Barka da Shigowa Harƙallar Kuɗi da Mutane ke Tallafe da Ita

Paxful na samar da sauyi a duniyar hada-hadar kuɗi. A cikin shekaru biyar kacal, mun zamo ɗaya daga cikin jagaba a muhallin kasuwancin bitcoin na mutum-zuwa-mutum wanda miliyoyin mutane suke amfani da shi a faɗin duniya. Sannan yanzu ne ma muka fara.

Waɗanda Suka Assasa

Paxful ta fara ne da sassauƙar manufa: domin ƙarfafa wa mutane biliyan huɗu da ba su da zarafin hulɗayya da bankuna, domin su samu damar sarrafa kuɗaɗensu ta hanyoyin da ba su taɓa jin labari ba.

Ray Youssef

Ray Youssef, Shugaba

Kasancewarsa baƙo daga Masar wanda ya girma a New York, a kullum burin Ray shi ne taimakon al'umma. Ya daɗe yana mafarkin a ce duniya ta kasance wurin da kowa na da zarafin gudanar da hada-hadar kuɗi. Wannan tunani nasa ya bunƙasa zuwa samar da Paxful.

Ɗabi'unmu

Muna wanzuwa ne tare da aiki a kan sauƙaƙa ɗabiy'u guda uku waɗanda ke mana jagora ga dukkannin fafutukarmu.

Muhimman ɗabi'un Paxful Muhimman ɗabi'un Paxful

Zamanto Jarumi

A Paxful, muna duƙufa ka'in da na'in domin aiwatar da abubuwa. Muna aiki ba dare ba rana domin kawo wa masu amfani da kafarmu abin da suka daɗe suna mafarki. Muna zamar da abin da ba zai yiwu ba ya zama mai yiwuwa domin kawo sauyi mai kyau a rayuwar miliyoyin mutane a duniya.

Gina domin Mutane

Yayin yanke wata shawara a Paxful, muna mayar da hankali ne a kan mutane - ba riba ba. Muna zuwa wuraren da duniya ta yi watsi da su sannan ta mance da su. Muna taimakon iyalai domin su ci gaba, muna gina makarantu, sannan muna ba wa masu amfani da kafar damar zamantowa iyayen gidan kansu.

Kasance Da Al'umma

Muna sauraren masu amfani da Paxful koyaushe 24/7. Ba mu kasance bishiyar giginya ba "na nesa ka sha daɗi" - muna nan tare da mutane. A koyaushe muna tattaunawa da masu amfani da kafarmu, muna tambayar su ra'ayoyinsu, sannan muna samar da abubuwan da suka fi na da.

Sayi kuma ka sayar da Bitcoin da Tether a kan Paxful

Kayanmu

Paxful na samar da sauyi a hada-hadar duniya inda ake ƙara karɓar kuɗin intanet - wanda hakan ke ba da damar tura kuɗi ga kowa, a ko'ina, sannan a kowane lokaci.

Ba ka da asusun banki? Wannan ba matsala ba ce. Muna da hanyoyin biyan kuɗi sama da 300 da za ka iya zaɓa daga ciki, wanda hakan ya samar da sauƙi a gare ka na sarrafa kuɗaɗenka yadda ka ga dama.

Fasahar da Mutane ke Tallafe da Ita

Duk al'amuran Paxful sun kasance na mutum-zuwa-mutum, wanda hakan ke nufin masu amfani da kafar na gudanar da kasuwanci ne da mutane na haƙiƙa - kamar dai yadda aka nufa game da amfani da bitcoin.

Lalitar Kuɗin Intanet ta Kyauta

Abin dogaro ne, mai sauƙin amfani, sannan na kyauta. Lalitarmu ta intanet na ba wa kowa da kowa wuri mai tsaro na adana dukiyarsu - za ka samu dama ko kai wane ne sannan daga duk inda ka fito.

Mai tsaro

Tsaro da rigakafin duk wata matsala su ne muhimman abubuwa yayin adana kuɗinka. Dukkannin kasuwanci a kan Paxful suna ƙarƙashin kariyar tsarin adana wanda hakan ke ba ka garanti na samun kwanciyar hankali.

#BuiltwithBitcoin

A nan Paxful, mun yi imani cewa Bitcoin shi ne makoma, sannan ta hanyarsa ne za a samu sauyi. Built with Bitcoin shirinmu ne da ke mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi, samar da ci gaba ga al'umma, tare da kawo sauyi mai amfani ga al'ummomin da ke buƙatar wannan taimako, duk ta amfani da Bitcoin.

Manufar wannan? Domin gina makarantu 100, samar da ruwan sha, da samar da ci gaba a fannin kasuwanci, duk ta hanyar samar da kuɗaɗen ayyukan daga Bitcoin. A yanzu haka muna kan gina makaranta ta huɗu, guda 96 ne kawai suka rage!

Bayan haka, shirin Built with Bitcoin ya taimaka a ɓangaren tallafi game da COVID-19 a Afirka - tare da tallafi daga masu amfani da kafarmu da kuma sauran abokan hulɗa, mun yi nasarar samar da abinci, man wanke hannu, da sauran kayayyakin kare kai daga cutar zuwa ga mutanen da ke da buƙata.

Shiga cikin tafiyarmu! Mu haɗa kai wajen kawo sauyi a duniya.

Ƙara Samun Bayani
Ray Youseff, Shugaban Paxful
Ray Youseff, Shugaban Paxful
Shiga cikin tafiyar Paxful

Tawagarmu

4

Ofisoshi a faɗin duniya

200+

Ma'aikata da ke da burin kawo sauyi mai kyau a duniya

21

Harsunan da ake magana da su a ofisoshinmu da ke faɗin duniya

1

Manufar kawo sauyi a duniya wanda zai ba wa kowa damar gudanar da hada-hadar kuɗi ba tare da fifiko ba

Shiga cikin tafiyar Paxful Ofishin Paxful na Talinn
Ofishin Paxful na Talinn Ofishin Paxful na New York
Ofishin Paxful na Manila Paxful na Hongkong

Tuntuɓa Domin Kasuwanci

Idan kana da matsalar da ke buƙatar taimako ko kana son turo mana tsokaci game da yadda za mu inganta hajojinmu, za mu so mu ji daga gare ka ta . Bugu da ƙari, idan kana so ne ka tuntuɓi Paxful dangane da al'amuran da suka shafi kasuwanci, to za ka iya kaiwa gare mu ta wasu hanyoyi na daban.

Yaɗawa da Tallatawa

Taimaka wajen yayata Paxful ta hanyar yaɗawa da tallatawa. Tuntuɓe mu a [email protected]‎ domin tambayoyi game da yaɗawa.

Ladar Gano Matsala

Shirin Ladar Gano Matsala na ba ka damar samun ladar gano matsaloli. Tura rahotonsu zuwa [email protected]. Ƙarin bayani here.‎

Asusun Haɗin Guiwa

Domin rajistar asusun haɗin guiwa saboda gudanar da kasuwanci a kan Paxful, za ka iya tura saƙon imel zuwa [email protected]. Duba ƙarin bayani a nan.‎

Cinikayya da Haɗin Guiwa

Domin neman ƙarin bayani game da haɗin guiwa da mu. Idan kana son haɗa guiwa da mu, to ka sanar da mu ta [email protected].‎

Shiga cikin tafiyar Paxful
Mu haɗa kai wajen gina kyakkyawar gobe
Shiga Cikin Tafiyarmu

Ƙirƙiri asusunka na Paxful domin ka yi rangadi a duniyar kuɗin intanet.