Tunasarwa ga Dillali game da Dokokin Aiki

Wannan Dokokin Aikin Dillali ya kasance abin da za a iya dubawa a gurguje na dillai, sannan ba maye gurbin Dokokin Aikin Paxful ba.

Ka tuna cewa, idan ka yanke hukuncin gudanar da kasuwanci a kan Paxful, to ka aminta da waɗannan dokoki ke nan.

 1. A matsayinka na dillali, ka ɗauki alhakin duk wata damfara da za ta iya aukuwa yayin sayar da dukiyarka ta intanet.
 2. Paxful tana da damar ƙin dawowa da kuɗaɗen da suka salwanta sakamakon damfara ko kuɗaɗen da aka biya ta hanyar tsarin adanarmu.
 3. Biyan dukkannin nau'ukan haraji nauyi ne da ya rataya a wurin dillali.
 4. Domin ba da rahoto wata matsala game da kasuwanci, daure ka buɗe jayayya sannan ka jira mai gudanarwa ya shigo cikin zancen.
 5. Ba za a tuhumi Paxful ba yayin da ka tura kuɗin intanet kafin a biya ka kuɗinka.
 6. Ba a yarda a gudanar da abubuwa da aka bayyana a ƙasa ba a kan Paxful sannan gudanar da su na iya kai ga haramta amfani da asusu:
  1. Sake sayar da katunan kuɗi
  2. Tura bayanan da ba su shafi gudanar da kasuwanci a kan Paxful ba a yayin kasuwanci
  3. Gudanar da kasuwanci ba a kan Paxful ba
  4. Rashin ba da amsa - ana buƙatar dillalai su riƙa ba da amsa nan take
  5. Kalamai marasa daɗi
  6. Satar kamannin mai gudanarwa
  7. Ƙirƙirar asusu sama da ɗaya (ba tare da izini ba)
  8. Yarjejeniya
  9. Riƙe kuɗi da gangan
  10. Duk wani nau'in damfara