Dokokin Aikin Samun Kuɗi na Paxful

Ranar farawa: July 1, 2021

DAURE KA KARANTA WANNAN YARJEJENIYA CIKIN NATSUWA. Idan ka yi amfani da Dokokin Aikin Samun Kuɗi na Paxful, ka nuna cewa ka aminta da waɗannan ƙarin "Dokokin Aikin Samun Kuɗi na Paxful" sannan ka aminta da cewa ka karanta cikin natsuwa kuma daki-daki, ka fahimta, sannan ka yarda da dukkannin dokoki da ƙa'idojin da suke ƙunshe a nan, waɗanda suka kasance ƙari a Dokokin Aiki na Paxful ("Yarjejeniyar"). Duk wasu dokoki da aka jaddada waɗanda aka yi amfani da su amma ba a zayyano su a ƙasa ba suna da ma'anonin da aka ba su a cikin Jarjejeniyar. Idan aka samu wani cin karo tsakanin Yarjejeniyar da Dokokin Aikin Samun Kuɗi na Paxful a yayin ko wanda ya shafi amfani da Dokokin aikin Samun Kuɗi na Paxful, to Dokokin Aikin Samun Kuɗin za a bi.

Game da Samun Kuɗi a Paxful

Aikin Samun kuɗi na Paxful wani tsarin gabatar da mutane ne wanda ke ba ka dama, a matsayinka na mai amfani da Paxful, don ka tura Kadarorinka na Dijital zuwa dandalin abokin hulɗa ("Abokin Hulɗar Samun Kuɗin"), a yayin da za ka samu riba saboda adana Kadarorin Dijital a lalitocinka.

Tsarin Gayyata

Shirin Riba na Paxful tsari ne da ke ba da damar gayyata wanda za a iya amfani da shi a kan kafar Paxful. Idan ka nuna cewa kana sha'awar shiga cikin shirin Riba na Paxful, to ka ba da dama a Paxful da ta tura bayanan asusunka da keɓantattun bayananka zuwa ga Abokan Harƙallar Shirin Riba, wanda za a yi hakan ne domin ba wa Abokin Harƙallar Shirin Riba ɗin damar bincikawa idan ka cancanta da ka shiga tsarin na Ribar Paxful. Waɗannan bayanai za su iya haɗawa da, amma ba su taƙaita ba ga, sunanka, lokacin haihuwa, da jaha da ƙasar da kake zaune. Abokin Harƙallar Shirin Riba na iya tambayan ƙarin bayanai. Dole ne ka bi matakan da ake da su na tura ƙarin bayanai. Abokin Harƙallar Shirin Riba na iya adanawa, dubawa, turawa, ko amfani da keɓantattun bayananka ta hanyoyin da ba haka muke yi ba. Idan ba ka so ka tura keɓantattun bayananka zuwa ga Abokin Harƙallar Shirin Riba, to kada ka shiga cikin shirin na Ribar Paxful.

Bayan tantancewa, za ka iya zaɓar nau'i(na'ukan) Kadarorin Intanet da ladaddakin da ke da dangantaka da shirin wanda Abokin Harƙallar Shirin Riba ke samarwa domin sanya kafin alƙalami. Idan ka zaɓi ka sanya kafin alƙalami na Kadarorin Intanet, to za a tsayar da Kadarorin Intanet ɗin a cikin lilitarka ta Paxful sannan a tura shi zuwa kafar Abokin Harƙallar Shirin Rabar. Kafin alƙalamin Kadarorin Intanet da aka sanya, da kuma ribar da aka samu, za ka iya samun sa ta cikin Lalitata / shsafin Riba a kan kafar Paxful.

