Sayi Ethereum ta amfani da Skrill

Paxful ta zamar da hanyar saye da adana kuɗin intanet abu mai sauƙi. Nemi tayi da ya fi dacewa a ƙasa sannan ka sayi kuɗin intanet ta hanyar Skrill a yau.

Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Sayi Daga

Biya Da

Farashin Ethereum

Yadda Ake Sayen Ethereum a kan Paxful

Paxful na da burin sanya miliyoyin mutanen da ba sa hulɗa da bankuna cikin hada-hadar kuɗi a duniya. Mun samar da hanya mafi sauƙi da za ka iya yin amfani da kuɗinka da sauran kuɗaɗen kan intanet domin sayen Ethereum (ETH) sannan ka yi amfani da shi a wurin da kake da buƙatar yin hakan, daga saye na yau da kullum har zuwa sanya hannun jari.

Muhalinnin kasuwarmu da ke gudana bisa taimakon al'umma tana ba ka damar sayen Ethereum kai tsaye daga masu asusu da ke faɗin duniya, ba tare da buƙatar sa hannun banki ko wasu kamfanoni na daban ba. Ga nan yadda za ka sayi ETH nan take:

  1. Yi rajistar asusu – Yi rajista domin samun lalitar kan intanet ta kyauta inda za ka adana ETH naka cikin tsaro.
  2. Nemo tayi – Zaɓi hanyar biyan kuɗin da ka fi so, ka sanya adadin kuɗin da za ka kashe a kan kuɗin intanet, sannan ka danna Nemo Tayi. Ka karanta dokokin kowane tayi cikin natsuwa sannan ka duba furofayil na mai sayarwar. Ka lura da farashinsu, kasancewarsu a kusa ko saɓanin haka, da kuma tsokacin da aka rubuta a kansu game da kasuwancin da suka gabata.
  3. Fara kasuwanci – Idan ka aminta da abubuwan da mai sayarwa ke buƙata, ka sanya adadin kuɗin da kake son kashewa sannan ku fara kasuwancin. Hakan zai buɗe ɓangaren tattaunawa a inda mai sayarwa zai turo maka ƙa'idojin gudanar da kasuwancin. Ka bi ƙa'idojin nasa daki-daki sannan ka yi tambayoyi idan akwai abin da ba ka fahimta ba.
  4. Samu ETH – Bayan ka tura kuɗin sannan ka yi maki na kasuwancin a matsayin an biya, ka ba wa mai sayarwar ɗan lokaci domin ya tantance harƙallar. Daga nan zai turo ETH kai tsaye zuwa lalitarka ta Paxful.
  5. Ka rubuta tsokaci – Ka sanar da mu da kuma sauran masu asusu ra'ayinka a kan wannan abokin kasuwanci naka. Hakan na da matuƙar muhimmanci wajen ba da ƙarin tsaro ga kafarmu domin amfanuwar al'umma.

Da fatan ka ga yadda ake sayen Etherum cikin tsaro, sauri, da sauƙi a kan Paxful? Yanzu kasuwancin kuɗin intanet ba shi da wani wahala sakamakon samar da hanyoyin biyan kuɗi sama da 300+ waɗanda za ka iya zaba daga cikinsu. Ziyarci Sashen Neman Sani ko ka tuntuɓi sashen taimakonmu domin samun ƙarin bayani.

Sayen USDT ya kasance abu mai sauƙi kasancewar akwai sama da hanyoyi 300 na biyan kuɗi waɗanda suka haɗa da biyan kuɗi hannu, turawa ta banki, da katunan kuɗi. Ba ka ga hanyar biyan kuɗin da ka fi so ba? Sanar da mu, mu kuma za mu yi ƙoƙarin sanya ta a kan kafarmu. Domin ƙarin bayani, duba Sashien Neman Sani namu ko ka tuntuɓi sashen taimako.