aikin ba tare da biyan wani kuɗi ba idan suna son amfani da bayanin, kamar yadda aka samar da shi ko bayan wani daga cikin Sassan Paxful ya masa kwaskwarima, ba tare da neman izini ko lasisi daga wani mutum na daban ba.
    4. Sannan ka aminta da cewa Paxful na iya ba da lasisi ga kowanne daga cikin Sassan Paxful domin amfani duk wani Aiki ko bayani da ka turo.
    5. Muna da damar cire duk wani abin da ka ɗora a kan Kafar, a bisa raɗin kanmu ba tare da gargaɗi ko ba da dalilai ba.
  16. YADDA ZA A TUNTUƁE MU

    Muna ba da shawarar cewa ka ziyarci shafin Fitattun Tambayoyi ɗinmu kafin tuntuɓar mu. Idan ta kasance shafin Fitattun Tambayoyi bai ƙunshi bayanain da kake nema ba, to Paxful na samar da taimako 24/7. Za ka iya tuntuɓar mu ta cikin ɓangaren taimako wanda ake samu a cikin shafin Fitattun Tambayoyin.

  17. ƘADDARA

    1. Ba za mu ɗuki alhakin jinkiri, gazawar gudanar al'amura ko katsewar Aiki ba wanda ya auku kai tsaye ko a kaikaice sakamakon wani dalili ko yanayi da ya fi ƙarfin ikonmu, wanda ya haɗa da amma bai taƙaita ba ga, faɗuwar darajar kasuwa, duk wani jinkiri ko gazawa da Allah ya aiko, ayyukan hukumomin jami'an tsaro ko na fararen hula, ayyukan 'yan ta'adda, 'yan ta-da-zaune-tsaye, yaƙi, yajin aiki, ko wani nau'in taƙaddamar ma'aikata, gobara, katsear sadarwa ko intanet ko ayyukan masu samar da sabis, gazawar kayan aiki ko softwaya, wasu nau'ukan annoba ko duk wani abin da ya faru da ya wuce ƙarfin ikonmu to ba zai shafi inganci da aiki da sauran ɓangarorin dokokin ba.
  18. YANAYIN YARJEJENIYA

    1. Wannan Yarjejeniya ya kunshi dukkannin yarjejeniyar da ke tsakaninka da Paxful dangane da batun da ya shafi dokoki da ƙa'idojin da ke cikin wanann Yarjejeniya sannan wannan yarjejeniya ya soke ko ya maye gurbin duk waɗansu nau'ukan fahimta ko yarjejeniya da suka kasance tsakaninka da Paxful dangane da abin da ake magana a kansa. Ba za ka iya zartar da duk wani 'yancinka ba ko haƙƙoƙin da ke kanka ƙarƙashin wannan Yarjejeniya ba tare da rubutaccen izini daga gare mu ba.