The interest earned by Users is determined by, and subject to the rules of, the Earn Counterparty and may be changed or modified by the Earn Counterparty at its sole discretion. By entering into a transaction with the Earn Counterparty you agree to be bound by the Earn Counterparty’s Terms of Service. The Earn Counterparty Terms of Service are valid in all cases except when they contradict or violate the Agreement, these Paxful Earn Terms of Service, are illegal, are unreasonable or otherwise difficult to comply with (as determined in Paxful’s sole and absolute discretion), or if you and the Earn Counterparty consent to alter the Earn Counterparty Terms. IT IS YOUR RESPONSIBILITY TO CAREFULLY READ THE EARN COUNTERPARTY TERMS AND FOLLOW THEM EXACTLY. IF YOU DO NOT FOLLOW THE EARN COUNTERPARTY TERMS, YOUR TRANSACTION MAY BE DENIED. NEVER ENTER INTO A PAXFUL EARN SERVICE TRANSACTION UNLESS YOU HAVE FOLLOWED ALL TERMS AND CONDITIONS LISTED. IF YOU FAIL TO FOLLOW THE TERMS AND CONDITIONS, PAXFUL MAY NOT BE ABLE TO ASSIST YOU IN A DISPUTE PROCESS TO RECOVER YOUR FUNDS.

Kuɗaɗe

A koyaushe Paxful za ta riƙa bayyana bayanan da suka shafi kuɗi domin yin ƙeƙe-da-ƙeƙe game da duk wani caji da za a maka sakamakon amfaninka da kafar Paxful. Domin neman ƙarin bayani dangane da kuɗin musanye, to ka tuntuɓi Sashen Taimakonmu.

Asusun da Suka Tantance da Kuma Iyakantattun Muhallan Shari'a

An samar da tsarin Shirin Riba na Paxful ne kawai domin masu asusu da suka cancanci amfani da tsarin. Paxful na da damar hanawa ko gyara tsarin Shirin Riba na Paxful ɗin ga kowane mai amfani da Paxful, sannan Abokin Harƙallar Shirin Riba na iya ƙin gudanar da harƙalla da kowane mai asusun Paxful. A matsayin ƙari a kan Iyakantattun Muhallan Shari'a kamar yadda aka zayyana a Sashe na 2.7 na Dokokin Aiki ɗinmu, masu asusu da ke Jahar Texas da duk wata ƙasa ko jaha da dokokin aikin Abokin Harƙallar Shirin Riba ya haramta wa amfani da tsarin, to ba zai iya shiga shirin Riba na Paxful ba.

BABU GARANTI, TAƘAITAWAR ƊAUKAR NAUYI DA KARƁAR KASADA

SHIRIN RIBA NA PAXFUL ANA KAWO SU NE "KAMAR A CIKIN" SANNAN "KAMAR YADDA SUKE" BA TARE DA WANI GARANTI, KO WAKILCI BA, KO DA WANDA AKA BAYYANA NE KO WANDA AKA SANYA KO WANDA AKA BA DA DAMA. PAXFUL TA NISANTA KANTA DA DAGA BA DA KOWANNE IRIN NAU'IN GARANTI, KO TALLA, KO SHAWARA GAME DA WANI DALILI, IYA MIZANIN ƘOLOLUWAR ABIN DA DOKA TA TANADAR. PAXFUL BA TA BA DA WANI GARANTI NA CEWA ZA A CI GABA DA IYA HULƊA DA KAFAR INTNAET ƊIN, KOWANNE NAU'I NA HARƘALLOLI, KO KUMA KOWANNE ABUN DA KE CIKIN KAFAR BA TARE DA KATSEWA KO MATSALA BA. PAXFUL BA ZA TA ƊAUKI ALHAKIN DUK WATA MATSALA DA TA AUKU SAKAMAKON NA'URAR WASU MUTANE NA DABAN BA KO FASAHARSU, KO KUMA KOWANE NAU'IN KATSEWA KO HASARA DA MAI ASUSU ZAI YI. KA YARDA KUMA KA AMINCI DA CEWA BA KA SAKANKANCE KAN WATA MAGANA BA KO WATA FAHIMTA, WACCE TAKE RUBUCE KO WACCE TAKE CIKIN SAUTIN MAGANA, DA KE DA DANGANTAKA DA AMFANINKA DA WANNAN KAFA. BA TARE DA TAƘAITAWA BA, KA YARDA KUMA KA AMINCE DA HAƊARURRUKAN DA KE TATTARE DA AMFANI DA KUƊAƊEN INTANET WAƊANDA SUKA HAƊA DA (AMMA BA SU TAƘAITA GA WAƊANNAN BA), MATSALAR NA'URA WANDA AKE KALLO, MATSALAR NA'URA WANDA BA A KALLO, MATSALAR INTNAET, MATSALAR SOFWAYA, KATSALANDAN NA WANI DABAN WANDA KA IYA HAIFAR DA HASARA KO RASHIND AMAR KAIWA GA ASUSUNKA KO LALITARKA KO SAURAN BAYANAN MAI ASUSU, MATSALAR UWAR GARKE KO ƁACEWAR BAYANAI. KA YARDA KUMA KA AMINCE CEWA PAXFUL BA ZA TA ƊAUKI ALHAKIN KOWANE NAU'IN GAZAWA TA ƁANGAREN AIKA SAƘO BA, KO MATSALOLIN DA SUKA SHAFI KATSEWA, KO SAURAN MATSALOLI, KO JINKIRI YAYIN AMFANI DA KAFAR, KO DA KUWA MENE NE YA YADDASA SU.

