Bayanin Sirri na Paxful, Inc.

Paxful, Inc. (wanda kumadu ake kira da "Paxful," "mu," ko "namu") sun ɗauki matakan kare sirrinka. A cikin Sanarwar Sirri ("Sanarwa") mun yi bayanin nau'ukan keɓantattun bayanai da za mu iya karɓa daga gare ka wanda ke da alaƙa da amfaninka da kafafen intanet da suka haɗa da, amma ba su taƙar ta a nan ba, https://paxful.com/, lalitar Paxful, kafarmu ta intanet ta kasuwancin bitcoin, manhajar waya, shafukan kafafen sada zumunta, ko wasu hajojin kan intanet (a jimlace, "Kafar"), ko yayin da ka yi amfani da wani daga cikin hajoji, ayyuka, ƙunshiya, fasali, fasahohi, ko abin da muke samarwa (a jimlace, "Ayyukan").

An tsara Sanarwar domin ta taimaka maka wajen samun bayanai game da al'amuran da suka shafi sirrantawa sannan ta taimaka maka wajen fahimtar zaɓuɓɓukan da kake da shi game da sirrinka yayin da kake amfani da Kafarmu da Ayyukanmu. Yana da kyau ka fahimci cewa, yadda muke gudanar da Ayyuka ya bambanta daga wuri zuwa wuri.

Ga dukkannin dalilai, kwafen wannan sanarwar sirri da ke cikin harshen Ingilishi shi ne na asali, sannan shi ke jagoranci. Idan aka samu saɓani tsakanin kwafen da ke cikin harshen Ingilishi da kowanne daga cikin fassarori da aka yi zuwa wani harshe, to za a yi amfani ne da kwafen da ke cikin harshen Ingilishin.

Keɓantattun bayanan da muke karɓa

Muna karɓar bayanai da suke da dangantaka da kai ("Keɓantattun Bayanai") wanda ke da alaƙa da amfaninka da Kafar, Ayyukanmu, ko kuma yayin hulɗayyarmu da kai. Nau'ukan Keɓantattun Bayanai da za mu iya karɓa daga gare ka sun haɗa da:

Bayanan Kai, waɗanda suka haɗa da:

 • Suna
 • Adireshin Imel
 • Lambar Waya
 • Ƙasa
 • Cikakken Adireshi
 • Ranar Haihuwa

Bayanin Asusun Paxful, ciki har da:

 • Sunan Mamallakin asusun
 • Bayanin Furofayil ɗin Mai Asusu a sashen "Taƙaitaccen Tarihi"
 • Hoton Furofayil
 • Ranar da Aka yi Rajista
 • Nau'in Kuɗin da ya zo a Saite
 • Yanayin Lokaci
 • Harshen da ya zo a Saite

Harƙallolin Asusu Paxful, ciki har da:

 • Saƙonnin Tattaunawar Kasuwanci (wanda na iya haɗawa da bayanin kuɗaɗe idan ka gabatar da shi ga mai sayarwa)
 • Fayilolin Tattauanwar Kasuwanci
 • Harƙallar Kasuwanci
 • Tarihin Harƙalla
 • Sunan Gayyatacce
 • ID ɗin Gayatacce
 • Liƙau ɗin Gayyata
 • Harƙallolin Gayyata
 • An Ƙirƙiri Tayi
 • Dokokin Tayi
 • Ƙa'idojin Kasuwanci
 • Sanarwar Asusu
 • Matsayin Asusu

Bayanan da ke da alaƙa da lalitar dukiyarka ta Kan Intanet, ciki har da:

 • Mabuɗan Sirri
 • Mabuɗen Gama-Gari
 • Balas ɗin Lalita
 • Harƙallolin da suka shigo
 • Harƙallolin da suka fita

Bayanan da aka karɓa da suka shafi Bin Dokokin "Sanin Abokin Harƙalla" (KYC), ciki har da:

 • Katin shaidar da gwamnati ta bayar
 • Shaidar Wurin Zama
 • Hotuna, idan ka zaɓi ka turo mana su
 • Bidiyo, idan ka zaɓi ka turo mana shi

Bayanan Na'ura da na Amfani da Kafa, ciki har da:

