Sell to
Get paid with
Price per Bitcoin
Yadda Ake Sayar da Bitcoin a kan Paxful
Yanzu abu ne mai sauƙi ka sayar da Bitcoin a matsayinka na dillalin Paxful. Kana da 'yancin saita farashinka tare da ƙawatawa da sama da hanyoyin biyan kuɗi 300 waɗanda za a iya amfani da su wajen biyanka kuɗin Bitcoin da ka sayar. A kasuwar mutum-zuwa-mutum, za ka iya sayar da Bitcoin ɗinka kai tsaye zuwa ga sama da mutane miliyan 3 a faɗin duniya. Kafarmu ta yi ƙoƙarin zamar da shi abu mai sauƙi ga sababbin hannu da gwanaye su samu riba tamkar guda.
Domin sayar da Bitcoin nan take, ƙirƙiri asusun Paxful ko ka shiga cikin wanda aka riga aka ƙirƙira. Da zarar ka shiga ciki, kawai ka bi waɗannan matakai:
- Saita abubuwan da kake buƙata – Ka zaɓi hanyar biyan kuɗin da ka fi so da kuma mafi girman adadin Bitcoin da kake son sayarwa. Sannan za ka iya bayyana wurin da kake da kuma nau'in kuɗin da ka fi so. Da zarar ka kammala wannan, ka danna Nemo Tayi. Za ka ga jerin tayi da suke da alaƙa da abin da kake nema waɗanda za ka iya zaɓa daga cikinsu.
- Duba tayi – Kafin zaɓar tayi, ka tabbatar da cewa ka duba dukkannin muhimman bayanai game da mai saye. Wannan ya haɗa da sunansa, ƙimarsa, matsayin tantancewar da aka masa, da farashinsa na kowane Bitcoin. Da zarar ka samu tayin da kake so, ka danna Sayar. Hakan ba zai buɗe kasuwancin kai tsaye ba, a maimakon haka, zai kai ka zuwa ga dokoki da ƙa'idojin tayi na mai saye.
- Fara kasuwancin – Idan ka gamsu da dokokin mai saye, ka sanya adadin da kake son sayarwa sannan ka danna Sayar Yanzu. Kai tsaye za a buɗe ɓangaren tattaunawar kasuwanci, sannan za a tura Bitcoin naka zuwa ɓangaren adana. Ka karanta ƙa'idojin da aka turo a natse sannan ka bi su. Da zarar mai saye ya kammala nasa ɓangare sannan ka samu kuɗin da aka turo, za ka iya tura Bitcoin ɗin. Za ka iya ɗauko rasidi bayan kasuwancin.
- Rubuta tsokaci – Bayan nasarar sayar da Bitcoin naka, kada ka manta da rubuta tsokaci game da abokin kasuwancinka. Hakan na da amfani ga kafarmu domin yana taimakawa wajen gina ƙimar mai asusu.
Domin samun ƙarin bayani, ka kalli koyarwa cikin bidiyo game da yadda za ka iya sayar da Bitcoin cikin sauri. Sannan za ka iya ƙirƙiran tayi domin sayar da Bitcoin ta hanyar bin jagoran ƙirƙirar tayi a kan Paxful wanda muka samar.
Kasuwar mutum-zuwa-mutum ta Paxful na da sauƙin amfani, tana da tsaro bisa tsarin adana, sannan ana iya kai wa gare ta daga ko'ina a duniya. Fara kasuwanci a yau!