Ɗan jira yayin da muke ƙoƙarin nemo maka tayi da suka fi aminci.

Buy from

Biya da

Price per Bitcoin

Yadda za a sayi Bitcoin ta amfani da Apple Pay

Juyawa ragowar Apple Pay ɗinka zuwa Bitcoin yana da sauƙi da kuma mai tsaro a kan Paxful.An kare shi ta adana, muhallin kasuwancinmu na muhallin yana ba ka damar yin kasuwancin tare da dubbannin masu talla na Bitcoin a duniya, kowace rana ta mako, ba sai ka biya ƙarin caje-caje ba. Za ka iya sayi Bitcoin ta yin amfani da Apple Pay a cikin wasu matakai masu sauƙi.

Da farko, ka shiga cikin asusunka na Paxful ko ka ƙirƙiri asusu idan kai baƙo ne a kafar. Da zarar ka shiga ciki, to ka danna Sayi Bitcoin sannan ka saita "Apple Pay" a matsayin hanyar biyan kuɗin da kake so wanda daga nan za a nuna maka dukkannin tayin da suka yi daidai da abin da kake nema.

Da sanyin safe ake kama fara, muna ba da shawarar a duba furofayil ɗin kowane mai sayarwa sannan a karanta tsokacin da masu sayen da suka gabata suka rubuta game da shi domin kimanta amincin gudanar da harƙalla da shi.

Idan ka ga tayi mai kyau daga amintaccen dillali, to ka danna Sayi domin katanta dokokin tayinsa. Kowane dillali yana da dokokinsa na daban amma mafi yawansu na buƙatar ka tura musu kwafen hoton katin shaidarka wanda gwamnati ta ba ka sannan da hoton fuskar na'ura da ke nuna cewa akwai adadin kuɗin da ake buƙata a cikin Apple Pay ɗinka.

Idan ka aminta da dokokin, ka danna Amince da Dokoki sannan ka Sayi Bitcoin Yanzu! domin fara tattaunawa kai tsaye tare da mai sayarwa. Kada ka tura kuɗi har sai idan dillalin ya ce ka tura sannan ka hanzarta danna Yi Maki a Matsayin an Biya bayan ka tura kuɗin daga asusunka na Apple Pay. Da zarar dillalin ya tabbatar da harƙallar, to zai turo BTC ɗin zuwa Lalitar Paxful ta Bitcoin ɗinka.

Ka same shi, yanzun nan ka sayi BTC ta amfani da Apple Pay! Yanzu za ka iya amfani da shi wajen biyan kuɗin ayyuka, sayen kayayyaki, ko ka yi amfani da shi a wata hanya ta daban. Domin tambayoyi, tsokaci, ko damuwowi game da kafarmu, ka danna Tuntuɓe Mu domin kaiwa ga tawagarmu ta masu taimakon kwastomomi.