Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Buy from

Biya da

Price per Bitcoin

Yadda za a sayi Bitcoin ta amfani da PayPal

PayPal na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin tura kuɗi ta kan intanet a faɗin duniya wanda yake matsayin zaɓi ga chek da sauran hanyoyin tura kuɗi. Ya samar da hanya mai sauƙi da sauri na turawa da karɓar kuɗaɗe a faɗin duniya, tare kuma da amfani da kuɗi a kowane lokaci, a kowane wuri.

Yanzu za a iya sayen Bitcoin ta amfani da PayPal nan take a muhallin kasuwancin mutum-zuwa-mutum na Paxful. Za ka iya samun tayi da dama da ke karɓar PayPal a matsayin zaɓaɓɓen hanyar biyan kuɗi a kan kafarmu. Idan ba ka samu tayin da ya burge ka ba, za ka iya ƙirƙirar tayinka domin jawon hankalin masu asusu da ke son gudanar da kasuwancin BTC ta amfani da PayPal a matsayin hanyar biyan kuɗi.

Domin gudanar da kasuwanci cikin aminci, wasu daga cikin masu sayarwa na iya buƙatar bin waɗansu ƙarin matakai na tantance abokan kasuwancinsu. A waɗannan matakai za a iya buƙatar ka gabatar da wasu nau'ukan takardu kamar katin shaida, hoton da ka ɗauki kanka, da/ko hotunan fuskar na'ura. Wannan na rage matsalar damfarar da ta shafi biyan kuɗi da amfani da asusun PayPal ba tare da izini ba, wanda hakan na ƙara zamar da Paxful muhallin kasuwanci mai aminci.

Dokokin da ƙa'idojin waɗansu tayi na iya bambanta da na waɗansu tayi na daban, saboda haka, ka tabbatar da cewa ka karanta kuma ka aminta da abubuwan da mai sayarwa ke buƙata kafin fara gudanar da kasuwancin. Za ka iya amfani da kalkuletar Bitcoin ɗinmu ta kan intanet domin samun ƙididdigar adadin BTC da za ka iya saye da adadin kuɗin da kake da shi cikin nau'in kuɗin da ka zaɓa. Domin samun ƙarin bayani, za ka iya kallon bidiyonmu na jagoranci da ke ɗauke da cikakken bayani game da yadda za a sayi Bitcoin ta amfani da PayPal a kan Paxful.

A nan Paxful, muna da burin sauƙaƙa hanyar sauya kuɗaɗen PayPal ɗinka zuwa Bitcoin ta amfani da muhallin kasuwancinmu na mutum-zuwa-mutum wanda ya kasance mai aminci da sauƙin amfani. Samu harƙallar da ta fi dacewa da kai a yau.