BABU WANI ABIN DA ZAI SA PAXFUL, ABOKAN HAƊIN GUIWARTA DA SAURAN MASU GUDANAR DA AL'AMURA, KO WANI DAGA CIKIN MA'AIKATANSU, DARACTOCI, WAKILAI, MA'AIKATA, MASHAWARTA, MA'AIKATAN TUNTUƁA KO WAKILAI, SU ƊAUKI ALHAKIN (A) KOWANE ADADIN KUƊI DA YA HAURA JIMILLAR DARAJAR KUƊIN GUDANARWA DA KA BIYA NA WANI AIKIN DA SHI NE SADIYYAR JAWO BUƘATAR ƊAUKAR MATAKI A CIKIN WATANNI SHA BIYU (12) KAFIN A SAMU HASARAR KO (B) KOWANE NAU'IN HASARAR RIBA, FAƊUWAR DARAJA KO KASUWANCI, KOWANE IRIN NAU'IN HASARA, DAMEJI, ƁACI KO GURƁATAR BAYANAI KO KOWANE NAU'IN KAYA DA BA A GANI KO AKA SAMU BAƁIN ABU TA HANYA TA MUSAMMAN, TSAUTSATSI, A KAIKAICE, KO HANYAR DA BA A GANI, KO SAKAMAKON FARUWAR WANI ABU, KO DA HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON KWANTIRAGI, SAƁA ƘA'IDA, RASHIN LURA, ALHAKIN AIKATAWA KAI TSAYE, KO WANI ABU NA DABAN, WAND AYA FARU GAME DA KO YAYIN HULƊAYYA AMINTACCIYA KO WACCE BA AMINTACCIYA BA DA KAFAR KO AYYUKAN, KO WANNAN YARJEJENIYA, KO DA AN TUNTUƁI AMINTACCEN WAKILIN PAXFUL KO YA SAN DA AL'AMARIN KO KUMA YA SAN DA WANNAN MATSALA NA IYA AUKUWA, SANNAN DA GAZAWAR DUK WATA HANYAR SAMAR DA MAFITA KO WANI ƁANGARE MAI AMFANI DAGA GARE TA DA ZAI TAIMAKA WA WANNAN AL'AMARI, SAI DAI IDAN DOKA TA GANO CEWA WANNAN HASARA TA SAMU NE SAKAMAKON BAYYANANN SAKACIN PAXFUL, DAMFARA, AIKATA BA DAIDAI BA BISA NIYYA KO KARYA DOKA DAGA CIKIN GIDA. WASU DOKOKI BA SU BA DA DAMAR WAREWA KO TAƘAITA NAU'UKAN HASARA DA SUKA AUKU BISA TSAUTSAYI KO SAKAMAKON WANI AIKI BA, SABODA HAKA, TAƘAITAWAR DA KE NAN SAMA BA DOLE NE YA YI AMFANI A KANKA BA.