 • Adiresoshin IP
 • ID ɗin kukis da/ko kuma sauran shaidu
 • Bayanan da suka shafi ta'ammulinka da Kafar, kamar su nau'in na'ura, bayanai da lokaci
 • Harshen da aka fi so
 • Bayanai game da abubuwan da aka aiwatar yayin amfani da Kafar

Ta yadda muke amfani da bayananka

Dalilan kasuwanci da ke sa mu karɓa, amfani da, riƙe, tare da tura Kaɓantattun Bayananka sun haɗa da:

 • Domin gudanar da Ayyuka ta hanyar tafiyar da Kafar, ciki har da:
  • Yin rajista, ƙirƙira, da gudanar da asusunka;
  • Tantance shaidarka da/ko kuma damar da kake da ita ta kai wa ga asusu, ko ka taimaka wa masu sayarwa su tantance shaidarka;
  • Samarwa, sauƙaƙawa, gudanarwa, da/ko kuma aiwatar da harƙalloli;
  • Sadarwa tsakaninmu da kai game da asusunka ko wani daga cikin abubuwanmu da kake amfani da shi;
  • Gudanar da abubuwan da suka shafi sanin damar karɓar bashi, Sanin Abokin Harƙalla, ko wasu bincike da ke kama da wannan;
  • Duba buƙata da aka turo; ko
  • Kwatanta bayanai bisa dalilai na samun daidai da tantancewa.
 • Domin gujewa haɗurra da kare ka, sauran mutane, da kuma kare Kafar da Harƙallolina.
 • Domin gabatar maka da abubuwan da ka fi so.
 • Domin ƙara fahimtar kwastomomi da yadda suke hulɗayya da Kafar da Ayyukanta.
 • Domin yi maka talla.
 • Domin gabatar maka da Abubuwan da suka fi dacewa da kai, da tayi da suka fi dacewa da kai, da talla a kan Kafarmu da kafafen intanet na wasu daban.
 • Domin gabatar maka da zaɓuɓɓukan da suka fito daga wurare taƙamaimai, abubuwa na musamman, da tayi na musamman.
 • Domin bin ƙa'idoji da dokokinmu, waɗanda suka hada da amma ba su taƙaita a nan ba, gabatarwa da ba da amsa yayin da wasu hukumomin doka suka buƙaci hakan da/ ko kuma masu gudanarwa daga wata hukuma ta doka, shugabanci, gudanarwa, zartarwa ko dokar gwamnati, hukuma mai gudanarwa a sashen shari'a, buƙatar bincike ko wasu matakan shari'a masu kama da wannan.
 • Domin sasanta jayayya, karɓa kuɗaɗe, ko shawo kan matsaloli.
 • Domin gabatar da taimakon kwastoma gare ka ko kuma sadar da bayanai zuwa gare ka.
 • Domin gudanar da kasuwancinmu.

Sannan za mu iya sarrafa Keɓantattun Bayani bisa wasu dalilai na daban yayin da muka tambayi izini daga gare ka kamar yadda doka ta tanadar.

Daga wuraren da muke karɓar keɓantattun bayanai

Muna karɓar Keɓantattun Bayani daga wurare daban-daban, ciki har da

 • Kai tsaye daga gare ka: Muna karɓar Keɓantattun Bayanai kai tsaye daga gare ka yayin da ka yi amfani da Kafarmu ko Ayyukanmu, ko aka samu sadarwa tsakaninmu da kai, ko muka yi hulɗayya kai tsaye.
 • Daga masu gudanar da ayyuka da/ko kuma masu sarrafa bayanai da ke taimakon mu wajen gudanar da Kafar da Ayyukan: Za mu iya neman masu gudanar da ayyuka domin su taimaka mana wajen gudanar da al'amuran Kafar ko Ayyukanta gare ka. Za mu yi hakan yayin da muka ga dama kuma bisa raɗin kanmu. Waɗannan masu gudanar da ayyuka na iya karɓar bayanai daga gare ka sannan su ba mu bayanan.
 • Daga sauran masu amfani da Kafar Paxful ko daga haɗin Gayyata da ya shafi Kafar Paxful ko Ayyukankta: Wasu masusu asusu na daban za su iya samar mana da bayanai game da kai waɗanda suka shafi harƙalloli ko tattaunawa. Gayyatattu ma za su iya samar mana da bayanai game da kai waɗanda suka shafi hulɗayya da harƙalloli kamar na gayyata.
 • Daga wasu mutane na daban da za su taimaka mana wajen tantance shaida, kare faɗawa tarkon damfara, sannan su ba da tsaro ga harƙallili.
 • Daga wasu mutane na daban da za su iya taimaka mana wajen tantance dacewar da ka yi da karɓar bashi ko ƙarfin tattalin arzikinka.
 • Daga wasu mutane na daban da za su taimaka mana wajen ƙwanƙwance Keɓantattun Bayanai, inganta Kafar ko Ayyukan ko yadda kake amfani da ita, tallata hajoji da ayyuka, ko gabatar da talle da tayi gare ka.
 • Daga kafafen sada zumunta, idan kana hulɗayya da mu a kan kafafen sada zumunta.

