The Affiliate Program has been temporarily paused as we make changes to create a fair and sustainable program for the Paxful community. Learn more here.

Dokokin AIkin Shirin Gayyata

Ranar farawa: 21 Oktoba, 2019

Mun gode da ka yi rajista a matsayin mamba a cikin Shirin Gayyata na Paxful. Paxful za ta adana bayanan da ka turo a yayin yin rajista sannan za ta alkinta shi kamar yadda Dokar Kare Bayanai ta Tarayyar Turai ("GDPR") ta samar. Ka aminta da Dokar Sirrantawa na bin ƙa'idojin GDPR na Paxful yayin rajistar Gayyata.

Idan ka ci gaba da amfani da kafar intanet ta Paxful (ko da a matsayin Gayyatacce ne ko koma bayan haka), to hakan na nuna cewa ka aminta da Dokar Sirrantawa, wannnan doka kuwa za a iya sabunta ta lokaci zuwa lokaci, samar da ƙari a kanta, ko sauya wani abu a cikinta. Za a iya samun Dokar Sirrantawarmu ta yanzu a shafin farko na wannan kafa ta hanyar danna liƙau ɗin nan: https://paxful.com/privacy. Domin ɗebe shakku, yana da kyau ka san cewa za a iya tura wasu bayanai game da asusunka zuwa ga waɗanda ka gayyata a matsayin wani ɓangare na kasancewarka a cikin Shirin Gayyatar. Wannan ya haɗa da, amma bai taƙaita ba ga bayanan wuri da harƙallolin da aka gudanar a cikin asusu.

Waɗannan bayanai da ke ƙasa sun kasance Dokoki da Ƙa'idojin da suka shafi Shirin Gayyata. Paxful na da damar (a bisa raɗin kanta sannan ba tare da ba da sanarwa ba) da ta: (a) sauya wani daga ciki ko dukkannin waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji, a kowane lokaci sannan daga lokaci zuwa lokaci, wannan ya haɗa da (amma bai taƙaita ba ga) sauya adadin kamashon da za a biya wanda aka yi bayani a ƙasa, (b) dakatarwa ko soke Shirin Gayyata, da/ko kuma (c) dakatarwa ko kuma kulle asusun Gayyatarka da asusunka na Paxful na dindindin idan aka same da gudanar da wasu laifuka da aka zayyana a ƙasa.

A matsayinka na Gayyatacce, kana da damar gayyato wasu mutane na daban zuwa Muhallin Kasuwancin Bitcoin ɗin Paxful sannan ka samu kamasho wanda ya dogara da kasuwancin BTC da suka gudanar a kan kafar. Paxful na biyan dukkannin kamashon Gayyata cikin BTC.

Shirin Gayyatar ya kasance bisa tsarin matakai biyu wanda ya shafi masu asusu a karon farko kawai:

  • Gayyatacce a Mataki na 1
    Gayyatacce a Mataki na 1 shi ne mutumin da ya yi rajista a Muhallin Kasuwancin Bitcoin ɗin Paxful ta amfani da keɓantaccen liƙau ɗinka na Paxful wanda aka samar maka yayin da ka yi rajista da Shirin Gayyata ɗin.
  • Gayyatacce a Mataki na 2
    Gayyatacce a Mataki na 2 shi ne mutumin da ya yi rajista a Muhallin Kasuwancin Bitcoin ɗin Paxful ta amfani da keɓantaccen liƙau ɗin da Paxful ta ba wa wanda ka Gayyata a Mataki na 1.

Kamashon da za a biya.

Za ka samu kamasho duk lokacin da Gayyatacce a Mataki na 1 ko Mataki na 2 ya kammala kasuwancin da ta shafi harƙallar "Sayen" BTC a kan Paxful, sai ko idan Paxful ta sauya wannan ƙa'ida daga baya.

