Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Buy from

Biya da

Price per Tether

Yadda ake Sayi Tether a kan Paxful

Paxful na da zummar samar da damar gudanar da harƙallar kuɗi tsakanin miliyoyin mutanen da ba su da zarafin mu'amala da banki a fadain duniya. Za mu ba ka 'yancin sayen Tether (USDT) da kudinka sannan ka yi amfani da shi ta hanyar da ka ga dama; ko dai ka biya kuɗin kayayyaki da ka saya ko ayyuka da aka maka, ko don kare dukiyarka daga hasara, ko domin sayen kuɗaɗen intanet, ko don ka yi tanadin gobe ta la'akari da darajar kuɗaɗen intanet.

A muhallin kasuwar Paxful wadda ke gudana da taimakon mutane, za ka iya sayen Tether kai tsaye daga sauran masu asusu kamar kai da suka fito daga ɓangarori daban-daban na duniya. Babu buƙatar sa hannun wasu bankuna, hukumomi, ko wasu masu shigada tsakani.

Ga yadda za ka fara:

  1. Ka ƙirƙiri asusu ko ka shiga cikin wanda da ma akwai shi. Yin rajista a kan Paxful na zuwa da lalita ta kyauta a inda za ka iya adana USDT naka.
  2. Ka zaɓi hanayr biyan kuɗi, ka sanya adadin abin da kake son kashewa cikin nau'in kuɗin da ka fi so, daga nan ka danna Nemo Tayi.
  3. Ka je kan kowane tayi sannan ka duba dokoki da ƙa'idojin. Ka lura da farashin da masu sayarwar suka sanya, tare kuma da maki na ƙimarsu da tsokacin da aka yi game da su domin ka auna cancangarsu.
  4. Da zarar ka samu tayin da ya yi daidai da abin da kake nema, ka tabbatar da kuɗin da za ka biya sannan ka fara kasuwancin. Hakan zai sa ɓangaren tattaunawa ya buɗe inda za ka samu damar tattaunawa kai tsaye kai da mai sayarwar.
  5. Yayin gudanar da kasuwancin, mai sayarwa zai turo maka ƙarin bayani game da yadda za ku ci gaba da kasuwancin. Ka bi ƙa'idojinsu daki-daki sannan ka tabbatar da harƙallar da zarar ka biya kuɗi.
  6. Da zarar mai sayarwa ya aminta da biyan kuɗin, zai turo maka USDT wanda ke ajiye a ɓangaren adana wanda zai taho kai tsaye zuwa lalitar Tether taka ta Paxful.

Da zarar ka kammala kasuwancin, za ka iya kashe Tether da ka mallaka ta hanyar sayen duk abin da ka ga dama, ko ta hanayr tura ta zuwa wata lalita ta daban.

Sayen USDT ya kasance abu mai sauƙi kasancewar akwai sama da hanyoyi 300 na biyan kuɗi waɗanda suka haɗa da biyan kuɗi hannu, turawa ta banki, da katunan kuɗi. Ba ka ga hanyar biyan kuɗin da ka fi so ba? Sanar da mu, mu kuma za mu yi ƙoƙarin sanya ta a kan kafarmu. Domin ƙarin bayani, duba Sashien Neman Sani namu ko ka tuntuɓi sashen taimako.