Yadda muke tura bayanai

A wasu lokuta, za mu iya bayyana wasu Keɓantattun Bayanai ga wasu mutane na daban. Rukunnen mutanen da za mu iya ba wa Keɓantattun Bayanai sun haɗa da:

 • Masu gudanar da ayyuka da/ko kuma masu gudanarwa: Za mu iya tura Keɓantattun Bayanai ga wasu ma'aikata na daban waɗanda suke gudanar da ayyuka da suka shafe mu ko a madadinmu. A misali, waɗannan ma'aikata na daban na gudanar da ayyuka da suka shafe ka, tantance bayaninka, taimakawa wajen gudanuwar harƙalloli, tura maka tallace-tallace game da kayayyakinmu da Ayyukanmu, ko samar da tallafi ga kwastoma.
 • Sauran abokan harƙalloli, kamar masu sayarwa: Za mu iya tura bayanai zuwa ga masu gudanar da harƙalloli da kai, waɗanda suka haɗa da sauran masu asusu wanɗanda daga wurinsu ne kake sayen dukiyar intanet ɗin.
 • Kamfanonin hada-hadar kuɗi da sauran kamfanoni da ke taimaka maka wajen biyan kuɗaɗe yayin gudanar da harƙalloli
 • Gayyatattu waɗanda suke samun gayyata daga Kafarmu
 • Wasu mutane na daban bisa dalilai da suka shafi kasuwancinmu ko makar yadda doka ta ba da dama ko ta buƙata, waɗanda suka haɗa da:
  • Domin bin doka, ƙa'idoji ko hukunce-hukunce, ko domin bin matakan shari'a (kamar su dokar kotu ko sammaci);
  • Domin gabatarwa wa a matsayin shaida ko wanke kai daga zargi da ya shafi doka;
  • Yayin da wata hukumar gwamnati ta buƙata kamar hukumar tabbatar da doka ko hukumar shari'a;
  • Domin tabbatar da cewa an bi Dokokin Aikin Kafarmu ko ƙa'idojinmu na cikin gida;
  • Domin kariya daga wata matsala ko hasarar kuɗi, wanda ke da alaƙa da bincike game da aikin da ya saɓa wa shari'a wanda ake zargi ko wanda ya tabbata, ko kuma domin mu kare 'yancinmu ko na wasu, kare dukiyoyinmu, ko lafiyarmu;
  • Domin saye ko sayar da wani ɓangare ko dukkannin kasuwancin Paxful. Misali, ta hanyar tura bayanai zuwa wani kamfanin da muke son haɗa guiwa ko komawa ƙarƙashinsa; ko
  • Domin taimaka wa gudanarwar mu, bin ƙa'ida, da jagorancin hulɗayya.

Tura bayanai zuwa wasu ƙasashe

Yana da kyau ka san cewa za mu iya tura Keɓantattun Bayanan da muka karɓa daga gare ka zuwa ga wasu ƙasashe koma bayan ƙasar da daga nan ne aka karɓi bayanan. Waɗancan ƙasashen ba dole ne ya kasance suna da dokokin kare bayanai iri guda da na ƙasar da daga nan ne ka turo mana gayanan ba. Yayin tura Keɓantattun Byananka, muna tabbatar da cewa mun yi hakan bisa bin matakan da doka ta tanadar.

