Ƙa'idojin Ladar Gano Matsala
Paxful, Inc. (wanda kumadu ake kira da "Paxful," "mu," ko "namu") na ɗaukar matakan inganta hajarmu tare da inganta al'amarin tsaro domin kwastomominmu. A cikin wannan Ƙa'idojin Ladar Gano Matsala ("Ƙa'ida"), mun yi bayanin abubuwan da suka shafi Shirinmu na Ladar Gano Matsala tare da yadda za a yi amfani da su wanda ke dangantaka da amfaninka da kafarmu ta https://paxful.com/, wanda ya haɗa da, amma bai taƙata ba ga, Lalitar Paxful, kafarmu ta intanet ta kasuwancin bitcoin, manhajar waya, shafukan kafafen sada zumunta, ko wasu hajojin kan intanet (a jimlace, "Kafar"), ko yayin da ka yi amfani da wani daga cikin hajoji, ayyuka, ƙunshiya, fasali, fasahohi, ko abin da muke samarwa (a jimlace, "Ayyukan"). An tsara wannan Ƙa'ida ne domin ta taimaka maka wajen bayani game da yadda za ka iya shiga cikin Shirinmu na Ladar Gano Matsaal, waɗanne binciken tsaro ne abin ya shafa, da kuma nau'in alfanu da za ka iya samu. Yana da kyau ka tuna cewa Ayyukan da muke gudanarwa na iya bambanta daga wuri zuwa wuri.
Ga dukkannin dalilai, kwafen wannan ƙa'idojin ladar gano matsala da ke cikin harshen Ingilishi shi ne na asali, sannan shi ke jagoranci. Idan aka samu saɓani tsakanin kwafen da ke cikin harshen Ingilishi da kowanne daga cikin fassarori da aka yi zuwa wani harshe na wannan ƙa'idojin ladar gano matsala, to za a yi amfani ne da kwafen da ke cikin harshen Ingilishin.
Mene ne Shirin Ladar Gano Matsala?
Domin inganta Paxful da Ayyukan da muke gudanarwa, Shirin Ladar Gano Matsala na Paxful na ba wa masu amfani da kafarmu damar samun kuɗi yayin da suka gano matsalolin da suka shafi gudanarwa.
Ta yaya za ka iya sadar da abin da ka samo daga Shirin Ladar Gano Matsala zuwa gare mu?
A tura dukkannin nau'ukan waɗannan bayanai zuwa ga [email protected]. A cikin bayanan da za ka tura, ka ba da cikakken bayanin raunin haɗi da shaidar da ke nuna cewa akwai matsalar (bayani / matakan sake samarwa / hotunan fuskar na'ura / bidiyoyi / takardu ko wasu fayiloli makamantan wannan).
Dokokin Shiri
Karya ɗaya daga cikin waɗannan dokoki zai iya kai ga ka zama ba ka cancanta da samun wannan lada ba.
- Ka gwada rauni kawai a kan asusun da ka mallaka ko asusun da ka samu izinin mai shi domin ka yi wannan gwajin a kansa.
- Kada ka yi amfani da wannan bincike wajen yin datse/jirkita bayanai ko jirkita wasu fasahohi. Ka yi amfani da shaidar faruwa kawai domin nuna wani al'amari.
- Idan aka kai ga bayanan sirri kamar su keɓantattun bayanai, bayanan shiga asusu, da sauransu a matsayin rauni na kaar, to kada a adana, ajiye, tura, shiga, ko sarrafa bayan ganowa na farko.
- Ba a ba wa masu bincike dama ko izinin gudanar da wani abu ba da zai samar da tangarɗa, lalata ko cutar da Paxful.
- Ba a ba da dama ba ga masu bincike da su bayyana nau'ukan raunin da suka samu ga al'umma (tura duk wani nau'in bayani ga kowane mutum koma bayan ma'aikatan Paxful da aka ba wa izini), ko kuma tura bayanan wannan rauni ga wani mutum na daban ba tare da izinin Paxful ba.
Ta yaya muke kimanta matsalolin da aka samu a ƙarƙashin Shirin Ladar Gano Matsala?
Ana amfani da tsarin lura da haɗari yayin kimanta dukkannin sakamakon da aka ba da rahoton su.
Yarjejeniyar Riƙe Sirri
Kafin mu fara tattauna duk wasu bayanan da suka shafi matsalolin da suka tabbata cewa ka gano su ƙarƙashin Shirin Ladar Gano Matsala, ciki har da ladar aikinka, da sauransu, akwai buƙatar ka shiga cikin Yarjejeniyar Riƙe Sirri tare da mu.
Ta yaya muke biyan ladar Shirin Ladar Gano Matsala?
Paxful ce take biyan dukkannin waɗannan ladaddaki. Dukkannin waɗannan ladaddki za a biya su ne idan ba su saɓa wa dokokin gudanarwa da ke suka shafi al'amarin ba, ciki har da, amma bai taƙaita ba ga takunkumin harƙalloli da na hada-hadar kuɗi.
Tsawon wane lokaci zai ɗauka kafin gama ƙwanƙwance sakamakon da aka gabatar muku ƙarƙashin Shirin Ladar Gano Matsala?
Kasancewar matsalolin fasaha suna da sarƙaƙiya nau'uka daban-daban, ba mu samar da wa'adin lokaci taƙamaimai ba na ƙwanƙwance bayanan da aka turo mana ƙarƙashin Shirin Ladar Gano Matsala. Ƙwanƙwancewarmu za ta zo ƙarshe ne kawai lokacin da muka tabbatar da cewa akwai ko babu nau'in rauni da ake magana a kai.
Waɗanne nau'ukan abubuwa ne ba sa cikin Shirin Ladar Gano Matsala?
Akwai nau'ukan raunin kafar intanet da ba sa cikin farfajiyar Shirin Ladar Gano Matsala. Waɗannan nau'ukan rauni da ba su shafi shirin ba sun haɗa da, amma ba su taƙaita ba ga:
- Tarkace;
- Rauni da ke buƙatar amfani da fasahar yaudara/leƙen asiri;
- Hari na DDOS;
- Matsalolin da suka shafi hasashe kawai waɗanda ba su da wani tasiri a zahiri;
- Raunin tsaro a kan manhajoin wasu mutane na daban ko kan kafafen intanet na waɗansu mutane na daban wadanda aka haɗa da Paxful;
- Sakamakon ɗaukar hoto ko rahotannin da aka samu daga ɗaukar hoto;
- Matsalolin da aka samu ta hanyar gwaji mai gudanar da kansa;
- Matsalolin da aka yaɗa su a duniya a cikin softwaya na intanet waɗanda suka kasance cikin kwanaki 30 da sanarwa a kansu;
- Harin datsar bayanan harƙallar mutane da kafar;
- Sanya abu a cikin kafar ba tare da hakan zai samar da wani tasiri taƙamaimai da za a iya gani ba;
- Zura mai kantu ruwa, wannan ya haɗa da dukkannin bayanan da wanda abin ya shafa ya sanya;
- CSRF da ya shafi shiga/fita;
Ƙarin Bayani
Idan kana neman ƙarin bayani game da ƙa'idojin, za ka iya tuntuɓar mu ta hanyar tura mana saƙon imel ta [email protected].