Kamar yadda ka sani, Paxful na saya Kuɗin Adana na kowanne kasuwanci da aka gudanar a kan kafar. Paxful na iya sauya Kuɗin Adanar a kowane lokaci sannan daga lokaci zuwa lokaci. Za ka iya samun bayani game da Kuɗin Adanar da adadinsa na yanzu a cikin wannan liƙau: https://paxful.com/support/en-us/articles/360013609793-Paxful-fees

  • Yayin da Gayyatacce a Mataki na 1 ya kammala harƙallar "Sayen" BTC akan Paxful, to Paxful za ta sanya kuɗi a Lalitarka ta Gayyata (cikin BTC) wanda ya kai darajar 50% na Kuɗin Adana na wannan lokaci.
  • Yayin da Gayyatacce a Mataki na 2 ya kammala harƙallar "Sayen" BTC akan Paxful, to Paxful za ta sanya kuɗi a Lalitarka ta Gayyata (cikin BTC) wanda ya kai darajar 10% na Kuɗin Adana na wannan lokaci.
  • Sai dai kuma, idan Gayyatacce a Mataki na 1 ya gudanar da harƙallar "Sayen" BTC a wurin wani Gayyatacce a Mataki na 1 na wani mamba ɗin Shirin Gayyata, to za a raba muku kamashon 50% daidai da daidai kai da ɗaya mamba ɗin.
  • Kamar haka kuma, idan Gayyatacce a Mataki na 2 ya gudanar da harƙallar "Sayen" BTC a wurin wani Gayyatacce a Mataki na 2 na wani mamba ɗin Shirin Gayyata, to za a raba muku kamashon 10% daidai da daidai kai da ɗaya mamba ɗin.
  • Duk lokacin da ka sayi daga wurin ko ka sayar wa Gayyatacce gare ka a Mataki na 1 ko Mataki na 2, to ba za ka samu wani kamasho ba.

Kamashon da ka samu daga kowace harƙalla za a tura shi ne zuwa cikin Lalitar Gayyatarka nan take da zarar an yi nasarar kammala wannan harƙalla. Duk lokacin da aka yi nasarar kammalar harƙallar, Paxful za ta tura saƙon imel da ke tabbatarwa. Ta wannan hanyar, za ka iya kallon yadda balas ɗin Lalitar Gayyatarka ke ƙaruwa daga cikin allon bayananka na Paxful.

A wassu lokuta, za ma ka iya samun kuɗin gayyata a duk lokacin da wanda ka Gayyata a Mataki na 1 da wanda ka Gayyata a Mataki na 2 suka kammala harƙallar "Sayar" da BTC a kan Paxful. Domin sanin cewa ko za ka iya samun kamasho yayin da wanda ka Gayyata a Mataki na 1 da wanda ka Gayyata a Mataki na 2 suka kammala harƙallar "Sayar" da BTC, to ka tuntuɓi Sashen Taimakon Paxful [email protected]. Paxful na da damar yin yadda ta so game da yanke hukunci a kan ko za ka iya samun kuɗin gayyata yayin da aka gudanar da harƙallar da ta shafi "Saye."

Cire Kamashonka.

Duk lokacin da sauran kuɗin Lalitar Haɗinka ya kai Dalar Amurka 10 (a kwatankwacin darajar BTC na wannan lokaci), to za ka iya tura dukkannin kuɗin zuwa ga taka Lalitar BTC ta Paxful. Da zarar abin da ya rage a Lalitar Haɗinka ya kai jimillar darajar $300, za a buƙaci ka tantance shaida da adireshi. Da zarar ka yi wannan, kana da damar aikata duk abin da kake so da ribarka. Yayin gabatar mana da wannan da kuma duk wasu bayanai na daban da za a iya buƙata, ka tabbatar da cewa dukkannin bayanan sun kasance gaskiya, daidai sannan ba sa ɗauke da yaudara. Ka yarda da cewa za ka sanar da mu cikin gaggawa yayin da wani daga cikin bayanan ya samu sauyi. Ka ba mu damar mu yi bincike, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar wasu mutane na daban, game da abubuwan da muka ga sun zama dole mu tantance game da shaidarka ko mu kare ka tare da kare kanmu daga faɗawa tarkon yaudara ko wasu laufuka da suka shafi kuɗi, sannan mu yake hukuncin da muek ganin ya dace ta la'akari da sakamakon waɗannan bincike. Yayin gudanar da waɗannan bincike, ka aminta da dacewa za a iya bayyana bayananka domin ba da misali da kuma kare faɗawa tarkon damfara ko a hukumomin hana laifukan da suka shafi kuɗi sannan waɗannan hukumomi na iya ba da cikakkiyar amsa ga tambayoyinmu.

Shawara: Muna ba da shawarar ka sayar da BTC ɗinka a kan kafarmu domin samun ƙarin riba.