Kukis da talla a kan intanet

 • Kuki ƙaramin fayil ne mai ɗauke da rubutu wanda kafar intanet ke adanawa a kan kwamfuta ko wayarka yayin da ka ziyarci kafar.
 • Kafarmu na amfani da kukis da fasahohin bibiya domin gudanarwar al'amuranta, sannan domin gabatar maka da tallace-tallace da za su iya burge ka. Domin samun ƙarin bayani, daure ka duba Ƙa'idojin Kuki ɗinmu.
 • Paxful na iya haɗin guiwa da wani kamfanin tallace-tallace domin bayyana tallace-tallace a kan Kafar Paxful ko kafafen wasu mutane na daban. Waɗannan kafafe da kuma kamfanonin tallace-tallacen ba Paxful ba ce ke gudanar da al'amuransu. Kamfanonin talla na amfani da fasaha wajen samun bayanan yanayin harƙallolinka a kan intanet domin gabatar maka da tallace-tallace da suka yi daidai da ra'ayinka. Idan ba ka son a yi amfani da waɗannan bayanai domin a riƙa kawo maka tallace-tallace da suka dace da kai, to za ka iya fita daga cikin tsari ta hanyar ziyartar:

Yana da kyau ka san cewa, hakan ba zai hana a riƙa kawo maka talla ba; za ka ci gaba da samun tallace-tallace na gama-gari waɗanda ba su taƙaita kan abin da ra'ayinka ke so ba kawai. Za ka iya sarrafa kukis a matakin burawuzarka. Idan ka ƙi aminta da kukis, hakan ba zai hana ka amfani da Kafarmu ba, amma zai iya taƙaita maka damar amfani da wasu ɓangarorin Kafar tamu.

Riƙe bayani

Muna riƙe Keɓantattun Bayanai na tsawon lokacin da ya zama dole bisa dalilan da suka sa aka karɓi bayanan, ko na tsawon wannan lokaci kamar yadda doka ta buƙata. Wannan na iya haɗawa da riƙe Keɓantattun Bayanai na tsawon lokacin da ake gudanar da kasuwanci. Muna ƙoƙarin goge Keɓantattun Bayananka da zarar ba a buƙatar su domin kowane ɗaya daga cikin dalilan kasuwancin da aka zayyana a sama.

Tsare bayanai

Paxful ta samar da tsari domin kare Keɓantattun Bayananka, wanda ya haɗa da matakan da aka tsara domin kare Kebantattun Bayananka daga ɓacewa, amfani da su ta hanyoyi da ba su dace ba, ko wani da ba shi da izini ya samu kaiwa gare su. Duk da haka, Paxful ba za ta iya tabbatarwa ko ta ba da garantin tabbatuwar bayananka cikin tsaro da sirrintawa ba na dukkannin bayanan da ka tura mana ko wadanda intanet ko mahaɗin intanet marar waya ya samar mana. Tura bayanai ta kan intanet sau da dama yana ɗauke da wasu haɗarurruka, ko da Paxful ta yi ƙoƙarin kare bayanai bayan ta karɓe su.

Yara da ke ƙasa da shekaru 18

Ba a samar da Kafar Paxful domin yara 'yan ƙasa da shekaru 18 ba. Ba ma karɓar keɓantattun bayanan yara da ba su wuce shekaru 18 da saninmu ba tare da izinin iyayensu ba. Idan muka fahimci cewa mun karɓi bayanai, waɗanda suka haɗa da Keɓantattun Bayanai, daga wani mutum da ya kasance ƙasa da shekaru 18 kuma ba tare da izinin iyayensa ba, to za mu goge bayanan nan take.

Sauye-sauye a bayanin sirri

Paxful tana da damar sauya wannan Bayanin daga lokaci zuwa lokaci. Za mu sanar da kai game da sauye-sauye da aka yi wa wannan Sanarwa ta hanyar sanya sabon kwafi na Bayanin a nan, sannan da ta hanyar imel, ko ta hanyar sanya sanarwa a shafin farko na Kafar Paxful. Muna ba da shawarar ka riƙa duba Kafar a-kai-a-kai domin ganin ko akwai sauye-sauye.

Tuntuɓe mu

Idan kana da wata tambaya game da wannan Bayani, ko idan kana son tambayar wani abu daga gare mu game da Keɓantattun Bayanai ko sirrantawa, to ka tuntuɓe mu ta: [email protected]

Ƙari da ya Shafi EEA

Waɗannan bayanai sun shafi, sannan kai tsaye an gabatar da su ne domin, mutanen da ke zaune a cikin Yankin Tattalin Arzikin Turai (EEA).

