Buy from
Biya da
Price per Bitcoin
Yadda za a sayi Bitcoin ta amfani da Revolut
Sama da kwastomomi miliyan 2 ne ke amfani da Revolut wanda yake ba da damarmaki da yawa da suka shafi harƙalloli irin na banki, sun haɗa da tura kuɗi zuwa ƙasashen waje da biyan kuɗi na mutum-zuwa-mutum. A yanzu za ka iya amfani da Rvolut domin sayen Bitcoin a kan Paxful ba tare da biyan wasu ƙarin kuɗi ba. Ga yadda za ka yi:
Abu na farko da kake buƙatar yi shi ne ka shiga cikin asusunka na Paxful ko ka ƙirƙiri asusu ta hanyar danna Ƙirƙiri asusu. Bayann ka kammala bin matakan tantance asusun, ka danna Sayi Bitcoin ka saita Revolut a matsayin hanyar biyan kudi da kake so domin duba tayin da suka dace. Tayin da suka fi dacewa su ne waɗanda suka kasance na dillalai masu ƙima sannan hanyar da za a gano su shi ne a duba furofayil ɗin mai sayarwa domin kallon waɗanda suka samu tsokaci mai kyau mafi yawa. Cikin sauƙi ka danna kan sunan dillalin domin kallon tarihin kasuwancinsa tare da tsokacin da abokan kasuwancinsa suka turo masa.
Da zarar ka samu tayin da kake so daga wurin dillali amintacce, to ka danna Sayi domin kallon abubuwan da suke buƙata yayin kasuwancin. Ka karanta ƙa'idojin kasuwancin a nitse sannan ka bi su daki-daki. Ka danna madannin "Amince da Dokoki sannan ka Sayi Bitcoin Yanzu!" idan ka gamsu da dokokin tayin. Daga nan akwatin tattaunawa kai tsaye zai bayyana a inda za ka iya tattaunawa da mai sayarwar sannan ka tambaya idan yana da ƙarin abubuwan da yake buƙata.
A lura da cewa Paxful na amfani da tsarin adana domin kulle BTC ɗin mai sayarwa da zarar an fara gudanar da kasuwanci — domin kuɗinka ya kasance cikin aminci.
Once you send the payment to the seller’s Revolut account, click Mark as Paid so that the seller can release the BTC from escrow. That’s it! You’ve successfully bought Bitcoin using your Revolut account.