Sell to
Get paid with
Price per Tether
Yadda ake Sayar da Tether a kan Paxful
A Paxful, muna taimaka wa mutane domin su samu 'yancin sarrafa kuɗi sannan su kasance iyayen gidan kansu. Wannan dalilin ne ya sa, bayan Bitcoin, a yanzu za ka iya sayar da Tether (USDT) kai tsaye zuwa ga sama da masu asusu miliyan uku da ke faɗin duniya. Muhallin kasuwancinmu wanda ke gudana da taimakon mutane yana ba wa mutane damar samun riba cikin sauƙi. Hakan na faruwa ne da taimakon tsarinmu na adana, 'yancin da kake da shi na zaɓar farashinka, da hanyoyin biyan kuɗi sama da 300 wanda za ka iya zaɓa daga ciki.
Domin farawa, ka yi rajista da Paxful ko ka shiga cikin asusunka da kake da shi sannan ka bi waɗannan matakai:
- Saita hanyar biyan kuɗi da ka fi so tare da nau'in kuɗin da ka fi son a biya ka da shi.
- Danna Nemo Tayi domin kallon jerin tayin da suka yi daidai da bayanan da kake nema.
- Yayin da kake duba tayi, ka lura da duk bayanan da ke nan. Wannan ya haɗa da maki na ƙimar masu saye, kasancewarsu suna nan ko ba sa nan, da farashin da suka bayar. Idan ba ka samu wanda ya dace da kai ba, a koyaushe za ka iya ƙirƙirar tayi naka na kanka domin jawo hankalin masu asusu da ke da ra'ayin sayen Tether ƙarƙashin dokokinka.
- Da zarar ka samu tayi da kake so, ka dannan Sayar. Ba za a fara kasuwancin kai tsaye ba, a maimakon haka, za a buƙaci ka karanta dokoki da ƙa'idojin mai sayarwar.
- Idan ka aminta da dokokin, ka sanya adadin da kake son sayarwa sannan ka danna Sayar Yanzu. Wannan zai sa kasuwancin ya fara sannan USDT naka za su tafi zuwa ɓangaren adanarmu.
- Ka lura da ƙa'idojin mai saye sannan ka samar da duk bayanan da suka kamata a cikin tattaunawar. Da zarar an turo maka kuɗin, za ka iya tura USDT daga ɓangaren adana zuwa lalitar mai saye, sannan ka ajiye rasidin.
- Bayan kammala kasuwancin, a koyaushe ka yi ƙoƙarin rubuta tsokaci dangane da mai sayen. Wannan ba wai yana taimaka musu wajen ƙara musu ƙima ba ne kawai, yana taimaka wa sauran 'yan kasuwa wajen samun haske game da nau'in mutumin da suke harƙalla da shi.
Domin tabbatar da cewa ba ka samu wata tangarɗa ba yayin gudanar da kasuwanci ka karanta dokokin sayar da Bitcoin daTether namu. Sannan za ka iya duba jagorar ƙirƙirar dokokin kasuwanci bisa tsari domin samun damar ƙirƙirar tayi masu jawo hankalin masu saye daga gare ka.
A kan Paxful, muna da matakai da dama da muke ɗauka domin tabbatar da cewa ka gudanar da kasuwanci ba tare da matsala ba a kowane lokaci kuma a ko'ina. Duba daga cikin dubban tayi da ake da su domin ka fara sayar da Tether a yau!