Mai Gudanar da Bayanai

Mai gudanar da Keɓantattun Bayananka Paxful, Inc. ne

Tushen Shari'a da ya Shafi Gudanar da Keɓantattun Bayanai

 • Tushen shari'a shi ne Sashe na 6(1)(b) na Gamammiyar Dokar Kare Bayanai ("GDPR"), yayin da aka yi amfani da Keɓantattun Bayanai domin gudanar da harkokin ayyukanmu da suka zama dole ko yayin da ka tura wata buƙata game da wani aiki.
 • Tushen shari'a shi ne Sashe na 6(1)(c) na GDPR yayin da aka yi amfani da Keɓantattun Bayanai domin cika dokokin shari'a ƙarƙashin EU ko dokar wata Jaha da ta kasance Mamba.
 • Tushen shari'a shi ne Sashe na 6(1)(d) na GDPR yayin da aka yi amfani da Keɓantattun Bayanai domin kare muradun wasu mutane.
 • Tushen shari'a shi ne Sashe na 6(1)(f) na GDPR yayin da aka yi amfani da Keɓantattun Bayanai domin gudanar da tsaftatacciyar harkar kasuwanci. A sama an kawo jerin tsabtatattun muradun kasuwancinmu inda aka yi wa take da "Yadda Muke Amfani da Bayananka".

'Yancin Kare Bayanai na Turai

Dokar Turai ta samar maka da wasu 'yanci dangane da Keɓantattun Bayananka, daga ciki har da:

 • 'Yancin samun damar kaiwa ga bayananka tare da gyara Keɓantattun Bayananka.
 • 'Yancin buƙatar Paxful ta goge wasu daga cikin Keɓantattun Bayanai masu alaƙa da kai.
 • 'Yancin tura bayanai, wanda ya haɗa da 'yancin turo buƙatar a tura wani daga cikin Keɓaɓɓun Bayanan da ka ba mu zuwa ga wata cibiya ko kamfanin kula da bayanai.
 • 'Yancin yanje duk wani izini da ka ba wa Paxful na karɓar, amfani, ko tura bayananka a kowane lokaci. Yana da kyau ka san da cewa, janye izini ba zai shafi damar da muke da Paxful ke ita na sarrafa Keɓantattun Bayananka ba kafin ka janye wannan izini.
 • 'Yancin ƙin yarda Paxful ta sarrafa Keɓantattun Bayananka, wanda ya danganta da yanayi na musamman da ya shafe ka.
 • 'Yancin tura buƙatar cewa Paxful ta taƙaita sarrafa Keɓantattun Bayananka, idan dai har an cike waɗansu ƙa'idojin taƙaitawar.
 • 'Yancin tura ƙorafi zuwa ga hukumar sa ido ta Turai.

Kada ka manta cewa, doka mai gudana na iya samar da zamar da wasu daga cikin waɗannan 'yanci na daban, ba wa Paxful damar ƙin karɓar buƙatarka, ko ba wa Paxful damar ƙara tsawon lokacin da za ta ɗauka kafin waiwaitar buƙatarka. Sannan Paxful na iya tuntuɓar ka domin tantance shaidarka, kamar yadda doka ta ba da dama, kafin ɗaukar mataki game da buƙatarka. Domin neman 'yancinka, kana iya tuntuɓar mu ta ɓangaren da ke sama mai taken "Tuntuɓe Mu".

Taransifa ta Ƙasa-da-Ƙasa

Za mu iya taransifa na Keɓantattun Bayanai da ke da alaƙa da mazauna EEA zuwa ƙasashen da ba sa ƙarƙashin Hukumar Turai domin samar da cikakken kariya, wannan ya haɗa da Amurka. Yayin irin wannan taransifa, Paxful na ɗaukar matakan tabbatar da cewa Keɓantattun Bayananka suna cikin tsaro yadda ya kamata. Idan ka kasance a wani ɓangare da ke ƙarƙashin EEA, Paxful za ta yi taransifa ɗin Keɓantattun Bayananka ne kawai idan: ƙasar da za a tura Keɓantattun Bayananka ta samu yarjewar Hukumar Turai; mai karɓar Keɓantattun Bayanan naka ya kasance a Amurka sannan ya samu amincewar Privacy Shield Framework ɗin US-EU; Paxful ta ɗauki matakan duk da suka dace na tsaro domin wannan taransifa, misali tura bayanin Satandard Contractual Clauses ɗin EU zuwa ga mai karɓar, ko; idan akwai dokar da ta ba da keɓantacciyar dama ga waɗannan ƙa'idojin GDPR da suka haɗa taransifa. Domin samun kwafe na matakin da Paxful ta bi domin gudanar da taransifa ɗin keɓantattun bayanai zuwa wajen EEA, to a tuntuɓe mu daga ɓangaren da ke sama na "Tuntuɓe Mu".

