Ma'aikatan Paxful su ne ƙashin bayan kamfaninmu. A kullum muna koyon sababbin abubuwa daga junanmu kasancewar mun fito daga al'ummu daban-daban da ke da al'adu mabambanta. Kun ma san me ya fi ƙayatarwa? Kowa na iya koyo daga harsuna da al'adu mabambanta. Duk da cewa muna da zaƙaƙurin tawagar ma'aikata, kafarmu ta samu ne sakamakon aikin haɗin guiwa da samar da rahotanni da shawarwari daga kowanne tawaga da sashe-sashe da muke da su.
Barkwanci da abokan aikina.
Kyakkyawar gobe. Kamfanin na da alamun kyakkyawar gobe, sannan na san da cewa zan iya ba da babbar gudummawa domin cimma wannan nasara.
Mutane na tambaya cewa me ya sa harƙallar kuɗi ta mutum-zuwa-mutum ke da amfani. Bankin Duniya ya tabbatar da cea kusan mutane biliyan 2 ba su da tagomashin amfani da bankunan gargajiya. Paxful na ba wa ire-iren waɗannan mutane damar shiga harkar hada-hadar kuɗi.
Abin da ke ƙarfafa guiwa tare da jawo son Bitcoin ga rayuwar al'umma.
Ni da alhakin tabbatar da cewa muna ankare da ɓata gari. Na samar wa tawagata kayan aiki da matakan da za su taimaka wajen tabbatar da hakan. Ko kaɗan ba ma lamuntar damfara ko zamba a kan kafarmu.
Ina ƙaunar damarmakin da suka shafi motsa jiki da kiwon lafiya! Haƙiƙa kamfanin ya damu da lafiyar ma'aikatansa. Yana da tsare-tsaren da ke samar wa ma'aikata da hutu ko da tsakiyar aiki ne.
Ina son al'umma su samu ƙarin ilimi game da masana'antar baki ɗayanta. Masana'antar harƙallar kuɗi ta mutum-zuwa-mutum tana da abubuwa da dama da za ta iya taimakon al'umma da su musamman ga mutanen da ba su samu damar harƙalla da bankuna ba.
Wane taron kamfanin Paxful ne ka taɓa zuwa wanda ya fi burge ka a rayuwa?
Abin da yake ƙarfafa mini guiwa shi ne damarmaki marasa adadi da ake da su a nan. Tun lokacin da nake sabon shiga, sun yi imani da ni da kuma hazaƙata. Sun ba ni damar nuna abin da zan iya aiwatarwa na ci gaba.
Duk lokacin da muka fita domin samun abin sha, yakan kasance lokaci na nishaɗi matuƙa sannan lokaci ne na haɗuwa da abokan aiki a wajen wurin aiki!
Aikina ya ba ni damar sarrafa abin da nake sha'awa zuwa aiki, wanda kuma yake tasiri sosai ga waɗanda suke kallon bidiyoyin da nake samarwa.
Ganin yadda duk tawagar tana bunƙasa, fafutukar yin aiki da kuma cikin farin ciki. Kasancewa ɗaya daga cikin masu yin aikin don ci gaban yana ƙarfafa mun gwiwa a kan Paxful. Sa'an nan kuma duk lokacin da darajar Bitcoin tana ƙaru!
Ina son kowa ya samu cikakken ilimi dangane da hada-hadar Bitcoin na gaba ɗaya sannan da matakan gudanar da kasuwancinsa a Paxful saboda mutane su gane idan ana yunƙurin damfarar su ne.
Zamantowa mafi girman kamfanin fasahar hada-hadar kuɗi da mafi girman kafar kasuwanci na mutum-zuwa-mutum!
Shan 'ya'yan itatuwa da cin kayan maƙulashe dangin gyaɗa a cikin kicin, musamman kashu.
Mutanen da nake aiki da su da kuma manufofin kamfanin waɗanda ke taimaka wa mutane wajen kai wa ga gudanar da hada-hadar kuɗin wanda da babu kamfanin ba za su samuw annan dama ba.
Kasancewar akwai hanyoyi ingantattu da mutum zai iya bi domin samun kuɗi a kan Paxful, sannan da kasancewar ba kowa ba ne ɗan damfara.
Shan shayi tare da abokan aikina. Lokaci ne da ya dace na jin ra'ayoyin mutane ba a hukumance ba dangane da abubuwan da ke faruwa a duka sashe-sashen kamfanin. Tattaunawar da ta kasance ba a hukumance ba na taimakawa wajen rage adadin awanni da za a ɓata lokacin tattaunawa a hukumance.
Motsa jiki, abincin rana, ranakun hutu. Babban abin da ake mantawa a koyaushe shi ne, Paxful ta kasance mafi daɗin sha'ani a duk kamfanonin da na yi aiki da su a tsawon rayuwata. Suna iya bakin ƙoƙarinsu domin samar wa ma'aikata da walwala tare da nuna musu cewa suna da muhimmanci.
Taron da ya fi ƙayatarwa shi ne na Ranakun Bazara a lokacin da kamfanin ɗungurungum, har da kowa da kowa daga sauran ofisoshi, ke taruwa domin gudanar da rangadin ƙarfafa tawaga zuwa Split da ke Croatia. Abun ƙayatarwa ne matuƙa yadda ake haɗuwa da abokan aiki, a san juna, sannan a inganta dangantakar da ke tsakanin mambobin tawagar.
Sakamakon da ake samu da kuma mambobin tawagata.
Kasancewar muna iya bakin ƙoƙarinmu wajen kare masu sayarwa da masu saye! Babban abin da ba ma fata shi ne al'amarin da zai sa mu riƙe BTC ɗinka.
Zuwa ofishoshi daban-daban domin ziyara da kuma samun horaswa.
Tawagata!
Akwai damarmaki na ci gaba da bunƙasa fasahar da mutane ke da shi da ta shafi ƙwarewa ko gudanarwa.
Dukkannin tarurrukan Paxful suna cike da nishaɗi! Amma na fi son taron Ranakun Bazara na 2019 inda muka kwashe sati guda a Croastia.