Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Buy from

Biya da

Price per Bitcoin

Yadda za a sayi Bitcoin ta amfani da Venmo

Idan kana son sayen Bitcoin amma ba ka da wata hanyar tura kuɗi ko ba ka damu da sirrintawa ba, to Venmo shi ne hanyar biyan kuɗi mafi dacewa da kai. Yana da sauƙin amfani - abin da kake buƙata kawai shi ne ka sauƙe manhajar sannan ka haɗa bankinka da asusunka na Venmo.

Domin sayen BTC ta amfani da Venmo, da farko akwai buƙatar ka yi rajista domin samun lalitar Bitcoin ta kyauta ta hanyar danna Ƙirƙiri asusu. Sannan akwai buƙatar ka tantance shaidarka kafin samun damar sayen BTC.

Bayan ka shiga ciki, sai ka danna Sayi Bitcoin sannan ka zabi Venmo a matsayin hanyar biyan kuɗi domin tace tayin da ba su dace da kai ba. Muna ba ka shawarar cewa ka nazarci furofayil ɗin mai sayarwa domin fahimtar amincinsu. Za ka yi hakan ne ta hanyar danna kan sunansu domin kallon tarihin kasuwancinsu da tsokacin da abokan kasuwancinsu na baya suka turo musu.

Ka zaɓi tayin da ka fi so sannan ka danna Sayi domin kallon ƙa'idojin tayin sannan ka fara gudanar da kasuwancin. Ka shirya wa tura hoton da ka ɗauki kanka yayin da kake riƙe da katin shaida mai aiki ko hoton fuskar na'urarka da ke nuna asusunka na Venmo yayin da mai sayarwar ya buƙaci haka. A wannan mataki, Paxful na ba wa kuɗinka kariya ta hanyar tsarin adana a inda ake riƙe Bitcoin ɗin mai sayarwa na wucin gadi har sai lokacin da aka kammala ko aka soke kasuwancin.

Danna Yi Maki a Matsayin an Biya da zarar ka tura kuɗin daga asusunka na Venmo sannan ka jira mai sayarwar ya turo Bitcoin daga ɓangaren adana zuwa lalitarka ta Paxful. Daga nan shi ke nan! Kuɗin da ke asusun Venmo yanzu ya zama Bitcoin.

Idan kana da tsokaci game da muhallin kasuwancinmu ko kana son buɗe jayayya, kada ka yi ƙasa a guiwa wajen tuntuɓar sashenmu na taimakon kwastotmomi. A koyaushe muna nan a kan intanet, a kowace rana a cikin sati domin taimaka maka game da damuwowinka.