Ka aminta cewa Paxful na taka rawa ne a matsayin mai samar da haɗaka game da Shirin Riba na Paxful. Sannan ka aminta da cewa Paxful ba ta da iko a kan, sannan Paxful ba za ta zama ta ɗauki alhakin shirye-shiryen samun riba wanda Abokin Harƙallar Shirin Riba ya samar. Paxful ba za ta ɗauki alhakin kowace asara ba wadda ta auku a sakamakon rauni da ya shafi harƙalla, datsar asusu, ko dakatarwa, ko tsayar da harƙalla, ko rufe kasuwanci, fatarar kuɗi, dakatarwa na bagatatan na kasuwancin Abokin Harƙallar Shirin Riba ko waɗansu matsaloli da za a iya fuskanta. Ka aminta da cewa za ka ɗauki duk wata hasara da ke da nasaba da kafar Abokin Harƙallar Shirin Riba da kuma duk waɗansu hasarori da za su auku gare ka sakamakon matsalolin da aka lissafa a sama. Idan ka samu wata hasara sakamakon faruwa matsalolin da aka bayyana a sama, to ka aminta da cewa za a yi amfani da kuɗaɗen da aka tsayar daga cikin asusunka daidai da mizanin lalacewa ko hasarar da aka samu.

Ka aminta kuma ka yarda da cewa idan wani ɓangare na shirin Riba na Paxful wanda Paxful ko Abokin Harƙallar Shirin Riba ke samarwa ya kasance ba a kaiwa gare shi ko ya samu tsaiko sakamakon dalilai da ke ƙasa, to Paxful ba za ta ɗauki alhakin duk wata hasara da ka yi ko wanda abokin harƙalla ya yi ba (ciki har da, amma bai taƙaita ba ga na kai tsaye, na kaikaice, ko hasarar riba) sakamakon:

  1. Dakatar da Abokin Harƙallar Shirin Riba, daina harƙallarsa, rufewa ko tsayar da kasuwancin;
  2. Dakatar da ayyuka domin yin gyararraki kamar yadda Abokin Harƙallar Shirin Riba ko Paxful za ta sanar;
  3. Matsalar na'ura yayin tura bayanai;
  4. Ƙaddara ko wasu haɗurra da suka auku sakamakon yanayin da ba a hango ba, wanda ba a iya kawar wa, da kuma wanda ba ya magantuwa, kamar goguwa, girgizar ƙasa, tsunami, ambaliya, yunwa, ɗaukewar wutar lantarki, yaƙi, hargitsi, ayyukan gwamnati, hare-haren 'yan ta'adda, da sauransu, waɗanda suka kai ga dakatar da Paxful ko dandalin Kishiyar abin da aka Nemo;
  5. Matsalar sabis, katsewa ko jinkirin tasowa daga zambar na'ura, cutar kwamfuta, gyaran da ya shafi fasaha ko matsala, ɗaga darajar shafi, lamurran banki, ko rufewa ta wani lokaci da ta taso daga dokokin gwamnati;
  6. Matsalar sabis, katsewa, jinkiri, ba mai da jawabi mai tsari, ko mai da jawabi mai tsari wanda ya yi jinkiri da ya samu sakamakon tsarin kwamfuta na dandalin Kishiyar abin da aka Nemo ko lalacewar Paxful, raggonta ko wani abu mai kama da haka wanda ya kasa aiki yadda ya kamata;
  7. Matsalolin fasaha da ba daidai ba waɗanda ba za a iya fahimta ba ko magance su ta hanyar fasahohin da ake da su na industiri;
  8. Laifi ko jinkiri na duk wani mutum na uku; ko
  9. Sauye-sauye a dukkan doka, ƙa'idoji, ko odar gwamnati.

Kun yarda kun kuma amince cewa, aukuwar yanaye-yanayen da aka bayyana a sama za su iya kai wa hada-hadar da ba daidai ba, katsewar kasuwa, da kuma wasu yanaye-yanayen da ba daidai ba da ake iya samu, sannan Paxful ke da haƙƙin watsi da zartar da hada-hadarka.