Dokokin AML

Paxful, Inc. da Paxful USA, inc (a ware ko a jimlace "Kamfanin"), wanda aka samar ƙarƙashin dokokin Jahar Delaware na gudanar da ayyuka ta muhallin kasuwancin kan intanet na mutum-zuwa-mutum ("P2P) domin saye da sayar da dukiyoyin kan intanet.

An yi rajistar Kamfanin da Hukumar Treasury Department’s Financial Crimes Enforcement Network (“FinCEN”) ta Amurka a matsayin Kasuwancin Hada-Hadar Kuɗi. An samar da ƙa'idoji da matakan Magance Fasa Ƙaurin Kuɗi ("AML) na Paxful domin kare kafar daga hulɗayya da suka saɓa wa shari'a, kare masu asusu, kasuwancin, da kuɗaɗen intanet da mutane da ke hada-hadar kuɗi, domin a kare su daga dukkannin nau'ukan miyagu. Kamfanin yana bin ƙa'idojin Bank Secrecy Act da sauran ƙa'idojin da matakan FinCEN.

A matsayin wani ɓangare na ƙa'idojin Bin Dokar Paxful, an tsara ƙa'idoji da matakan da suka shafi Sanin Abokin Harƙalla ("KYC") domin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙungiyoyi domin ba wa Kamfanin damar samun tabbacin cewa ta san kwastomominta waɗanda ta gudanar da wannan tantancewa a kansu. Wannan ƙa'ida na aiki a kan dukkannin masu asusu da ke kan kafar sannan ƙa'ida ce da dukkannin ma'akata, ma'aikatan lokaci zuwa lokaci, jami'ai, mamallaka da daraktocin kamfanin duka suke bin ta.

Ta hanyar bin tsarin kiyaye haɗari a matsayin wani ɓangare na bin ƙa'idar KYC da AML, Paxful ta ɗauki waɗannan matakai da aka bayyana a ƙasa:

  • Zaɓar Babban Jami'in Tabbatar da Bin Doka wanda yake da cikakkiyar ƙwarewa da cin gashin kai, wanda haƙƙi ne a kansa ya lura da bin matakan da suka shafi dokoki, ƙa'idoji da tsarin ma'aikata;
  • Samarwa da kula da al'amuran da suka shafi kare haɗurra kamar su KYC, Himmar da Ake Buƙata Daga Kwastoma (CDD), da Ƙa'idar Ƙarin Himma da Ake Buƙata (EDD);
  • Samar da tsare-tsaren kare haɗurra da suka shafi tantance masu amfani da Kamfanin (wanda a nan ke nufin wannan rubutun Kafar Intanet);
  • Samarwa da gudanar da abubuwan da ake buƙata da suka shafi buƙatun dokoki da na gudanarwa;
  • Kundace Rahotannin Ayyukan da Suka Kasance Abin Zargi (SARs");
  • Ba da horaswa na illahirin kamfani BSA/AML/OFAC;
  • Amfani da fasahohin kare damfara daban-daban;
  • Dokoki masu gudana da suka shafi bibiyar harƙalla;
  • Gudanar da bincike ta amfani da ƙididdigar blockchain;

Muna kundace SARs idan muka fahimci cewa, ko muka zargi, ko muka samu dalilin da zai sa mu zargi cewa wasu al'amura abun zargi sun faru da kafar. Harƙallar da ta aksance abar zargi yawanci takan kasance wadda ba a saba da ita ba a tarihin kasuwancin mai asusu, ko keɓantattun harƙallolinsa, ko sauran abubuwa da suka keɓanta da shi. Jami'inmu na Tabbatar da Bin Doka zai duba sannan ya gudanar da bincike a kan harƙallar da ta kasance abin zargi idan an karɓi bayanai wadatattu domin kundace SAR. Jami'inmu na Tabbatar da Bin Doka na adana bayanai da fayilolin da suka dace na dukkannin SARs ɗin da aka kundace.

Sannan Kamfanin ya kwaikwayi nau'ukan ƙa'idoji da matakan takunkumi na OFAC waɗanda aka tsara domin kare kafar daga masu amfani da ita ta hanyoyin da aka haramta, wada kuma masu aikata haramtacciyar harƙallar za su iya haɗawa da mutanen da doka ba ta ba su damar amfani da kafar ba, waɗanda ke ƙoƙarin, tsallakewa, kaucewa, ko zagaye wa dokokin hani na U.S. ko na duniya.

Paxful na ba da cikakken haɗin kai ga dukkannin OFAC, 'Yan Ƙasa Masu Doka ta Musamman (SDN) da kuma jerin mutanen da aka Katange. Duba liƙau ɗin da ke ƙasa domin kallon jerin ƙasashen da Kamfanin ya haramta wa amfani da kafar Paxful.

Idan ya kasance Paxful ta samar maka da fassarar wannan ƙa'ida da ta kasance cikin ahrshen Ingilishi, to ka aminta da cewa an samar da fassarar ne domin ka ji daɗin amfani da shi kawai sannan kwafen ƙa'idar da ke cikin harshen Ingilishi shi ne zai jagoranci hulɗayyarka da Paxful. Idan aka samu saba wa juna tsakanin abin da kwafen ƙa'idar cikin harshen Ingilishi ya fada da abin da kwafen fassarar ya faɗa, to kwafen da ke cikin harshen Ingilishi shi ne zai yi jagoranci.