Abubuwan da ba a Yarda da Aikata su ba

Abubuwan da ke biye sun kasance (amma ba dukansu ke nan ba) jerin nau'ukan ayyukan da za su iya sanyawa Paxful (wanda wannan ya danganta da yadda Paxful ta ga damar yanke hukunci) ta (a) soke ko janye biyan ka Kamasho da aka yi (ko da ka cire su ko ba ka cire ba), sannan/ko kuma (b) kora ko kuma kulle asusunka na Gayyata na Paxful dindindin.

  • Amfani da saƙonni ta hanyoyin da ba su dace ba domin gayyato mutane zuwa kafar Paxful.
  • Shiga duk wani nau'in harkar da ta saɓa wa doka, ko da yana da dangantaka ko ba shi da dangantaka da amfaninka da kafar Paxful da hajojinta.
  • Ƙirƙirar ƙarin asusu a kan kafar Paxful wanda ya ci gajiyar Shirin Gayyatar Paxful ta kowace irin hanya. Asusu guda kawai aka ba ka damar mallaka. Sannan ba a ba ka damar sayarwa, ba da aro, amfani tare da wani ko bayyana asusunka ko bayanan da za a iya amfani da su wajen shiga asusunka ga wani mutum da ba kai ba. Ƙirƙirar bayanan ƙarya na asusunka, yin ƙarya game da ƙasarka ko gabatar da fayilolin shaida na damfara, duk abubuwa ne da aka hana kai tsaye.
  • Duk wani takawa ko saɓa waɗannan Dokoki da Ƙa'idojin wanda ko dai ka yi ko kuma wakilanka suka yi.
  • Amfani da - a cikin kowane nau'i na talla ko wasu kafafen sadarwa ko bayanai kowane iri wanda ka ƙirƙira ko ka yaɗa ko kake gudanarwa - kalmomin da suka haɗa da "pax" ko "paxful" ko wata kalmar mai kama da wannan, furuci irin wannan, ko wasu kalmomi, alamomi da Paxful za ta ga cewa sun yi kama da alamar kasuwancin PAXFUL.
  • Ƙasƙantarwa, ɓatanci, ko cin mutuncin (a) Paxful ko wani daga cikin daraktocinta, jami'anta, ma'aikatanta, 'yan kwangilarta, ko wakilanta, or kuma (b) masu asusu a kafar Paxful, ciki har da sauran mambobin Shirin Gayyata.
  • Shiga duk wata harka da Paxful ke da yaƙinin cewa (wanda tana da damar yanke wannan hukunci yadda ta ga dama) zai iya tura ta ga fuslamtar bincike na hukuma, gudanarwa, ko na tuhuma, a ƙarƙashin hukumomi, dokoki, ko gudanarwar kowace ƙasa, haɗakar kasa-da-ƙasa (ciki har da Tarayyar Turai), ko wasu wani hukunci ko gwamnati wanda ya haɗa da caca ba bisa doka ba, damfara, fasa ƙaurin kuɗi, ko ayyukan ta'addanci.
  • Shiga duk wani nau'in harkar da ta saɓa wa doka, ko da yana da dangantaka ko ba shi da dangantaka da amfaninka da kafar Paxful da hajojinta.
  • Gabatar da bayanan ƙarya, ko waɗanda ba daidai ba, ko waɗanda ke cike da yaudara.
  • Gabatar da bayanan shaida da na adireshi domin tantacewa waɗanda suka kasance na ƙarya, waɗanda ba daidai ba, ko waɗanda ke cike da yaudara.
  • Ƙarfafa wa wani guiwa ko sa shi ya aikata wani abu daga cikin abubuwan da aka hana a ƙarƙashin wannan Sashe.

Haƙƙin Ƙirƙira

Sai dai har idan mun bayyana, dukkannin haƙƙoƙin mallaka a Kafar Intanet ɗin da kuma a dukkannin ƙunshiya da aka gabatar da ke da dangantaka da ayyukanmu, sun kasance kayayyakin Paxful ko waɗanda ke da lasisin kawo kaya ga Paxful sannan suna ƙarƙashin kariyar dokokin haƙƙin ƙirƙira. Ba mu ba da kowane nau'in lasisin amfani da ƙunshiyar Kafar Intanet ɗin ba. Ba za ka iya sayarwa ko sauya tsarin kayayyakin Kafar ba ko sake samarwa, ko nunawa, ko gabatarwa ga jama'a, ko rabawa, ko amfani da kayayyakin ta kowace hanya da ya shafi amfanin kai ko na neman kudi. An hana amfani da kayayyakin a kan kowace kafar intanet ko yayin tura fayiloli ko wasu nau'ukan harƙalloli masu kama da wannan ko da kuwa bisa kowane irin dalili ne.

