Gayyatacce a Paxful

A Biya Ka domin Gayyato Mutane Zuwa Paxful

Shirinmu na Gayyatar Bitcoin na taimaka maka domin samar wa al'ummarka 'yancin hada-hadar kuɗi. Sannan a matsayin bonanza, kuɗi za su rinƙa shigo maka.

Gayyato mutane zuwa Paxful

Samun Kuɗi Nan Take ga Kowanne Kasuwanci

Za ka samu kuɗi duk lokacin da mutanen da ka gayyato Paxful da mutanen da su ma suka gayyato suka sayi Bitcoin.

Kuɗin Shiga Yayin Kowane Kasuwanci

Za ka samu kuɗi duk lokacin da mutanen da ka gayyato Paxful da mutanen da su ma suka gayyato suka sayi Bitcoin.

Samu 50% na Kuɗin Adana Samu 50% na Kuɗin Adana

Yayin da mutanen da ka gayyato suka sayi Bitcoin a kan Paxful.

Samu 10% na Kuɗin Adana Samu 10% na Kuɗin Adana

Yayin da mutanen da abokanka suka gayyato suka sayi Bitcoin a kan Paxful.

Me ya sa ya Kamata ka Zama Mai Gayyata?

Shirinmu na Gayyatar Bitcoin hanya ce babba da za ka iya yaɗa labarin kuɗin intanet ga al'ummarka.

Lalitar BTC
Samu Bitcoin Samu Bitcoin

Kana da kashi 50% na kuɗin adana a duk lokacin da ɗaya daga cikin waɗanda ka gayyata ya sayi Bitcoin.

Tsari mai bunƙasa
Bunƙasa Harƙallarka Bunƙasa Harƙallarka

Za ka samu kashi 10% na kuɗin adana a duk lokacin da wani da ke da alaƙa da kai ta neya ya sayi Bitcoin.

Cire kuɗi
Cire Kuɗi a Koyaushe Cire Kuɗi a Koyaushe

Da zarar ka samu a ƙalla Bitcoin ɗin da ya kai darajar Dalar Amurka 10, za ka iya tura kuɗaɗenka zuwa lalitarka ta Paxful a duk lokacin da kake so.

Zamo Mai Gayyata

Ta Yaya Abin Ke Wakana?

Haƙiƙa abu ne mai sauƙi-ka zamo Mai Gayyatar Bitcoin ta hanyar bin matakai uku marasa ɓata lokaci.

Zamo Mai Gayyata
Gayyato Kowa Gayyato Kowa

Tura lamba ko liƙau ɗin Gayyatarka kan kafafen sada zumunta, zaurukan kuɗin intanet, ko ga al'umma. Za ka iya samun keɓantaccen lambarka ko liƙau ɗinka a ƙarƙashin Allon Baynan Gayyatarka (kafar intanet) ko ɓangaren Gayyata (waya).

Zamo Mai Gayyata
Jawo su Zuwa Kasuwanci Jawo su Zuwa Kasuwanci

Wayar da kan waɗanda ka gayyata game da yadda za su gudanar da kasuwanci a kan Paxful. Duk lokacin da suka sayi Bitcoin, za ka samu kashi 50% na kuɗin adanarsu. Sannan za ka samu kashi 10% na kudin adanar a duk lokacin da waɗanda suka gayyata suka sayi Bitcoin a kan Paxful.

Zamo Mai Gayyata
A Biya Ka A Biya Ka

Ka bibiyi harƙallolin waɗanda ka gayyata daga Allon Bayanan Gayyatarka sannan ka duba yadda kuɗaɗen da kake samu suka ƙaruwa kai tsaye. Da zarar kuɗaɗen da ka samu sun kai a ƙalla darajar Dalar Amurka 10, to za ka iya turawa zuwa lalitarka ta Paxful.

Za a Maka Jagora ka Fara
Abin dariya ne ko? Abin dariya ne ko? Bari mu maka jagora don ka fara!

Ƙirƙiri asusunka na kyauta a kan Paxful domin fara gayyato mutane.

Gayyata Fitattun Tambayoyi

Watakila kana da wasu 'yan tambayoyi. A ƙasa mun kawo amsoshin wasu daga cikin fitattun tambayoyin.

