Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Sell to

Get paid with

Price per Ethereum

Yadda Ake Sayar da Ethereum a kan Paxful

Paxful na zamar da shi abu mai sauƙi ga sababbin hannu da ƙwararru domin su samu 'yancin sarrafa kuɗaɗensu. Sannan tun da muna da kasuwar mutum-zuwa-mutum, za ka iya sayar da Ethereum (ETH) kai tsaye zuwa ga miliyoyin masu amfani da wannan kafa a faɗin duniya ba tare da buƙatar bankuna ko kamfanoni ba!

Ga nan abubuwan da kake buƙar aikatawa:

Kafin ka samu damar fara sayar da Ethereum, dole ne da fari ka fara ƙirƙira da tantance asusunka na Paxful ko ka shiga cikin asusunka wanda da ma ka mallaka. Da zarar ka shiga, kawai ki bi waɗannan matakai:

  1. Saita dokokinka - Tantance yawan adadin ETH da kake son sayarwa sannan ka zaɓi hanyar biyan kuɗin da kake so. Sannan za ka iya sanya nau'in kuɗin da ka fi so da kuma wurin da kake idan ka ga dama.
  2. Nemo tayi - Da zarar ka sanya dokokinka, ka danna Nemo Tayi domin kallon jerin tayi waɗanda za ka iya zaɓa daga ciki.
  3. Duba tayi - Kada ka manta, ka duba dukkannin muhimman bayanai da suka shafi mai saye waɗanda suka haɗa da matsayin tantancewarsa, adadin kasuwanci da ya yi nasarar kammalawa, da kuma tsokacin da wasu masu asusu suka rubuta game da shi, kafin ka yanke hukuncin mu'amala da shi.
  4. Fara kasuwanci - Idan ka samu mai saye da ya dace ka yi hulɗa da shi, ka danna Sayar domin kallon dokoki da ƙa'idojin da mai sayen ya rubuta. Idan ka aminta da su, ka sanya adadin ETH da kake son sayar masa sannan ka danna Sayar Yanzu. Hakan zai kai ka zuwa ɓangaren tattaunawar kasuwanci sannan za a tura ETH naka zuwa ɓangaren adana inda zai zauna da wucin gadi.
  5. Kammala kasuwancin: Da zarar mai saye ya kammala abin da ya kamata ya yi, sannan ya turo maka kuɗin kuma sun shigo gare ka, to za ka iya tura ETH daga ɓangaren adana zuwa lalitarsu. Sannan za ka iya sauke rasidin kasuwancin idan kana son ajiye tarihin harƙallar.
  6. Rubuta tsokaci - Kada ka manta da rubuta tsokaci game da abokin kasuwancinka bayan nasarar kammala kasuwancin.

Duba Sashen Neman Sani domin samun ƙarin haske game da yadda za ka sayar da ETH nan take. Sannan za ka iya ƙirƙirar tayi idan kana son samar da dokoki ko ƙa'idojin kasuwanci naka na kanka. Kada ka yi ƙasa a guiwa wajen tuntuɓar sashen taimako idan kana da wata tambaya. Fatan alkairi!