Ba za ka iya kwafar wani abu ko wata ƙunshiya ba da ke kan Kafar ko duk wani abu da za a iya samu daga kan Kafar har sai da rubutaccen izini. Duk sauran damarmaki waɗanda ba a bayyana su ba a nan da amfani da abubuwa da ke kan Kafar, sun kasance ƙarƙashin mallakin Paxful kaɗai.

Iyakokin Ɗaukar Hasara/Zare Hannu

Kafar da Shirin Gayyata an samar da su ne a "kamar yadda yake a "sannan "kamar yadda akwai shi" bisa tsarin bayananka sannan ana amfani da shi ba tare da buƙatar wakilci ko sa hannu ba. Ba mu ba da wani nau'in garanti ba kowanne iri a fuskar doka wanda ke da alaƙa da kafar ko Shirin Gayyata, wannan ya haɗa da ba da garanti na samun ingancin kayayyaki, ayyuka, samun gamsuwa da ake buƙata, rashin matsala, daidaito, tsaro, da cikar muradi, ko kuma kowane nau'in garanti da ya shafi amfani da ko kuma gudanar da kasuwanci.

A iyaka ƙurewar damar da doka ta ba mu, alhaki ba zai hau kanmu ba game da:

  • 1. duk wata hasarar dukiya (wannan ta haɗa da hasarar rabeno, riba, kwantiragi, kasuwanci, ko kuɗin da ake tunanin a adana);
  • 2. kowane nau'in rashi na alheri ko faɗuwar ƙima;
  • 3. ko wane nau'in hasarori na musamman ko na kai tsaye ko da ta yaya suka auku.

Ɗaukar Hasara da Rashin Tuhuma

Ka aminta cewa ba za ka tuhumi Paxful, Inc. ba (ko wani daga cikin jami'anmu, daraktoci, mambobi, ma'aikata, wakilai da abokan hulɗa) dangane da kowace nau'in tuhuma, buƙata, aiki, abin da ya ɓaci, hasara, ko abin da ya janyo kashe kuɗi, wanda ya haɗa da kuɗaɗen da aka biya bisa shari'a da ƙa'ida, waɗanda suka samo asali daga ko suka danganci: amfanin ka da, ko abin da kake gunarwa da ke da alaƙa da, Shirinmu na Gayyata; ko idan ka karya waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji. Bugu da ƙari, ka aminta ka kasance ka ɗauki cikakken alhakin (sannan ba ka ɗora mana kowane nau'in alhaki ba) dukkannin tuhuma, hasara, abubuwan da suka lalace, rashi, abubuwan da suka kai ga kashe kuɗi, ciki har da kuɗaɗen da shari'a ta nemi a biya, wanda ya fito daga gare mu sakamakon ko wanda ke da dangantaka da kayar Dokoki da Ƙa'idojin da ka yi ko duk wani alhaki da muka ɗora maka sakamakon ta'ammulinka da hajojin da kuma Shirin Gayyata, ko yayin da wani mutum na daban ya yi hakan ta amfani da asusunka, na'urarka, ko asusun intanet ɗinka; ko yayin da ka karya wata doka ko 'yancin wani mutum na daban.

Gaba ɗaya

Waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji da kuma amfaninka da Kafar da Shirin Gayyata duk za su kasance ƙarƙashin sannan daidai da abin da Dokar Amurka ta tanadar. Duk wata jayayya da ta tashi da ke da alaƙa da waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji ko amfaninka da Kafar ko Shirin Gayyata za a fuskance su ne a kutunan Amurka kaɗai. Babu wani abu daga cikin waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji da zai taɓa 'yancinka ƙarƙashin dokar Amurka. Idan wata kotun Amurka ta bayyana wani ɓangare na daga waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji a matsayin marar inganci ko wanda ba za a iya sanyawa a kan mutane ba a ɗungurungum ɗinsa ko wani ɓangarensa, to wannan ba zai shafi inganci da tasirin sauran ɓangarorin dokoki da ƙa'idojin ba. Duk waɗansu kanu-kanu da ke cikin waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji suna nan ne kawai a bisa dalailai na ƙarin bayani amma ba su kasance an samar da su domin ɗora wata doka daga cikin waɗannan Dokoki da Ƙa'idoji ba.