Mene ne Paxful?
Paxful kasuwar mutum-zuwa-mutum ce da ke ba ka damar saye da sayar da kuɗin intanet ta amfani da kowanne daga cikin sama da hanyoyin biyan kuɗi 300. Ya kasance kamar eBay, amma idan ana maganar kuɗi - sannan ba shi da iyaka kwata-kwata. Muna da masu amfani da kafar sama da miliyan 4.8 a faɗin duniya. Dukkannin kasuwancinmu a kan Paxful suna ƙarƙashin tsaron ɓangaren adana, wanda hakan ke nufin za ka gudanar da harƙalla cikin kwanciyar hankali kasancewar kuɗaɗenka suna da kariya.
A ina zan ga abin da na samu daga gayyata?
Za ka iya kallon abin da ka samu a kan allon bayanan gayyatarka ko na dillali.
Shin zan iya ƙirƙirar tsararrun liƙau na gayyata domin in riƙa kallon ƙididdigar alƙaluman amfani da su?
E. A kan allon bayananka na gayyata, za ka iya ƙirƙirar keɓantattun liƙau da za a iya bibiya daga ɓangaren Bibiyi Shaida, domin tura wa mutanen da ka gayyata.
Mene ne ba a yarda da shi ba?
Domin tabbatar da cewa mun samu yarjejeniya game da abubuwan da aka yarda da su da waɗanda ba a yarda da su ba, a ƙasa mul lissafo wasu abubuwa da ake son ka guje su a matsayinka na Mai Gayyata.

