Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Sayi Daga

Biya Da

Farashin Bitcoin

Yadda ake Sayen Bitcoin ta amfani da Cash App

Cash App lalita ce ta kan intanet sannan manhaja ce ta biyan kuɗi wanda ke ba ka damar turawa da karɓar kuɗi nan take zuwa ga 'yan uwa da abokai. Sannan tana ba ka damar karɓar biyan kuɗi daga wayoyi da katunan kuɗi domin kasuwancinka, tare da ba da damar tura kuɗi zuwa asusun bankinka.

A farfajiyar kasuwancin mutum-zuwa-mutum da ke kan Paxful, yanzu za ka iya sayen Bitcoin ta amfani da Cash App. Ka bi waɗannan matakai domin samun BTC ɗinka:

  1. Shiga cikin Paxful – Shiga cikin asusunka na Paxful ko ka ƙirƙiri wani sabo. Yin rajista da Paxful na ba ka damar mallakar lalitar Bitcoin a kyauta.
  2. Zaɓi hanyar biyan kuɗinka – Zaɓi Cash App a matsayin hanyar biyan kuɗi domin a nuna maka jerin dukkannin tayi da suka aminta da wannan hanyar biyan kuɗi. Sannan za ka iya sanya adadin kuɗin da kake son kashewa domin tace tayin da ba su dace da kai ba. Kana son samun ƙarin bayani game da Bitcoin ɗin da za ka samu? Jarraba kalkuletar Bitcoin.
  3. Samu tayi mai kyau – Ka duba cikin jerin tayin sannan ka tabbatar da cewa ka gudanar da bincike game da masu tayin. Ka yi la'akari da kasancewar masu tayin a kusa, darajar ƙimarsu, tarihin kasuwancin mai sayarwar, da sauran alƙaluma. Da zarar ka samu tayi mai kyau da ta dace da buƙatarka, to ka bibiyi dokokin dillalin cikin natuswa kafin fara gudanar da kasuwancin.
  4. Ka aminta da dokokin sannan ka fara gudanar da kasuwancin – Yayin sayen Bitcoin ta amfani da Cash App, a koyaushe ka tanadi $Cashtag ɗinka tare da shaidar biyan kuɗi domin tabbatar da an gudanar da kasuwanci ba tare da wata matsala ba. Har ila yau, waɗansu dillalai za su buƙaci ka tura kwafen katin shaidarka da waɗansu takardu na daban domin tantance shaidarka. Saboda haka, ka shirya cewa ana iya turo ire-iren waɗannan buƙatotci gare ka. Da zarar an fara gudanar da kasuwancin, ka bi ƙa'idojin dillalin. Yana da kyau ka san cewa Paxful ta samar da tsarin adana wanda ke ajiye Bitcoin din mai sayarwa har sai an kammala gudanar da harƙallar domin a kare ka daga fuskantar damfara. Da zarar an yi nasarar kammala kasuwancin, za a tura maka Bitcoin ɗin kai tsaye zuwa cikin lalitarka ta Paxful.

A nan Paxful, mun samar da hanya mafi sauƙi da aminci da za a iya sayen BTC ta amfani da Cash App. Domin samun ƙarin bayani game da sayen Bitcoin a kan kafarmu, kada ka yi ƙasa a guiwa wajen duba sashen neman saninmu ko ka tuntuɓi sashen taimakonmu.