Barka da Shigowa Harƙallar Kuɗi da Mutane ke Tallafe da Ita

Paxful na samar da sauyi a duniyar hada-hadar kuɗi. A cikin shekaru biyar kacal, mun zamo ɗaya daga cikin jagaba a muhallin kasuwancin bitcoin na mutum-zuwa-mutum wanda miliyoyin mutane suke amfani da shi a faɗin duniya. Sannan yanzu ne ma muka fara.

Sayi kuma ka sayar da Bitcoin da Tether a kan Paxful

Kayanmu

Paxful na samar da sauyi a hada-hadar duniya inda ake ƙara karɓar kuɗin intanet - wanda hakan ke ba da damar tura kuɗi ga kowa, a ko'ina, sannan a kowane lokaci.

Ba ka da asusun banki? Wannan ba matsala ba ce. Muna da hanyoyin biyan kuɗi sama da 300 da za ka iya zaɓa daga ciki, wanda hakan ya samar da sauƙi a gare ka na sarrafa kuɗaɗenka yadda ka ga dama.

Fasahar da Mutane ke Tallafe da Ita

Duk al'amuran Paxful sun kasance na mutum-zuwa-mutum, wanda hakan ke nufin masu amfani da kafar na gudanar da kasuwanci ne da mutane na haƙiƙa - kamar dai yadda aka nufa game da amfani da bitcoin.

Lalitar Kuɗin Intanet ta Kyauta

Abin dogaro ne, mai sauƙin amfani, sannan na kyauta. Lalitarmu ta intanet na ba wa kowa da kowa wuri mai tsaro na adana dukiyarsu - za ka samu dama ko kai wane ne sannan daga duk inda ka fito.

Mai tsaro

Tsaro da rigakafin duk wata matsala su ne muhimman abubuwa yayin adana kuɗinka. Dukkannin kasuwanci a kan Paxful suna ƙarƙashin kariyar tsarin adana wanda hakan ke ba ka garanti na samun kwanciyar hankali.

Tuntuɓa Domin Kasuwanci

Idan kana da matsalar da ke buƙatar taimako ko kana son turo mana tsokaci game da yadda za mu inganta hajojinmu, za mu so mu ji daga gare ka ta . Bugu da ƙari, idan kana so ne ka tuntuɓi Paxful dangane da al'amuran da suka shafi kasuwanci, to za ka iya kaiwa gare mu ta wasu hanyoyi na daban.

Yaɗawa da Tallatawa

Taimaka wajen yayata Paxful ta hanyar yaɗawa da tallatawa. Tuntuɓe mu a [email protected]‎ domin tambayoyi game da yaɗawa.

Ladar Gano Matsala

Thank you for your interest in Paxful’s Bug Bounty Program. We are currently reviewing our program for process improvements, and therefore, we are not currently accepting bug reports. Please check back for an updated version in a few weeks. For more information, you may contact us by emailing [email protected].‎

Asusun Haɗin Guiwa

Domin rajistar asusun haɗin guiwa saboda gudanar da kasuwanci a kan Paxful, za ka iya tura saƙon imel zuwa [email protected]. Duba ƙarin bayani a nan.‎

Cinikayya da Haɗin Guiwa

Domin neman ƙarin bayani game da haɗin guiwa da mu. Idan kana son haɗa guiwa da mu, to ka sanar da mu ta [email protected].‎

Shiga cikin tafiyar Paxful
Mu haɗa kai wajen gina kyakkyawar gobe
Shiga Cikin Tafiyarmu

Ƙirƙiri asusunka na Paxful domin ka yi rangadi a duniyar kuɗin intanet.