  • Ƙirƙirar asusu sama da ɗaya - guda ɗaya kaɗai aka yarje maka a kan Paxful.
  • Amfani da turawa kai tsaye daga kan kafar intanet ɗinka zuwa kan kafar intanet ta Paxful.
  • Gudanar da harkokin damfara domin samun waɗanda za a gayyata.
  • Sayen talla domin tallatawa, kamar su: Paxful, paxful.com, ko wani suna mai kama da wannan - ko da kuwa jerin abajada ɗin ba daidai ba ne.
  • Yin amfani da sunayen wasu kamfanoni abokan takaran Paxful domin tattala hajar Paxful - ko kwatantan Paxful da sauran kamfanoni ta hanyar nuna gazawarsu.
  • Ɗora bayanan ƙarya domin jawo hankalin kwastomomi, ko yaudarar kwastomomi ta kowace hanya.
  • Cajan wani kuɗi bayan abin da kake samu na Gayyata a kan Paxful.
Kana son ƙarin bayani? Duba Dokokin Aikin Shirin Gayyata ɗinmu.
Mene ne Shirin Gayyata na Paxful, sannan ta yaya yake aiki?
Shirin Gayyata na Paxful wata dama ce mai kyau da za ka iya samun ladar gayyato mutane zuwa Paxful. Abu ne mai sauƙi - idan ka gayyato mutanet zuwa Paxful, za ka samu kasonka daga cikin kuɗin adana a duk lokacin da suka sayi kuɗin intanet a kan Paxful. Za ka samu kashi 50% na kuɗin* adana daga mutanen da ka gayyato kan Paxful, sannan kashi 10% na kuɗin* adana na mutanen da waɗanda ka gayyyata suka gayyato zuwa Paxful. Sannan wannan ba sau ɗaya ba ne kawai, duk lokacin da suka sayi kuɗin intanet a kan Paxful. Za ka iya tara ɗimbin waɗanda ka gayyata cikin sauƙi yayin da ka tura liƙau ɗin gayyatarka zuwa kafafen sada zumunta, ko ka tallata shi a kan kafarka ta intanet.
Yaya tsarin kamashon kowane mataki yake na shirin?
Za a biya ka duk lokacin da wanda ka gayyata, ko waɗanda suka gayyata ya yi nasarar kammala kasuwanci a kan Paxful. Ana lissafa adadin kuɗin da za ka samu ta la'akari da kuɗin adana, wanda ya kasance kashi 1% na jimillar kuɗin kasuanci, sai in har idan kuɗin da aka adana ya yi ƙasa da kashi 1%. Idan kuɗin da aka adana ya yi ƙasa da kashi 1%, za a lissafa kuɗin gayyatar ta la'akari da adadin kuɗin adana na wannan lokaci. Tsarin biyan kuɗin ya kasance kamar haka: Mataki na 1: Za ka samu kashi 50% na kuɗin adana yayin da mai asusun ya yi nasarar sayen kuɗin intanet. Mataki na 2: Za ka samu kashi 10% na kuɗin adanarmu yayin da mai asusun ya yi nasarar sayen kuɗin intanet.
Waɗanne ƙunshiya ne da nau'ukan talla suka fi dacewa wajen jawo mutane zuwa ga liƙau ɗin gayyatana?
Akwai wurare daban-daban da za su taimaka waɗanda suka haɗa da blog ɗinka, kafarka ta intanet, Google AdWords, Yandex Direct, Yahoo/Bing ads, mobile ad networks, YouTube da sauran fitattun kafafen nishaɗantarwa da na hada0hadar kuɗi. Kafafen sada zumunta ma wata hanyar ce da za ta taimaka maka domin samun Bitcoin ta hanyar gayyata. Yana da kyau ka yi amfani da bibiyar bayanai dangane da dukkannin talla da kake yi, wanda hakan zai ba ka damar gane wanne ne daga ciki ya fi karɓar ka sannan ka ɗauki darasi daga nan.
Adadin sau nawa ake sabunta ƙididdigar da ke kan Allon Bayanan Gayyatana?
Ana sabunta ƙididdiga a kan Allon Bayanan Gayyatarka ne nan take. Saboda haka, duk abin da ka kalla a kan allon bayanan su ke bayyana abin da ke da akwai a wannan lokaci.
Me ya sa wasu daga cikin waɗanna na gayyata suka gudanar da kasuwanci da yawa alhali wasu kuma sun yi rajista ba tare da gudanar da ko kasuwanci guda ba?
Mutane suna da buƙatoci mabambanta. Wasu sukan so su saye Bitcoin a karon farko a kan Paxful sannan su adana shi na tsawon watanni ko ma shekaru, alhali wasu kuma za su ci gaba da amfani da kafar domin saye da sayarwa. Sannan matsain harƙallolin waɗanda ka gayyata na iya danganta da irin bayanan da ka samar musu yayin gayyatar su, sannan da su kansu wadanne irin mutane ne.
Yaushe za a biya ni?
Yawanci ana sanya ribar da ka samu daga gayyatar da ka yi zuwa cikin lalitarka ta Gayyata da zarar wanda ka gayyata ya kammala kasuwanci. Da zarar ka tara ribar gayyata cikin Bitcoin da ya kai darajar Dalar Amurka 10, za ka iya tura su zuwa lalitarka ta Paxful a duk lokacin da ka ga dama. Da zarar ka samu Bitcoin da ya kai darajar Dalar Amurka 300, za mu buƙaci da ka kammala tantancewar shaida da ta adireshi. Shawara: Za ka iya sayar da Bitcoin ɗinka a kan kafarmu domin samun ƙarin riba!
A ina zan samu liƙau ɗina na gayyata?
Za ka samu liƙau na gayyatarka a kan allon bayananka na dillali da na gayyata.
A ina zan iya duba tsararren bibiyan shaidana?
A nan gaba kaɗan, za ka iya duba ɓangaren bibiyar shaida naka daga cikin allon bayananka. Ka ci gaba da bibiyan bayanai!
Waɗanne ƙasashe ya dace na mayar da hankali gare su yayin da nake gayyata?
Paxful ruwan dare ne gama duniya sannan za a iya amfani da shi a kusan kowane wuri a duniya ta amfani da intanet. Saboda haka, zaɓen mutanen da za ka mayar da hankali kansu ya rage gare ka - kusa da kai, yankinku, cikin ƙasarku, ko koma bayan haka. A yanzu haka, mafi yawan masu amfani da kafarmu sun fito ne daga Amurka, alhali Afirka, Asiya, da Latin Amurka sun kasance kasuwanninmu masu saurin bunƙasa.
Matakai nawa ne suke cikin Shirin Gayyata na Paxful. sannan ta yaya suke aiki?
Samun Bitcoin ta hanyar waɗanda ka gayyata bai taƙaita ga wadanda ka gayyata kai tsaye ba kawai. A mai makon haka, akwai matsayi a Shirin Gayyata na Paxful -- ɗaya kai tsaye ɗayan kuma a kaikaice: Mataki na 1: Waɗannan su ne waɗanda aka gayyata waɗanda suka yi rajista kai tsaye ta amfani da liƙau ɗinka. Mataki na 2: Waɗannan su ne waɗanda aka gayyata da suka yi rajista ta amfani da liƙau ɗin ɗaya daga cikin mutanen da ka gayyata kai tsaye.
Idan wanda na gayyata yana gudanar da kasuwanci da wani wanda aka gayyata, a nan ma zan samu cikakken kamasho?
Idan mutane biyu da ka gayyata suna gudanar da kasuwanci da junansu, za ka samu kashi 25% na jimillar abin da aka samu a maimakon kashi 50% ɗin da aka saba.
Wani wanda na gayyato zuwa Paxful ya yi rajista ba tare da amfani da liƙau ɗina ba. Shin a haka ma zan iya samun kamasho?
Sai dai kash! Ba zai yiwu ba. Za a samu kuɗin gayyata ne kawai yayin da masu asusu suka yi rajista ta amfani da keɓantaccen liƙau ɗinka.
Ina da zauren kafar sada zumunta da ke da alaƙa da bitcoin, sannan masu bibiyar kafar na da sha'awar saye da sayar da bitcoin. Shin ya kyautu in ba su shawarar amfani da Paxful a matsayin hanyar yin hakan?
Ƙarai da gaske! Paxful na ɗaya daga cikin hanyoyi mafi sauƙi a duniya da kowa kuma a ko'ina zai iya saye da sayar da Bitcoin. Waɗanda ka gayyata zuwa harƙallar kuɗin intanet za su iya yin rajista ta amfani da liƙau ɗin gayyatarka domin su fara saye da sayar da Bitcoin cikin mintuna! Duk lokacin da suka yi sayayya a kan Paxful, za ka samu kuɗin gayyata.