Ƙari da ya shafi Kalifoniya

Waɗannan bayanai sun shafi, sannan kai tsaye an gabatar da su ne domin, mazaunan Kalifoniya.

'Yancin Sirrintakarka na Kalifoniya

Yayin da muka bayyana wasu keɓantattuan bayananka da za su iya sa a gane ka zuwa ga wasu mutane na daban waɗanda za su yi amfani da bayanan domin gudanar da tallace-tallace, to kana da 'yancin neman ƙarin bayani game da wanɗanda suka karɓi bayananka. Domin samun wannan dama, ka tuntuɓe mu kamar yadda aka bayyana a ɓangaren da ke sama mai taken "Tuntuɓe Mu."

Bayanin "Kada A Bibiya"

Kafarmu ba a gina ta bisa tsarin da za ta iya fahimtar buƙatar ko saƙon "Kada A Bibiya" ba.

Facts What does Paxful do with your personal information?
Why?

Financial companies choose how they share your personal information. Federal law gives consumers the right to limit some but not all sharing. Federal law also requires us to tell you how we collect, share, and protect your personal information. Please read this notice carefully to understand what we do.

What?

The types of personal information we collect and share depend on the product or service you have with us. This information can include:

 • Social Security number or account balances
 • Payment history or transaction history
 • Credit history or credit scores

When you are no longer our customer, we continue to share your information as described in this notice.

How?

All financial companies need to share customers' personal information to run their everyday business. In the section below, we list the reasons financial companies can share their customers' personal information; the reasons Paxful chooses to share; and whether you can limit this sharing.


Reasons we can share your personal information

Does Paxful share?

Can you limit this sharing?

For our everyday business purposes - such as to process your transactions, maintain your account(s), respond to court orders and legal investigations, or report to credit bureaus

Yes

No

For our marketing purposes - to offer our products and services to you

Yes

No

For joint marketing with other financial companies

Yes

No

For our affiliates' everyday business purposes - information about your transactions and experiences

Yes

No

For our affiliates' everyday business purposes - information about your creditworthiness

No

We don't share

For nonaffiliates to market to you

No

We don't share

Questions?

Go to www.paxful.com

Who we are

Who is providing this notice?

The privacy notice is provided by Paxful and is applicable to your personal Paxful account.

What we do

How does Paxful protect my personal information?

To protect your personal information from unauthorized access and use, we use security measures that comply with federal law. These measures include computer safeguards and secured files and buildings.

How does Paxful collect my personal information?

We collect your personal information, for example, when you

 • open an account or provide account information
 • give us contact information or make a transfer
 • use your Paxful account to send or receive funds

We also collect personal information from others, such as credit bureaus, affiliates, and other companies.

Why can’t I limit all sharing?

Federal law gives you the right to limit only

 • sharing for affiliates' everyday business purposes — information about your creditworthiness
 • affiliates from using your information to market to you
 • sharing for nonaffiliates to market to you

State laws and individual companies may give you additional rights to limit sharing. See below for more on your rights under state law.

Definitions

Affiliates

Companies related by common ownership or control. They can be financial and nonfinancial companies.

 • Our affiliates include companies under common control of Paxful Holdings, Inc.

Nonaffiliates

Companies not related by common ownership or control. They can be financial and nonfinancial companies.

 • Nonaffiliates with which we share personal information include service providers that perform services or functions on our behalf.

Joint marketing

A formal agreement between nonaffiliated financial companies that together market financial products or services to you.

 • Our joint marketing partners include financial companies.

Other important information

We may transfer personal information to other countries, for example, for customer service or to process transactions.

California: If your Paxful account has a California mailing address, we will not share personal information we collect about you except to the extent permitted under California law.

Vermont: If your Paxful account has a Vermont address, we will not share personal information we collect about you with nonaffiliates unless the law allows or you provide authorization.